Chapter 14
Chapter 14
fuskar Shamwilu ya kau, yaji wani ƙunci a ransa batare da yayi magana ba yayi shigewar sa, Audi bai kula da yanayin sa ba saboda babu nutsuwa a tare dashi, yini ranar ana abu ɗaya gabaki ɗaya ta ƙarasa fita hayyacinta ta galabaita ainun, har zuwa washe garin ranar again haka ta kwana, Sai a lokaci suka yi tunanin ko zasu kai ta asibitin nan ƙauyen, yace "shi ko ƙwandala bazai kashe a kanta ba" Wadata da matar sa suka nemi taimakon wasu maƙota mata aka riƙeta da ƙyar take takawa duk nisan asibitin haka aka je da ita, Audi yana biye a bayan su sai mita yake ba wanda ya kula sa, yana kallo Wadata yake bayar da kuɗin sa idan aka buƙaci wani abu, sau biyu yana leƙa ɗakin haihuwa tare da sanar da ita kada ta kuskura ta haifa masa mace idan ba namiji ba, kowa sai kallon sa yake da mamaki, cikin hukunci na ubangiji da taimakon nurses ɗin aka samu ta haihu da ƙyar bayan wahalar da ta sha. TWO WRITERS EMPIRE ✍️✍️ Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa, FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira ɗari shidda shidda, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya. [8/3, 8:26 PM] J💕: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t *FARAR TASKA* Fertymerh Zarah 10 "Alhamdulillahi ta haihu" yaji ɗaya daga cikin masu karɓan haihuwar ta faɗa, yaran suka soma tsalle cikin murna, ya tashi da sauri ya nufo ungozumar yana tambayar "me aka haifa? Cikin takaicin halin sa tace" macece" ya buga wani ashar da duk wanda yake asibitin sai da ya dube sa, ya soma safa da marwa yana faɗin "Kai Ina bazai yiwu ba gaskiyar Shamwilu ne bani nake mata ciki ba, kai tsaye ya nufi ɗakin haihuwar, masu kula da asibitin suka hana sa, ya soma zage zage yana kumfar baki akan an hana masa ganin matarsa, har zuwa wannan lokacin Ummy bata san halin da take ciki ba, bata san me ta haifa ba saboda a galabaice take, sai barci take mai nauyi barcin gajiya, Wadata yayi magana da kansa akan a basu jaririyar zasu mata huɗuba tunda uban nata yace ya yafe, Audi ya ɗaga murya yace "da alama Kaine uban yarinyar kake fakewa da sunan taimako, shiyasa idan ƙwandala aka nemi ka bayar kake badawa jiki na rawa, dama ruwa baya tsami a banza, yau na ƙara tabbatar duka yaran nan da kake saka su makaranta kana kula dasu saboda ƴa'ƴanka ne" gabaki ɗaya gurin aka ɗauki salallami, Wadata ya yunƙura ya shaqo wuyan rigarsa cikin bacin rai, wasu maza suka riƙe shi "wannan kowa ya san mashayin giya ne a ƙauyen nan, ka sani babu kamar sa, Malam Wadata Meyasa zaka biye masa kayi faɗa dashi wanda babu tantama a buge yake duk wannan haukar da ka gan shi yana yi a yanzu". Maganar ta fusata Audi matuƙa wanda ta saka ya hau zage zage kamar ransa, hayaniyar sa ta tayar da Ummy da ƙyar ta fito tana dafa bangon ɗakin, Deejah ta fara ganin ta tana fitowa ta nufe ta da sauri tana faɗin "Innar'mu" hankalin kowa ya koma kanta, su Saratu suka ƙarasa suna mata ya jiki, jiri take gani ga jikin ta sai karkarwa yake alamar bata da lfy sosai har da yunwa ma a tare da ita, sai a lokacin