Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 11

Chapter 11

A Gidanmu Take Book 1 Complete Hausa Novel – Ahmad’s Regret and Fateemah’s Mystery 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ne yau ake shirye shiryen karɓar kaya, inda Mommy tayi namijim ƙoƙari wajen ganinta ƙayata abun, Abinci musamman akayi daga gidan Abincin Mommy, yayinda aka dafa abubuwa masu daɗi da ban sha'awa aka zuba a take-away, drinks kuma ba'a magana mommy tayi ordernsu kamar ba gobe. (Azuciyana nace wannanma ba ranar Auren ba) An kawo kaya komai yayi daidai inda akayiwa Bintu kaya nagani nafaɗa, kowa yasa Albarka anyi mata fatan Alkhairi. Abdul ne yabijirowa Bintu da maganar pre-wedding pics, Bintu taje sama ta sakko kasa tace bazatayi ba! Hakan ya fusata Abdul har yayi fishi da ita kota kirashi baya ɗaukan kira. Abun yadami Bintu, tasamu Beebah tayi mata bayanin duk abinda yafaru, Beebah tace Abu me sauƙi basai kitura mishi text kice kin yadda zakiyi ba, Idan yazo saimu tafi tare inyaso sai ayi dani. Thats my sisterluv inji Bintu tabawa Beebah hannu suka tafa tace hakan kuwa za'ayi.. _✅ote, comment, and share pls_ ✍️🗒️ *_jiddah S Mapi_* [6/23, 12:50 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to my love_ *WATTPAD* Jiddahpretty *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* Page 41&42 " hakan kuwa akayi data turawa Abdul message aranan yazo suka ɗibi kaya sai wajen ɗaukan hoto, Dasukaje ɗaukan hoto akace Bintu tashirya, Bintu tace itafa bazatayi wani hoto ba sabida bidi'a ne, amma ayi da Beebah tinda su 'yan biyu ne, Da farko Abdul yaki amma dayaga Bintu ta nace kawai saiya amince suka ɗau hotunan" Beebah kamar itace Amaryan dagaske, tayi kyau bana wasa ba, Sunyi hotuna kala-kala ciki harda wanda Beebah tariƙe wuyan Abdul, da wanda yaɗan sunkuyo daidai wuyarta, sunyi kyau matuƙa fiye da tsammani. "Ahmad yana kwance akan gado yana ɗan chat da Abokinshi Habeeb, sai kawai yaji karan message. daya duba message ɗin saiyaga Abdul ne yatura mishi hotona, daya buɗe hotonan saiyaga Abdul da wata fine girl, sunyi kyau sosai, Yacewa Abdul gaskiya kunyi kyau Amaryar taka kyakkyawa Allah yabada zaman lafiya. "Ameen" cewar Abdul. _Bintu_ Ita kuwa Bintu dilki akeyi mata lagadan ba ajalan ba, Beebah ma tace sai tayi dilkin tare suke dilkin sunyi kyau bana wasa ba, idan kagansu kamar larabawa. *************** "Lokaci yaja kwanaki sun wuce, kamar yadda akasa date na Auren Bintu Da Abdul hakan kuwa akayi yau Alhamis, za'ayi kamu, a wetline dake cikin garin Adamawa" Bintu da Beebah anko sukayi sunsa doguwar rigan material jaa ne yalƙi sunyi makeup idan kaga Bintu zakace ba 'yar nan kasan bace kamar balarabiya Ƙawayensu kuwa sunsa Pink na dogayen riga plane material sun ɗaura kansu da baƙaken ɗan kwali, Abun ba'a magana. Hall ɗin da aka kama musu an ƙayatashi da kayan kyale kyale, Wajen yayi kyau, Abokan Ango sunsa baƙin shadda dayaji zubi Abun saidai kawai ayi shiru. Can nahango Beebah da Bintu suna musu, Bintu ce tace ita bazata iya zama acikin mutane ba! Beebah kuwa tace ay bata isaba! suna cikin musune Bintu dataga sun dameta sai kawai tajuya tafita a hall ɗin, daidai lokacin da MC. Yafara cewa ana neman amarya afili. Gashi Bintu tafita, ƙawaye sai juye juye suke sun rasa ya zasuyi,gashi MC. Yanata kiran Amarya, da Beebah taga haka sai kawai tafara tafiya Zuwa wajen Ango tana shiga tsakiya zata wuce taji MC. Yana cewa atafawa