Chapter 8
Chapter 8
min bulala (geza) idan ka sake anjima ka dawo min a buge sai jikin ka ya gayamaka wlhy". Yace " ai na daina shan barasa tunda bakya so Audi kawai zan ra ka" tayi ƙwafa tana girgiza ƙafafunta tace " naman nake jira yanzu kada ka bata min lokaci" ya fice da sauri jikinsa har rawa yake saboda yunwa, bai yi tunanin zai sami Audi a zaune inda ya barshi ba ya ɗauka ya jima da shiga gida, yana fitowa suka haɗa ido, yace " baka shiga gida ba kenan? Audi yace " ina zaune ina ta faman tunani, lafiya na ganka kamar a hargitse? Shamwilu yayi murmushin yaƙe yace " yanzu na gama dukan yasira shine ka ganni haka, inace kaji tana ihun neman taimako ko? Audi yace kunnena ba a can yake ba, ni tunani nake akan rayuwar nan tun ɗaxu, amma me tayi maka da dawowar ka zaka dake ta yarinya tana maka biyayya sosai". Shamwilu yace "girki tayi min babu nama aciki, na gayamata ko ban bayar da kuɗin nama ba dole zata saka kuɗin jikinta ta siye naman ta saka min ko da tsoka ɗaya ce idan ba haka ba duk ranar da ta sake ta min girki ba nama tabbas jikin ta zai gayamata" Audi cikin mamaki yace " yanzu saboda wannan ka dake ta" shamwilu yace " ƙwarai kuwa ai gobe bazata sake min girki ba nama ba ko bata da kuɗin zata je taci bashi ta saka min, ai shiyasa nake gayamaka idan baka dukan mace raina ka take sosai kuma bazata taba ganin ka da girma a idon ta ba". Audi ya jinjina kansa cikin gamsuwa tuna yanda Ummy ke tsoron sa kuma tana masa biyayya akan komai yace, Shamwilu ya soma tafiya yana faɗin " sauri nake yunwa nake ji zanje na siyo naman na dawo, ba dan mutanen gari su zage ni idan suka ganta a yanzu ta fito ba da tabbas ita zata je ta siyo naman, duk na yiwa jikin ta tabon duka shiyasa bana son ta fita a yanzu" Audi yace " shikenan sai ka dawo nima zan shiga daga ciki na nemi abinda naci". TWO WRITERS EMPIRE ✍️✍️ Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa, FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira ɗari shidda shidda, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya. [8/2, 9:00 PM] J💕: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t *FARAR TASKA* Fertymerh Zarah 6 Audi bai motsa daga wurin da yake zaune ba har sai da ganin Shamwilu ya bacewa idanun sa, ya sauke numfashi kaɗan kafin ya tashi, ya ɗauki kayan nomansa jiki ba ƙwari saboda yunwa ya shiga cikin gida, zaune suke tsakar gida kowacce tana tsefe gashin kanta, Deejah ce kawai mamanta take mata, yaji wani yarrr gashin jikinsa ya tashi ganin irin yalwar gashin dake tattare da kowaccen su, da sauri ya ɗauke kansa daga kallon su har wani tsoron yake ji, yaji Muryar Ummy tana faɗin " Barka da dawowa mai gida" bai amsa ba yayi shigewar sa ɗaki, kayan sa ya ajiye ya dawo da sauri yana faɗin " kowaccen ku ta rufe min kanta kafin naci kutumar uban ku yanzu" da sauri Ummy ta soma basu kallabin su jikinta na rawa tace " ku yi sauri ku ɗaura a kai kun ji" suka karba suna tunzure baki ƙasa ƙasa, ta ɗaure na Deejah ta riƙa hannunta suna ƙoƙarin barin gurin yace " dawo nan ina magana zaki tashi ki tafi saboda kin raina ni, sai na fasa maki baki yanzu kinsan halina" ta sunkuyar da kanta ƙasa batare da tayi magana ba, ya dubi yaran tare da nuna su da ɗan yatsansa yace " wallahi summa tallahi kun ji na rantse ko, duk ranar da ku ka sa ke na ƙara shigowa gidan nan baku gaidani kamar mahaifiyar ku ba sai fatar jikin ku ta gayamaku, na fita neman abinci na dawo a gajiye sai ku zuba min shegun idanun ku kuna kallona" Ummy tace " Ayi masu afuwa mai gida, zasu gyara" ya ja ƙaramin tsaki yana faɗin " ina abinci na" ta ɗago daga sunkuyen da take wannan karon tana kallon sa, kallo ne mai cike da ban mamaki, to ko dai baya hayyacinsa yaje yaa sha ya bugu ne idan ba haka ba ta yaya zai tambaye ta abincin sa bayan ba shi yake ciyar dasu ba ita take ciyar da kanta da yaranta, duk aikin noman nan da yake zuwa har ya gama ya cire yaje ya siyar bai taba bata ko gwangwani na gero ba, rabon da ya ciyar da ita tun bata haifi Deejah ba tun iyayen sa suna da rai....kin min shiru ina magana saboda kin raina ni sai kallona kike, mayya namana bazai ciyu a gurin ki keda ƴaƴan ki ba" ta lumshe manyan idanuwanta a hankali kafin ta sunkuyar da kanta tare da faɗin " babu abinci su kansu yaran maƙota suka je suka ciyo" yayi jim cikin takaici kafin yace " kowacce mace tana nemawa mijinta abinda zai ci har da nama amma banda ke, babu ta inda kike kyautatawa mijin ki, wani lokacin sai na zauna nayi tunanin menene amfanin ki a gurina babu banda ki haifa ƴaƴa mata, to wlhy nagaji idan har bazaki ciyar dani ba to dole zaki bar gidannan ke da yaran ki naje na nemo wata na aura" ƙwallah ta cika idanunta, cikin rawar jiki tace " idan na bar gidan ni da su a ina kake so mu je mu zauna, waye zai bani gurin zama da yara uku haka, bani da wani sauran gata a duniyar nan banda kai, kai kaɗai nake dashi sai waɗannan yaran, kuma Allah ne gatan mu kaine gatan mu, bani da iyaye bansan ƴan uwana ba ina kake so naje, kayi haƙuri duk abinda naje na samu zan riƙa ajiye maka dan Allah" yayi ƙwafa batare da yayi magana ba ya nufi ɗakinsa, cikin sa sai ƙugi yake alamar yunwa, har ya kwanta ya sake dawowa har lokacin tana zaune dirshan a ƙasa cike da damuwa, yace " ƙuɗin gida da nace ku riƙa biya duk wata ki bani yanzu" tace " babu kuɗin Mai gida wallahi bani da ko sisi a hannuna, abincin da zamu ci da dare shi nake tunanin ta inda zan samu yanz.....tayi shiru sakamakon ɗauke ta da mari da yayi, duka yaran sai da suka razana, yace " wallahi sai kin bani kuɗina yau ko ki bar gidan, ni zaki raina wayau ki maidani mahaukaci, ina yi magana kimin ƙorafi, ko dan saboda ina ɗaga maki ƙafa ne, baki da lbrn Yasira matar Shamwilu har kuɗin ta take sakawa ta siye nama ta saka a girki saboda ta faranta ran mijin ta amma ke dussa wannan ta dabbobi kin kasa bani sai ƙorafi da bani haquri, haquri zan ci...... ta lumshe idanuwanta cikin ƙunar zucci, hawaye suka zubo,
Table of Contents