Chapter 18
Chapter 18
kayan su daga gidan sa, ta ɗauke kanta da sauri daga fuskarsa ita da yaran suka shige gidan Wadata. Shamwilu yace "Amma yarinyar nan ta gama raina ka abokina, har ta iya shigewa wani gida batare da ta gaida ka ba kamar fa bata ganka ba". Audi yayi Jim kafin ya sauke numfashi kaɗan yace "Ni fa zan dawo da Ummy" "Meyasa? Shamwilu ya tambaya a razane yana kallon sa cike da fargaba, Audi yace" saboda mata ta ce, bangane tana da muhimmanci a rayuwa ta ba sai da bata gidan nan na kwana huɗu rak, kasan Allah idan tayi wata bata gidan nan zan haukace saboda ina son ta sai ynzu na gane hakan" Shamwilu ya bata ransa, "kai haba kada ka bayar da maza, duk yaushe aka yi sakin, kwana huɗu Kacal me ka iya ganewa acikin sa yaushe ma ka gama hukunta ta har ta gane girman laifin da ta aikata maka, wallahi karya kake ba son ta kake ba kuma baza ka mayar da ita ba, saboda wane dalili ka saki mata shekaranjiya kace har kayi dana sanin da zaka mayar da ita". Audi ya dube sa da mamaki yace "mata ta ce ba matar ka ba, menene damuwar ka? Yace" babu, amma ina so ka sani gona ta da take hannun ka zan karɓa na siyar zan bawa ƴaƴa na jari zasu je can kudu kasuwanci" Audi yace "Shamwilu menene haɗin mgnr Ummy da gona, Naga kamar ka ɗauki zafi dan kawai zan mayar da ita, na ɗauka kai abokina ne da zaka ƙarfafa min gwiwa akan na mayar ita saboda ta cancanci haka, kai ne fa ka saka na sake ta". Da jin haka sai Shamwilu ya hau bakin sa, ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba sai fada yake yana zage zage wanda ya saka audi saukowa yana bashi hakuri, Shamwilu ya tashi ya fice cikin bacin rai, Audi ya shiga gidan sa zuciyar sa a dagule, yana jiyo dariyar yaran a gidan wadata suna wasa wanda basa samun damar yi a gidan sa tun suna yara ya hana su wasa da sake wa a gidansa, kullum idan ba suna taya maman su aiki ba to suna zaune suna hira sama sama, duk sai yaji babu daɗi, ya ɗauki turmi ya kai gun katanga da yake ba mai tsayi bace irin na ƙauye ya hau ya taka yana kallon yaran, sai ga Ummy ta fito daga wanka tun da ya ɗora idanunsa akan mazaunan ta yaji yana neman nutsuwar sa, jikin sa ya ɗauki karkarwa gab da zata shiga ɗakin Saratu ya ɗaga murya sosai yace "Wallahi na mayar da aure na, dama can sakin ba har zuciya nayi shi ba..... Jin muryarsa ya saka ta juyowa tana kallon inda yake leqen su, yaran ma kowane ya tsaya yana kallon sa cirko cirko, ya cigaba da faɗin " eh na mayar da aure na, maza maza ki tattaro yaran nan ki dawo dasu ɗakin ki, (ya dube su) kai maza ku shiga ku ɗauko duka kayan ku, ku dawo gidan uban ku ai nine uban naku saboda me zaku je ku zauna a wani gida. Meelah tayi caraf tace" Malam Wadata ne baban mu kai kuma ba baban mu bane dan haka bama son gidan ka mun fi son wannan gidan " Cikin bacin rai ya ciro takalmin ƙafansa ya jefe ta dashi da sauri ta kwace, yace" ungo nan, shegiya mai shegen iya yi, to ko zaki mutu nine uban ki nina haife ki baki isa ki canza ni ba, zaki dawo ki same ni gidan nan sai na yanke wannan bakin naki da kike turomin, ke Hadiza maza ɗauko min takalmin nan ki kawo min yanzu" da sauri Deejah taje ta ɗauki takalmin zata kai masa Meelah ta riqe ta "idan kika je zai riqe ki ya hana maki dawowa, bani nan", ta karɓa tare da jefa masa tsakiyar gidan sa, wani haushi da takaici ya taso masa a zuciya kafin yayi magana Ummy ta saka yaran duka ɗaki suka barshi nan tsaye yana leqen su, a zuciye ya sauko ya saka takalmin ya fita daga gidan kai tsaye fadar mai gari ya nufa, ya zauna yana faɗin "Ranka shi daɗe na kawo ƙarar Malam Wadata ne saboda ya ɗauke min mata ya boye a gidan sa bansan me yake nufi ba" Mai gari ya dube sa da mamaki yace "ba dai Ummy kake magana ba ko? Yace" Ita mana duk duniya bani da wata mata bayan ita kai ma shaida ne" mai gari yace "eh tabbas ni shaida ne akan ka saki Ummy, kuma da bakin ka kace ka barwa Wadata" ya sassauta murya yace "Ranka shi daɗe duk acikin bacin rai ne nayi hakan, Ina neman afuwa tun da na mayar da mata ta ya bani abata, ayi mashi magana ya bani mata ta ranka shi daɗe kum..... Yayi shiru sakamakon ganin Wadata yazo a fusacce, bayan ya gaisa da Mai gari yace" Ranka shi daɗe Ina ƙarar Audi Akan leƙen gidana alhali bana gida, kuma ko da ina nan bai kamata ya leƙamin mata ba" a firgice Audi ya dube sa yana faɗin "Matata na leqa ni ko matar ka idanuwana basu nuna min ba kuma banji ƙamshin ta ba" mai gari yace "laifine babba kaje ka leqa gidan wani...... ya katse sa da hanzari" ranka shi daɗe na karbi laifina abawa Malam Wadata haƙuri Akan kuskuren da nayi amma ya maida min mata, ya gayamin duka nawa ne kuɗin sa da ya kashe a asibiti zan biya sa yanzu" Wadata ya dube sa yana faɗin "Ummy bata son zama da kai a yanzu, kuma da zarar ta gama Idda ni ne wanda zai aure ta". TWO WRITERS EMPIRE ✍️✍️ Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa, FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira ɗari shidda shidda, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya.
Table of Contents