ma'aikaciyar asibitin tace "kun bar yarinya ta wahala sosai a gida wanda yayi sanadiyar mutuwar yaron cikin ta..... Me? duk suka zaro ido suna kallon ta cikin mamaki, tace" eh yaron yazo babu rai Allah yayi masa cikawa, mahaifiyar kuma ta zubar da jini ana buƙatar jini a saka mata a yanzu" Audi yace "Amma kika ce mace ce ta haifa" taja tsaki batare da ta dube sa ba alamar bata da lokacin sa, hakan ya saka shi nufar ɗakin da Ummy ta fito da hanzari, yaron baƙi sidik kamar mahaifin shi babu inda yaron bai ɗauko Audi ba, jikin sa ya ɗauki rawa, ya taba jin jirin ya jujjuya shi ya tabbatar lallai da gaske baya motsi, ya mayar da kanshi qasa ya riqe qafafuwan sa a sama yana jijjigashi tare da faɗin "kai magaji, magaji Kai, kada kamin haka" ya kai hannu ya daki ɗuwawun jinjirin ko alamar motsi babu, sai ya fashe da kuka, kuka yake wiwi ya fito dauke da yaron, "wannan haɗa baki akayi domin a cutar dani saboda an ga na sami magaji sak Irina aka kashe shi, wallahi bazan yarda ba sai an bi min haqqin ɗana, bazan bar asibitin nan ba sai kun bani ɗana mai numfashi, Ina ganin motsin shi a cikin ta ko da muka zo da ita asibitin nan, yana motsi yana kuka a jikinta, ta yaya zai mutu" Iya ruɗewa ya ruɗe, yace "wallahi Naga sanda yake motsi kune kuka kashe shi da gangan, yaron da ko da muka zo da ita asibiti yana kuka acikinta, shauƙinsa ne ya saka ni biyo sa, ba dan ya kira ni Baba ba, da bazan zo ba, ajikina naji zaa haifamin magaji Sai ku ka rushe min mafarki na ku ka kashe min shi wallahi duk sai nayi shari'a da ku", ya cigaba da sharar ƙwallah yana kallon yaron, ɗaya daga cikin nurses ɗin tace "mahaifiyar yaron bata ganshi ba kafin kaje ayi masa sutura ka bayar da yaron ta ganshi saboda zata tsaya a saka mata jini" yace "Idan akwai wani shege da ya isa akan wannan ɗan yazo ya karbe shi hannuna yanzu, wallahi babu wanda zai ganshi acikin ku kuma Allah ya isa ɗana da aka kashe min" ya soma tafiya kowa gurin sai kallon sa ake kamar zararre, sai ya sake dawowa yana kallon Ummy yace "na sake ki saki ɗaya saboda ɗana da kike kashe min kuma kada ki kuskura ki je gidana macuciya azzaluma Allah ya isa", Nurse ɗaya tace "haba malam haba malam kai wane irin mutum ne marar hankali da imani, ya matar ka tana cikin hali irin wannan saboda baka da imani da tausayi kace ka sake ta duk wahalar da tash.....(ya katse ta) ke dallah rufa min baki wawiyar, ji ƙaton bakin ta yhen yhen yhen, gaki nan kin tsufa ba aure, kin rasa mashinshini, tsohuwar banza waye bai san ki a duk ƙauyen nan da maita ba, asibitin nan taku kowa yasan ke kike cinye duk wanda ya mutu yaron nan ma kece kika cinye shi kuma wlhy sai mai gari ya raba mu yau, ke ko aren kin yi balle kisan zafin haihuwa, kece baki da imani, har kike faɗa akan ..... Tace "Audi kada ka gayamin magana saboda a girme na girme ka da shekaru, kada ka min rashin mutunci saboda kaje ka cika ciki da giya wallahi zan saka ayi min maganin ka a gurin nan, ka ji min ɗan iska marar tarbiya, matar ka tana wani hali na neman taimako sai ka sake
Table of Contents