Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

A Gidanmu Take Book 1 Complete Hausa Novel – Ahmad’s Regret and Fateemah’s Mystery 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Mommy taɗago kanta tana kallon Beebah..... ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:49 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* *dedicated to my Eeshart❤️* *WATTPAD* Jiddahpretty *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* Page 35&36 "Tana zuwa ɗakin tashaƙo wuyar Beebah ta rinƙa zabga mata belt tana huci, Beebah taji wuya sai zazzare ido take ihunma takasa" Suna cikin haka Mommy tashigo ɗakin, taga Beebah a hannun Bintu sai zare ido take, ita kuma Bintu sai huci take tana zaneta, Mommy tayi saurin shiga ɗakin tana ƙoƙarin kwatan Beebah Amma takasa, Dataga Beebah tana jujjuya idanu Alaman zata suma, tafita a ɗakin da gudu tana ihu takira Baba me gadi da driver. Tace kuzo zata kasheta ranta yaɓaci dama haka take idan ranta yaɓaci, da gudu suka shiga ɗakin, sukayi kan Bintu suna ƙwatan Beebah Amma ina Rikon da Bintu tayi mata bana wasaba! "Da kyar da suɗin goshi suka ƙwaci Beebah, ai kuwa tanajin an saketa ta kwasa da gudu tayi cikin toilet ta kulle ƙofar" _Ahmad_ Ajmad ne yake tambayar Habeeb meyake faruwa awayar? Habeeb yace wallahi Ahmad narasa ganewa Bintu wani irin zuciya ne da ita idan ranta yaɓaci, tanada hakuri sosai Amma idan ranta ya ɓaci ba'a gane kanta, yanzu fa dukan Beebah takeyi kamar 'yarta, Ahmad yace ay dama haka me hakuri yake idan ranshi yaɓaci ba kyau, saidai kuyi ta mata Addu'a....... Kafin yakarasa yaji wayarshi tana kara, daya duba saiyaga sunan Abdul ne, yayi dariya yaɗau wayar, yace "hello dude ya kake?" ɗayan bangaren akace lafiya ya jikinnaka? Ahmad Yace da sauki, Albishirinka? Ahmad yace goro, nasamu matar Aure anan Adamawa, Ahmad yace kai banason ƙarya, yace wallahi nake faɗa maka kuma Aurenta zanyi insha Allah. kaima ina maka Addu'a kullum Allah yabayyana maka Fateemahnka idan har tana raye, idan kuma bata raye Allah ya musanya maka da mafi Alkhairi, Ameen cewar Ahmad cikin sanyin murya yayi maganar sukayi sallama. "Abdul abokin Ahmad ne yakasance me bashi shawara ako da yaushe, bayason damuwar Ahmad ko kaɗan, sannan yana taƙaicin yaga Ahmad yana tafiya da Abokanan banza, shima yana daga cikin masu bincikowa Ahmad Fateemahn shi". _Bintu_ Bintu takicin abinci taki yiwa kowa magana agidan, har na tsawon kwana biyu, abun yadami Mommy sosai yau ta tarasu a falon ta tanason ta sasantasu, zaman dasukeyin baya mata daɗi ko kaɗan. kuma haka akayi dan Bintu ta sakko Beebah kuwa tabata hakuri komai yawuce. Yau friday Bintu ce ta dami Abdul sai yazo gidansu, shikuma Abdul yana gudun wulaƙancin Beebah yace mata gaskiya yau bazan zoba Babyna, tace mishi dan me? Yace babu, tace idan badan wulaƙancin da Beebah tayi maka ba nasan bazaka ki zuwa ba! Yace mata Aa wallahi bahaka bane, tace to kazo, da Abdul yaga ta nace yace mata to zanzo Amma sai bayan juma'a tace tom. Haka akayi kuwa bayan juma'a saiga Abful yazo, yayi kyau yasa brown na shadda da hula brown yayi kyau sosai, Bintu kuwa tasa Abaya pink da gyallenshi tasa flat shoe pink tayi kyau kamar asace a gudu. Tana zuwa wajenshi yaji ƙamshin turarenta a hankali ya lumshe idonshi, ya buɗe yace "Tsarki ya tabbata ga ubangijin dayayi wannan halitta" Bintu tayi dariya har kumatunta ya lotsa tace godiya nake masoyina. Abdul yayi dariya yace ranki ya daɗe dolene yau nayi snapping naki ko ɗayane Bintu tarufe fuskanta tace banason hoto, Abdul yayi yayi ta ɓuɗe fuskanta taƙi, ahaka ya ɗauketa hoton ta rufe fuskanta da hanunta, tana dariya. Haka sukaci gaba da hirarsu cikin farin ciki, suna cikin hiranne Abdul yanata dariya, dan Bintu yau tana ta bashi labarai, kawai saiga Beebah tazo wucewa, da Alama mommy ce ta aiketa. Bintu tayi shiru zuciyarta tana bugawa tana tsoron kar Beebah ta wulaƙanta Abdul irin na rancan. Beebah tana isowa wajensu ta tsunkuya har ƙasa tace "ina wuni yaya Abdul".... ✍🗒️ *jiddah S Mapi* [6/23, 12:49 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!*🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *dedicated to my love ❤️* *WATTPAD* Jiddahpretty *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* Page 33&34 "A firgice mommy taɗago kanta tana kallon Beebah tace ke Beebah bakida hankali ne? Ya 'yar uwarki tana nuna miki saurayinta zaki faɗi maganan banza akanshi? Idan nakarajin irin wannan maganan daga bakinki saina ɓata miki rai tashi kibani waje" Beebah tafita a ɗakin, mommy tace kiyi hakuri Hassana na kinga 'yar uwar taki batada hali me kyau, bani hoton nashi nagani, Binta tace to saita nunawa Mommy hoton mommy tace kaii amma gaskiya sirikinan ya haɗu masha Allah ya sunanshi? Abdul inji Bintu, masha Allah Babban suna Allah yabarku tare, kuma Allah ya nunamin ranar Aurenku Ameen. _Ahmad_ Habeeb ne yasashi agaba yayi ta mishi nasiha, Ahmad yace nagode Habeeb Allah yabar zumunci. _HABEEB_ "Habeeb kuwa acikin zuciyarshi yana tunanin yafaɗawa Ahmad damuwarshi amma yana tsoron kar ayi mishi mumunan fahimta, azuciyarshi yace kai garadai nafaɗa mishi ko zai nema min mafita, Wani abu yace mishi Aa karka faɗa ka riƙe sirrinka, ba lalle bane kowa yayi maka kyakkyawan zato" Yana cikin tunanin yaji an dafashi, Ahmad ne yace "abokina kasan bana ɓoye maka komai a rayuwata? Habeeb yace eh, to kaima banason ka ɓoyemin komai inason kafaɗamin damuwarka, na lura tin Wancan zuwannaka kana ɓoyemin wani abu" Habeeb yace babu komai Ahmad dama wata 'yar matsalace agida amma in Allah ya yadda za'ayi solving nasu very soon. To Allah yasa Ameen _Bintu_ Yau ce ranan dasukayi da Abdul zaizo wajenta dan haka tasha wanka tasa atamfa ja da jar gyale sai jar takalmi tayi makeup, idan kaganta kamar kasace ka gudu. Abdul yazo gidansu Bintu anyi mishi tarba me kyau, Bintu ta ajeshi a babbar falo suna hira sai Abdul yace "Babe tinda nazo banga twins nakiba ki kirata mana mu gaisa". Bintu tace tom, saita ɗau waya takira Beebah tace kiseni a falon Mom, Beebah tace ok Jim kaɗan saiga Beeba tasha doguwar rigar material ja itama jar gyale tasa, tana zuwa falon ta tsaya akan Bintu tace gani, Bintu tace Abdul ne yakeso ku gaisa, tace to bagani ba! Bintu tayi shiru Abdul yace ya kike ƙanwata? Beebah tace Aa niba ƙanwar ka bace ni ƙanwar Habeeb ce, Abdul yayi dariya yace toya kike ƙanwar Habeeb? Tace lafiya "Yace ok saiya cire kuɗi yace gashi ko ƙanwar Habeeb, Beebah tace Aa ai gidanmu ba'a yunwar kuɗi. Ta juya tayi tafiyarta Bintu tayi shiru tarasa yazatayi, Abdul yace karki damu my dear nasan yaranta ne yake daminta karkiji komai. A rayuwar Bintu ba abinda tatsana kamar wulaƙanci haka suka ƙarashe hiransu da Abdul tarakashi wajen motarshi tace mishi sai yaushe Kenan yace gaskiya ba rana Babe, tace dan Allah kayi hakuri da abinda twins nawa tayi maka yace ba komai babe, haka sukayi sallama yatafi tana ɗaga mishi hannu. Tajuya tashiga cikin gida ta samu Beebah kwance suna waya da Habeeb, tana zuwa ta wupce wayar ahanun Beebah Tace "bakida hankali Ko? to yau zan koya miki hankali har Zaki wulaƙanta Abdul kuma kinsan shi zan Aura? Beebah tace bani wayata! Baza'abada

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});