Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 1

Chapter 1

Farar Taska Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

[8/1, 9:02 PM] J💕: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t ﺑِﺴْـــــــﻢِﷲِﺍﻟﺮَّﺣْﻤَﻦِﺍلرَّﺣِﻴﻢ ©️Fertymerh Xarah💞 *FARAR TASKA* 1 Gudu gudu, sauri sauri haka take haɗa tafiyar ta, tana yi tana waigawa bayanta tana hango yanda yara suke biye dashi suna mashi waqa, wasu ma riƙe da babbar rigarsa suna jansa sai tangaɗi yake kamar zai faɗi ƙasa, tana shiga gida ta nufi inda mahafiyarta ke ƙoƙarin kunna gawayi domin ta ɗora girki, ta ajiye mata markaɗen gari a gabanta da sauri ta juya zata fice tace " Saurin me kike haka, ina zaki je, ba yanzu kika shigo ba? ta shagwabe fuska kamar zata yi kuka cikin damuwa da bacin rai, tace " Innar mu yanzu na hango yara suna bibiyar baba da waqa ina tunanin yaje ya sha wannan abin da bakya so yana sha a kullum" batare da tayi magana ba taja dogon tsaki ta juya tana cigaba da gyara wuta, ganin haka yasa yarinyar yar kimamin shekara goma da haihuwa fita da sauri ta nufi inda mahaifin su yake, yaran suna hangota suka soma gudu suna faɗin " ga Meelah ta zo kowa ya gudu kada ta fasa masa goshi" duk suka gudu suka barshi, cikin takaici bayan ta ƙaraso inda yake tana kallon sa tace " Baba kasan Innar mu Bata so kana shan wannan abun meyasa bazaka daina ba, baka jin kunyar yanda yaran ƙauye suke biyo ka kullum da waƙa, innar mu ta gayamana wannan abin da kake sha ba mai kyau bane, hassalima addinin mu ya hana kuma tace yana taba lafiyar ɗan adam muma kada mu kuskura muce watarana zamu sha, meyasa kai bazaka daina ba ko dan saboda Allah da ya hana? ya buɗe idanunsa da ƙyar tare da nuna ta da ɗan yatsa yace " zan ci uban ki yanzu idan kika sake min magana irin wannan, maza matsa bani hanya kar nasa ƙafa na shure ki nayi maki illah bani da kuɗin magani" ta riƙa hannunsa suka soma tafiya tana addu'a a ranta Allah yasa kada ya daki Inna, wani lokacin duk ya sha ya fita hayyacinsa haka yake zuwa yayi ta dukanta a gabansu, tun suna yara har suka taso yake wannan halin bai daina ba, sanda suka iso gidan ko kaɗan Inna bata tayar da kai ta dube su ba, ta cigaba da aikin da take tana kiran Safeenah, da sauri ta fito daga ɗaki tana faɗin " Innar mu sai ƙwalla min kira kike kamar zaki fasa kaina, sallah fa nake yi" cikin takaici ta dube ta tana faɗin " yanzu fisabilillah Safeenah sai yanzu kika Asr? tace " kiyi haƙuri kada ki dake ni Inna wallahi barci ya ɗauke ni bansan lokaci yayi ba" tayi ƙwafa tana faɗin " zo ki gyara kayan miyar yanzu kafin tuwon ya nuna" tace " to innarmu" ta ƙarasa wurin ta da sauri, Audi ya dube ta cikin maye yana faɗin " ke Ummy baki ganni bane kika yi kunne uwar shegu dani" a raunane ta ɗago tana kallon sa, tace " kayi haƙuri sannu da dawowa" yace " saboda kin raina ni sai da nayi magana zaki min sannu, to ki riƙe sannun ki bana so amma jikin ki yau zai gayamiki tunda har yanzu baki hankali ba baki san yanda ake tarairayar miji ba" gaba ki ɗaya duka ɗiyan suka buɗe ido suna kallonsa, Meelah tace " dan Allah Baba kada ka dake ta yau kayi haƙuri ka barta" yace " yi min shiru kafin na fasa maki baki yanzu" ya nufi inda yake ajiye bulalar sa ƙatuwar gaske, Innar