Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Farar Taska Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ki cire zanin ki buɗe min ƙafafun ki kafin raina ya baci nayi maki mugun bugu yanzu, banda kin raina ni har ina magana kina min musu, ƙarya zan maki bakya buƙata na ne? Jiki a sabule ta ƙarasa shiga ɗakin yanda yaran ba zasu iya hango su ba, ta kwanta tayi yanda yace idanunta a sama, yazo yayi abinda zai yi ya tashi yana sauke numfashi kaɗan saboda wata nutsuwa da yake ji a ransa, yana kallo ta tashi da ƙyar har zata fice yace "dawo nan" Sai da antar cikinta ta kaɗa wannan karon bata san kiran na menene ba, yace "ɗauki dubu ɗaya a kuɗin kije kuci abinci" ta zare idanu tana kallon sa cikin mamaki kamar kunnuwanta basu ji da kyau ba, ta sani ba zai taba maimaita mata abinda ya faɗa ba, ta ɗauki ɗaya tana masa kallon mamaki da ƙyar ta buɗe baki tace "mun gode maigida" ya ɗauke kansa gefe batare da yayi magana ba, ta juya ta fice yaran har lokacin suna tsaye ƙofar ɗakin ta hankalinsu a tashe ganin ta shiga ɗakin baban nasu duk tunanin su bata samu kuɗin ba dukan ta zai yi, suna haɗa ido da ita ta sakar masu murmushin nan nata mai sanyi, tace "Safeenah zo kije ki siyo mana dankali yau shi zamu dafa muci, Baban ku ne ya bayar da kuɗin" ta faɗa cikin son cire masu zargin mahaifin su" duk suka saki murmushi suna kallon ta, ta ba feenah kuɗin kafin ta nufi bayi tana faɗin bara na watsa ruwa kafin ki dawo. Washe garin ranar sun shirya tsab zasu je makaranta, Deejah bata da takalmin sakawa kuma bata da ko sisi da zata siya mata, Meelah ta cire nata ta bata tana faɗin "ni zan iya tafiya a haka" Feenah ta cire nata ta bawa Meelah tana faɗin "ga nawa ki saka ni zan tafi a haka" cikin tausayawa Ummy tace "ki ɗauki nawa ki lallaba dasu tun da sun maki yawa" Ta girgiza kanta tana faɗin "innarmu ke Kuma Idan zaki fita me zaki saka, ni bazan karɓa ba na gayamiki zan iya tafiya a haka" kafin Ummy tayi magana Feenah ta fice da gudu sauran suka bi bayan ta, haka taje makaranta sai dariya ake mata babu takalmi a ƙafarta, wannan dariyar da ƴan ajin nasu suke mata ta janyo hankalin malamin zuwa gare ta, tana gefe sai Rubutun ta take batare da damuwa ba kamar ba ita ake yiwa dariya ba, kallon uniform ɗinta yayi tun daga hijab har kayan jikin ta duka a yage suke, wani guri duk an saka allura da zare an ɗin ke kuma a hakan kayan basu da dirty ko kaɗan, yayi gyaran murya kaɗan kafin ya tsawatar da ƴan ajin akan abinda suke, kowanen su ya nutsu saboda sanin halin sa Sam baya wasa da kowa a class ɗin, babu bata lokaci ya cigaba da koyarwa wanda bai san dalili ba akai akai idanuwansa suke satar kallon ta, ta kuwa tsura masa ido cikin son fahimtar abinda yake koyar dasu, yayi tambaya itace ta farko da ta soma ɗaga hannun ta sama, ya bata izini akan ta amsa, ta tashi tsaye ta amsa tambayar, ya jinjina kansa cikin mamaki, bayan gama karatun ya nuna ta da yatsa tare da faɗin "your name? Kai tsaye tace" Safeenah Audi" ya jinjina kansa kafin yace "ki karbo duka littafansu ki biyo ni dasu" babu bata lokaci kowanen su ya soma haɗa littafin sa yana bata tana karɓa, sanda tazo fita ta tuna babu takalmi a ƙafarta ta dawo kusa da