Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

A Gidanmu Take Book 1 Complete Hausa Novel – Ahmad’s Regret and Fateemah’s Mystery 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yakama hanyan Kaduna, ko waiwayar Adamawa be karayi ba! "Abdul ne yaje gidansu Bintu yafaɗawa mommy abinda yake faruwa, aruɗe mommy tafito tashiga motar suka nufi Asibitin". _Bintu_ Bata dawo hankalinta ba har yanzu likitocine akanta, Beebah kuwa sai kuka take kamar ranta zai fita, Azuciyarta kuma tana Addu'an Allah yasa ba Aljanu bane suka shafi Bintu, Domin ita tana matsifar tsoron me Aljanu. _Ahmad_ Allah Allah yake yakarasa garin Kaduna, yama rasa me zai fara tinani a halin yanzu? Fateemahn shi yagani ko kuma idonshi ne yake mishi gizo? To Amma idan Fateemah ce ai zatayi mishi magana, to amma ita wannan tagudu, anya itace Fateemahn shi? Kodai kamane kawai? Komadai menene idan naɗauko Mommy da Fareedah zasu san komai, Yanata magana shi kaɗai kamar taɓaɓɓe, idan yatuna yanda tarike wuyanshi sai yayi murmushi.... ✍️🗒 *Jiddah S Mapi* [6/23, 12:51 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* *Dedicated to my love* *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *Wattpad* _Jiddah S Mapi_ Page 49&50 "Mommy suna zuwa Asibiti Beebah ta taso tazo wajenta, mom ce ta tambayeta meya sami Bintu? Beebah tace wallahi mom nima ban sani ba, Amma inada tabbacin Aljanu ne suka shafeta! Mom tace ke Beebah banason iskanci, kifaɗamin meya sameta ko kodai wani Abun Abdul yayi mata? Beebah tace wallahi mommy ba abinda aka mata kawai tana ganin Abokin Abdul damukaje ɗaukan hoto dashi tafara ihu wai ataimaketa zai kasheta" Mommy tace ina yake Abokinnashi? Mom tun lokacin data fara ihu yatsaya awajen yana nunata ko magana beyi ba To mukuma munbita, mun barshi awajen, Zuciyar mommy ce tayi matsifar tsinkewa!!! Atake ta tsunkuya dan wani hajijiya takeji, Tacewa Beebah kiramin Abdul yakaini inda kukabar mutumin, Beebah ce tace tom mommy lafiya? Mommy tadaka mata tsawa! Kiramin Abdul nace, Beebah ce tabar wajen da sauri dan ganin yanayin mommy. _Ahmad_ Gudu yake akan hanya, burinshi kawai ya iso KD dan jiyake kamar ba mai amotar, dayaga motar bata mishi gudu sai kawai yaɗau waya yakira Habeeb, yace mishi dan Allah ka nemamin jirgi yanzunnan, Habeeb ne yace ok kasameni a Airport, Ahmad yajuya motarshi yakoma Adamawa zuwa Airport, Yana zuwa yatarar da Habeeb harya karɓa mishi pass, Yamika mishi hannu suka gaisa, Yace yau ba surutu sauri nake, Habeeb abun yabashi mamaki taya za'ayi Ahmad yayi sauri haka? Duk yanda akayi akwai matsala. Mangariba cif yashiga garin KD, Yana sauka a Airport yafita da sauri yatari Napep, Yawuce sai gidan Mommynshi, Yana zuwa me gadi yahanashi shiga, Yarokeshi, megadin yace bazan yadda na rasa aikina ba Ahmad! Hajiya tace duk ranan dakazo nabuɗe maka kofa abakin Aikina, Amma Alfarma ɗaya zanyi maka Shine kazauna anan yanzu Fareedah zatazo dan hajiya ta aiketa, Idan tadawo saika faɗa mata sakonka.. Be gama magana ba, saiga motar Fareedah ta kunno kai, Tana ganin Ahmad ta ɗauke kanta tana kokarin shiga gida, Ahmad ne yayi mata Alama da hannu, yahaɗa hannunshi waje ɗaya Alaman yana neman Alfarma, Hakika Fareedah taji tausayin Ahmad yau, ganin duk yanda yabi ya rame yayi baƙi kamar bashi ba! Saita buɗe mishi ɗayar kofar tayi mishi Alama dayazo, Ahmad ne yasauke ajiyar zuciya, Yatashi yaje yashiga motar, Yana shiga megadi yabuɗe mata get tawuce ciki, Acikin gida ta tarar da mommy tana zaune tayi tagumi kamar kullum. Tana fita amotar tabuɗewa Ahmad shima yafito. Mommy kamar daga sama taga Ahmad acikin gidanta kuma