Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Farar Taska Book 1 Complete Hausa Novel 1,188 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

buɗe min ƙafafu nace" ta tashi da ƙyar tana cije bakinta saboda bayanta dake ciwo, cikin rawar murya tace " mai gida dan Allah kayi haƙuri ko ɗakin kane sai muje amma acikin yaran nan idan wata aciki ta tashi fa? Yace " ni zan kai ki ɗakina dan kin raina min wayo, ɗakina ne zanje dake ki kwanta min ml katifa, aiko darajar ƙasan ɗakina baki cancanci kwanciya ba balle ki hau makwancina, maza buɗe min qafa idan bazaki iya ba na buɗe ta ƙarfi da kaina" idanunta suka cika da ƙwallah ta tashi da ƙyar tana ƙoƙarin fita, yace " gidan uban wa zaki je ki barni anan? cikin rawar murya saboda kuka tace " zan kwanta ƙasa a waje ne, zai fimin akan gaban ƴaƴana" yayi ƙwafa yabi bayanta, da ƙyar ta kwanta a ƙasa yasa ƙafa ya hangame ƙafarta a fusacce yana cire wandon jikinsa, ban da hawaye masu ƙunar zuciya babu abinda take, yayi iya yinsa ya tashi ya fice yana babbatu tare da tsine mata albarka ita da yaranta mata, ta kasa ko wani ƙwaƙwaron motsi daga inda take kwance a ƙasa, barcin ma ya ƙauracewa idanuwanta, kasancewar sa uban ƴaƴanta ya saka duk wata muguwar addu'a take kasa yi masa, tana ji an soma kiraye kirayen sallah ta tashi da ƙyar ta lallaba ta shiga bayi tayi wanka, washe gari bayan fitar su makaranta ta nufi inda Saratu ta jima zaune a gidan suna hira ba dan komai ba sai dan ta kaucewa ganin ta dashi, babu abinda ta tsana a duniya irin ta buɗe ido ta ganshi a gabanta, yanda take jin tsana da tsoronsa a zuciya har tana hasashen shine ajalinta wata rana, muryarsa kaɗai idan taji ji take kamar ana fisgar numfashinta, sai da lokacin dawowar su makaranta yayi kana ta nufi gida, bata jima ba sai gasu sun shigo duka suna kuka a tare su uku, hankalinta yayi matuƙatar tashi har ta manta cikin jikinta saboda tsananin ruɗewa ta nufe su tanaa tambayar su meya faru, " baba ne ya tare mu a hanya yayi mana dukan tsiya" suka cire kayan jikinsu suna nuna mata bayan su, abinka da farar fata duk shatin bulala ruɗuɗu a bayansu, dukan da aka masu irin na mugunta kamar ana bugun babban mutum, jikinta ya ɗauki rawa iya ruɗewa ta ruɗe ga hawaye dake ta ambaliya a fuskarta, ta taba jikin wannan ta taba jikin wannan tace " me kuka masa yayi maku wannan duka haka" Safeenah tace " wai mu ba ƴaƴan sa bane mu shegu ne baya son mu, innar'mu ki kaimu inda mahaifin mu ai shi bazai dake mu haka ba" duka su ukun ta haɗa a jikinta ta rungume, wannan karon sautin kukan ta ya kasa boyuwa saboda zafin dukan da ta gani a jikinsu, kuka take ba kakkautawa wanda ya saka su shiru da nasu kukan suna saurarenta. [8/2, 6:56 PM] J💕: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t *FARAR TASKA* Fertymerh Zarah💕 4 Shigowarsa ya saka duk suka yi shiru suka qara ƙanƙame Ummy, ya ja dogon tsaki cikin takaici yana faɗin " wai har ni zaa tare a hanya akan waɗannan mayun yaran naki ace ana so, har ana kirana da baban turawa, an mayar min da gida a garin nan gidan turawa saboda jajjayen fatar ku, na soma gajiya wallahi ta Allah zaku barmin gidana, na gayamiki ba tun yau ba ki nemi uban su ni ba yarana bane, iyayena basu taba haifar mace ba har suka bar duniya, ta ina nake da