ƙawarta a hankali tace "Maryama ko Zaki aramin takalmin ki naje na dawo" Maryama ta cire takalmin ta bata batare da tayi magana ba, cikin farin ciki ta saka takalmin tabi bayan sa har staff room, Kai tsaye inda teburinsa ta nufa ta ajiye tana ƙoƙarin fita ya dube ta yana faɗin " takalmin waye kika saka" ta juyo tana kallon sa kafin tace "na ƙawata ne Maryama" yace "ke Ina naki takalmin" tace "ƙanwata ce bata da takalmin sakawa shine na bata nawa ta saka" yayi shiru yana ƙara kallon ta kafin yace "iyayen ku suna da rai? Ta gyaɗa kai da sauri, yace" shine basu siya maki takalmin ba kika fito a haka, look kin ga uniform ɗin jikin ki kuwa? ta dubi kanta tana kallon yanda kayan suka tsufa suka koɗe kuma a yage kafin ta dube sa tace "basu da kuɗin da zasu siya min wasu" yayi jim kaɗan kafin ya saka hannu a aljihun kayan jikin sa, ya ciro kuɗi ya bata yana faɗin kije ki siye takalmi kuma a canza maki uniform". Ta dubi kuɗin kafin ta dube sa ta girgiza kanta, " Innar'mu ta hana mu karɓan kuɗi a gurin kowa sai ita kaɗai da baban mu" ya mayar da kudin aljihunsa yan faɗin "shikenan zaki Iya tafiya" ta juya da sauri ta bar office ɗin cikin mamaki malamin ko meyasa zai bata kuɗi, ba wanda ta gayawa har kawar ta Maryama, sai bayan sun tashi makaranta suna tafe take bawa ƙannen ta lbr Malam Huzaifa, kowa a makarantar ya san shi, shi ɗan gayu ne kamar yanda suke faɗa, Meelah tace "gwara da baki karɓa ba domin Innar'mu zata yi faɗa kuma ranta zai baci" ta cire takalmin ta bawa safeenah ta saka, idan sun yi tafiya itama ta cire ta bata ta saka saboda zafin rana haka suka yi tayi har suka iso gida, aikuwa nan suka ba Ummy lbr malamin, tace "Sam kada ku kuskura ku karbi kuɗi a hannun duk wani namiji, daga baban ku sai mijin auren ku" Feenah tace "Ai mu baza muyi aure ba Innar'mu, zamu kasance dake ne har qarshen rayuwar mu". Tace "zaku yi aure ku haifa min jikoki, burin kowacce uwa ta ga ta aurar da ya'yanta mata, ku daina faɗin baza ku yi aure ba bana so". Meelah ta tashi tana faɗin "da gaske ni bazan yi aure ba, bana so ana duka na kuma na faɗa ko da baba zai yanke duka hannu da ƙafafuna tabbas wata rana zan rama maki dukan da yake maki" ta bar gurin batare da ta tsaya sauraren Ummy ba, Feenah ma tabi bayan ta tana faɗin "Nima Ina bayan Meelah Innar'mu bazan yi aure ana dukana kamar yanda Baba yake dukan ki ba". Ummy tayi Jim cikin tunani kafin ta dubi Deejah tace "kije ki cire kayan jikinki kizo kuci abinci" Deejah ta tashi ta fice, Washe garin ranar haka Safeenah ta je makaranta ba takalmi kamar jiya, kuma haka yaran ajin su suka dinga mata dariya bata kula su ba inda sabo dama ta saba da halin su kullum yi mata dariya akan kayan jikin ta, yau ma ko da ya gama darasin sa sai ya bata umarni kamar jiya akan ta haɗa duka littafan ta same sa da su, sanda ta ajiye tana ƙoƙarin juyawa ya fito da takalmi ya bata, ta dubi takalmin cikin mamaki kafin ta dube shi, tace " innarmu ta hana mu karɓan komai a hannun namiji idan ba Baban mu ba" yace "Amma kika ce kuɗi ta hana ku karɓa ai? Tace" komai ma ta hana" yayi murmushi kafin yace "ki karɓa ni ba

Table of Contents

Chapters

18 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});