mu na ganin haka ta tashi ta nufi ɗaki ba dan komai ba saboda bata so maƙota su jiyo dukan da yake mata, yaran suka soma kuka sosai suna bashi haƙuri bai saurare su ba, suna ji yana dukan mahaifiyar su da ƙarfi babu yanda zasu iya taimakonta, suna jin yanda take nishi alamar dukan yana shiga jikinta sosai amma bazata iya buɗe baki tayi kuka saboda ta ɗaga hankalin ƴaƴanta ba, har ya gaji dan kansa ya fito daga ɗakin ya nufi nasa, da sauri duka su ukun suka faɗa ɗakin suka nufi mahaifiyar su, a tare suka faɗa jikinta suna wani irin kuka gwani tausayi ganin yanda take kwance hawaye na fita gefen idanuwan ta, ga shatin bulala a jikinta da cinyoyinta, suka rufe mata cinyoyin suna ƙara rungumeta cikin tsantsan so da tausayi ga mahafiyar su, Tace " Safeenah kije ki ƙarasa girkin, ai zaki iya ko? Safeenah ta gyaɗa kanta tana share wasu ƙwallah, kafin ta tashi ta fita jiki a sanyaye, Meelah tace " Innar mu zaki sha ruwa na kawo maki? ta gyaɗa kanta a hankali, Meelah ta tashi da sauri ta fita daga ɗakin bata jima ba sai gata ta dawo ɗauke da Cup ɗin ruwa ta zauna gabanta tana faɗin " tashi kisha innar mu" ta tashi da ƙyar tana rumtse idanunta tare da dafe ɗan matashin cikinta ta zauna, Meelah ta kai cup ɗin ruwa bakinta ta soma sha, sai da taga ta ɗauke kanta gefe kafin ta ajiye cup ɗin tana faɗin " Innarmu inje in ɗora ruwan zafi na gasa maki jikin ki? ta girgiza kanta a hankali tace " ki bari idan na huta kaɗan zanje nayi wanka". Haka suka yi ta ɗawainiya da Mahaifiyar tasu cikin so da kulawa duk da suke yara hakan bai sa sun gane mahaifinsu baya kyautawa mahaifiyar su. Malam Audi ɗan Asalin jere, mashayin giya idan nace mashayin giya ina nufin komai zai iya akan ya sami giyar, yana shekara ashirin ya tashi da ɗabi'ar shaye shaye ga rashin ji, dalilin haka iyayen sa suka je suka samo masa mata mai kyau buzuwa suka aura masa ko da Allah zai sa ya gyara ɗabi'un sa, tun bayan auren sa da Ummy Aysha maimakon su ga canjin da suke fatan samu sai suka ga sabanin haka, sun yi faɗa sun yi rarrashi bashi da niyar canzawa, duka kayan ɗakin da aka kawo Ummi dasu ya siyar gurin shan giya, idan bashi da ko sisi zai je duk inda zai nemi bashi yaci bashi yaje ya siya, duk garin babu wanda bai san Malam Audi da Aminin sa Shamwilu saboda barasa ba, wanda yawanci duk abubuwan da yake yi shine yake saka shi komai, iyayensa su suke kula da Ummi yarinya mai kyau da kirki ga nutsuwa amma bata yi dacen miji nagari ba, bayan ta sami cikin farko ta haifi Safeenah, tun a lokacin ya ke ƙara cusguna mata na ta haifa masa mace ba namiji ba, acewar shamwilu ƴaƴa mata basu da wani amfani a rayuwa, hakan ya ƙara hasala Audi wanda yaji sam baya son a haifa mace, ya faɗa ya ƙara faɗa da babbar murya baya son ƴaƴa mata kada ta kuskura ta ƙara haifa masa, tun da ta sami ciki na biyu ta shiga tsoro da zullumi tayi tattaki har inda iyayen ta taje ta sanar dasu irin halin da take ciki game da mijin da suka aura mata, sosai sun ji babu daɗi kuma sun nuna bacin rai ganin yanda duk ta rame wannan hasken nata mai ban sha'awa duk ya soma gushewa, suka riƙe ta suka hanata tafiya har sai da iyayensa suka

Table of Contents

Chapters

18 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});