gadon haifar ƴaƴa mata, sannan kaf dangin mu bamu da masu jajjayen fata, ta ina nayi gadon haifar su, ƴaƴan da na dasa acikin ki ai sai dai su fito a irina ba irin ki ba" cikin karkarwar murya jin yana maganar zai kore su tace " kayi haƙuri maigida" ya ƙara turo baki yana hararar su kafin yace " wallahi ta Allah aka sake tare ni a hanya ana son waɗannan yaran sai nayi masu duka, sai na bata wannan fatar jikin tasu, saboda haihuwar su komai nawa yake lalacewa, saboda su na rasa iyayena duka da ban haifesu ba da yanzu ina tare dasu, da ace maza ne kika haifamin Allah kaɗai yasan inda suna na zai kai saboda tarin arziki, ga ƴaƴan Shamwilu nan kullum sai ya saka su a gaba yaje dasu gona, shiyasa duk lokacin gona yazo yake cin gajiyarta ni bani da wani magaji da zai kama min". Duk suka yi shiru ba wanda yayi magana sai ƙwallah da suke sharewa, ya nufi hanyar fita kome ya tuna ya dawo yana nuna ta da yatsa " Kin ga wannan cikin wallahi kinji na rantse ba gudu ba ja baya idan macece ki danneta kada ki taba haifarta kai ko ta fito ki mayar da ita ko kuma kije ki jefar da ita, wallahi bayan wannan matan guda uku da na haqura nake zaune dasu bazan ƙara zama da wata macen ba, idan har bakiyi yanda nace ba zaki tattara ƴaƴanki ki bar min gidana kai garinan ma zaki bari gabaki ɗaya ai saboda ni aka kawo ki kike zaune kuma zan kora ki" yana gama mgnr ya fice yana faɗa sosai, Deejah tace " Innar mu ki kaimu inda baban mu ai shi bazai riƙa dukan mu yana dukan ki ba" tayi murmushin yaqe tana goge hawayen fuskarta tace " ban taba baku labarin illar shan barasa da abinda take haifarwa ba? Duk suka jinjina kansu, tace " to wannan yana ɗaya daga cikin ilollin duk mai shan barasa shiyasa na hane ku da santa kada ta taba Baku sha'awa ko lasawa kuyi Idan kuka ga ya ajiye kwalbar domin tana saka mutum mantuwa ya manta komai da kowa nashi, kuma haramun ne shanta, shiyasa kuka ga mahaifin ku yana irin wannan halin ba yin kanshi bane duk barasar ce take saka shi haka, amma shine mahaifin ku kuma yana son ku har zuciyarsa, idan ya daina shan barasa a rayuwarsa zaku ganshi ya dawo dai dai kamar Malam wadata" Safinah tace " Innar mu meyasa bazai daina sha ba tunda haramun ne? Tace " zai daina ai ya kusa ya daina dana haifa masa yaron cikina" Meelah tace " idan kuma macece kika haifa kenan bazai daina sha ba innar mu? Tayi jim tana kallonta cikin mamaki kafin tace " zai daina ku daina wannan maganar a yanzu, kowa yaje ya cire kayan jikinsa na ajiye maku abinda zaku ci idan kun gama ku huta haka" suka fashe da kuka suna faɗin duk jikin su ciwo saboda zafin duka, haka ta riƙa rarrashinsu da basu baki har ta samu suka daina kukan. Bayan wani lokaci anyi hutu daga makaranta sai gasu sun shigo gidan a guje kowacce tana so ta fara zuwa ga Ummy, jin hayaniyarsu ta fito daga ɗakin tana faɗin " kuyi sannu kada ku zame kuji ciwo, murnar me kuke yi haka" Meelah tayi caraf tace " Anyi hutu Inna kuma kowa yaci jarabawarsa" Ummy ta nemi guri ta zauna da ƙyar tana murmushi suma suka zauna kusa da ita kowa na ƙoƙarin nuna mata sakamakon jarabawar sa, Safeenah tace " Innar mu kinga a ajin mu nice nayi ta biyu, Meelah ce tayi ta ɗaya a ajin

Table of Contents

Chapters

18 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});