amotar Fareedah, Tashi tayi ta iso inda suke, Tana zuwa ta fesawa Fareedah mari har guda uku, kana tace "Fareedah bakida hankaline? Kokin manta me nace miki? Ko kin fini son Ahmad ɗinne? " Fareedah tayi shiru. Ahmad ne duk jikinshi yayi sanyi, Har yayi dana sanin zuwa, Yatsuguna kasa zai fara magana mommy tace idan kasake kace uffan Allah ya isa! Fita kabarmin gida, Ahmad ne yafara kuka yace "Mommy nayadda zan fita nabar miki gidanki, Amma ina neman wata Alfarma? " Mommy tace "Banason jin komai daga Bakinka Ahmad kaficemin agida" Wannan karon Fareedah ma tasa baki a rokon mommy, Fareedah kuka Ahmad kuka, Kuma dukansu a tsunkuye suke, Mommy ce taga sun mugun bata tausayi, sai kawai itama tafashe da kuka ta tsunkuya tarike hanunsu ta ɗagasu ta rungume, Ahmad yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya, Rabonshi dayaji ɗumin jikin mommy tin lokacin da Daddy yarasu, Sun kai minti talatin ahaka kafin mommy tace kafaɗamin abinda yake daminka Ahmad? Ahmad ne yace "Mommy naga Bintu a Adamawa" Mommy ce tayi saurin rufe bakinshi da hannunta, Tace shiiii banason karya, karkayimin karya don kanason in soka, Ahmad yace mommy na rantse da Allah Bintu nagani, harda goshin sallahn ta Mommy tayi shiru, taya za'ace wanda yamutu ya dawo? Kodai Ahmad yasamu taɓin Hankali ne sanadin shaye shaye? Can tace idan har da gaske kake gobe zamuje Adamawan in tabbatar, Idan naje kuma naga karya kakemin, tofa bani bakai Ahmad, Yace mommy nayadda idan ba ita bace Karki kara yimin magana Kuma nima bazan sake zuwa inda kike ba! Fareedah tazama shaida. Mommy tayadda da sharuɗanshi sukasa niyyan gobe da safe zasu tafi Adamawa. ****** Mommy sunje wajen dasu Beebah sukabar Ahmad Amma basu ganshi ba! Mommy taruɗe tafita a hayyacinta, Da kyar suka kama hanya suka tafi Asibiti, Suna zuwa daidai Lokacin Bintu ta farfaɗo. Amma wani ikon Allah sai kallonsu take kamar bata sansu ba! Idan sunyi mata magana saita fara kuka, Likita ne yace sun duba sunga ba wani matsala zasu iya tafiya gida. Suna zuwa gida mommy takira Habeeb ɗakinta, Tacewa Habeeb "gobe zamubar garinnan" Kakiramin Abdul yazo muyi magana. Habeeb ya ruɗe yace, Mommy meyasa zamubar garinnan? bayan nanne mahaifarmu? Mommy tace banason dogon surutu Habeeb kayi Abinda na umarceka. Habeeb yayi shiru, can yace kuma Mommy kikace gobe? Mommy tace da Asuba ma kuwa... _✅ote, comment and share pls_ ✍️🗒️ *Jiddah S Mapi* [6/23, 12:51 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to all my fans_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *Wattpad* _Jiddah S Mapi_ Page 51&52 "Washe gari" Mommy ce tacewa su Beebah sushiga mota zasu koma Gombe, Beebah tace "yanzu mommy kina ganin idan muka bar garinnan ba damuwa? Kituna fa mun saba da mutane anan, Bakya tunanin muje can mushiga wata rayuwa? " Mommy ce ta dakatar da ita da hannu tace "Beebah bakisan damuwan dazamu shiga anan idan har muka Zauna yafi nacan bakoh? " Beebah ce tace "Mommy wace irin damuwa zamu shiga? Kodan Bintu bata buɗi baki tayi magana bane haryanzu? Mommy kika sani ko iskokai ne suka shafeta?" Mommy ce tacewa Beebah wannan maganar taki ɓatamin lokaci kawai kike, Kishiga mota kawai mutafi. Beebah ce tashiga motar badan taso ba! Bwyan sun shiga mota gaba ɗayansu, Driver yaɗauki hanyar barin garin Adamawa, Beebah kuka takeyi sabida ko sallama basuyi da kawayenta ba, Mommy ce take bata hakuri tana lallashinta har tayi shiru. _Ahmad_ Suna idar da sallahn Asuba suka kama hanyan Adamawa, Amma mommy tace subi flight na safe, Suna zuwa Airport, daidai lokacin da aka

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});