Amarya. "kawai sai taji wajen ya ƙaure da tafi, Abdul yana zaune yana kallon ikon Allah yarasa meyake faruwa, MC. Yace ana neman Ango afili" Abdul ne yatashi jiki amace yana Zuwa wajen MC. Yanaso yace ai ba ita bace Amaryar Amma yana zuwa daidai tsakiyan fili yaji ance atafawa Ango da Amaryarsa waje ya kaure da tafi ana ihu. MC. Yace Anaso ango yayi rawa da Amaryarsa rawa irinna nuna farin ciki da farko dai ango yakama hanun Amaryar tashi su shigo tsakiyar fili yanda baƙi zasugansu da kyau... _Ahmad_ Ahmad kuwa sauri yake ya isa garin Adamawa sabida Abdul yadameshi da kira, gudu yake akan kwalta kamar zai tashi sama, yana duba agogonshi yana kara spirit. _Bintu_ Bintu kuwa tana fita a hall ɗin napep takama ta tafi gida dan tafara jin kanta yana ciwo. Tana zuwa gida tawuce zata shiga ɗakin mommy taga mutane dayawa, kawai saita juya tawuce ɗakin Habeeb. Amma me? Tana shiga ɗakin Habeeb taganshi yarungume hoto yana kuka kamar ƙaramin yaro. Tayi sauri ta karata cikin ɗakin tana me kiran yaya Habeeb yaya Habeeb meya sameka kake kuka? Habeeb ne yayi saurin ɓoye hoton yana share hawayrnshe. Yace Bintu na meya dawo dake gida ana tsaka dayin kamunki? Yaya ni wallahi banason wannan hayaniyar ne tana sani ciwon kai. yaya meya sameka kake kuka? Kuma hoton waye ka ɓoye abayanka? Habeeb yayi shiru can yace Babu komai Bintu na, wannan wani sirri ne nawa dana ɓoye bana so kowa yasani harsai ranan da Allah yakarɓi rayuwata, Bintu tace yaya meyasa kake irin waɗannan maganganun yau fa ranar murna ce sanin kanka ne nice farkon da mommy tafara Aurarwa agidannan. be kamata ka zauna acikin baƙin ciki ranar Aurena ba! Kamata Ai farin ciki zakayi, Habeeb yace to Bintu insha Allah zan daina damuwa". yanzu ina kika bar su Beebah da Abdul? Bintu ta shagwaɓe fuska tace "suna wajen kamu". _Hall_ "Abdul da Beebah ba sun rasa yanda zasuyi haka suka daure suka shiga fili sunata caskalewa, Abdul yariƙe hanun Beebah suna rawa kamar 'yan india, Abokansa kuma suna watsa kuɗi kamar ba gobe. _Ahmad_ 3:30pm cif yashigo garin Adamawa, bai tsaya ko inaba Sai a babban hotel na garin, yana zuwa yabiya kuɗin ɗaki aka bashi key yawuce, yana shiga cikin ɗakin ya ajiye kayanshi akan gadon yabuɗe toilet yashiga yayi wanka, yana fitowa daga wanka yashafa lotion da turaren jiki me kamshi, yataje suman kanshi, ya ɗauko wata baƙar shadda me kyau wanda tasha adon jaa ajiki, yasa jan hula, yaɗauko jan Agogo da takalmi jaa yasa, idan kaga Ahmad zakace balarabe ne, kamar asace a gudu yayi kyau har yafi kyau kyau awannan rana. "yayi sauri yaɗau makullin mota yabuɗe ɗakin yafita, Yana fita harabar hotel ɗin kallo yakoma sama, kowa idonshi akan Ahmad, wani dagacan gefe yace inama ace nine wannan. Jin hakaAhmad yajuya yace mishi bawan Allah ka godewa Allah aduk inda ya ajiyeka, ni nan dakasan matsalata da bazakaso ace kasanni bama balle ace kaine ni". Yana gama faɗan haka yajuya yayi tafiyarshi, wajen parking na motoci yanufa, yana zuwa yashiga baƙar motarshi kirar land-rover. ya tada motarshi yanufi hanyan wetline wajen kamu. Yana zuwa yayi parking yashiga cikin hall. Dashigarshi hall ɗin kallo yakoma sama, kowa yana kallonshi maza da mata. "MC ne yace ga babban abokin ango atafa mishi, waje ya kaure da tafi, ana ihu MC. yace muna neman amarya da ango dakuma babban abokin ango afili" Beebah tinda ta ɗaura idonta akan Ahmad taji zuciyanta ya buga, gayen ya birgeta infact wankanshi ne yafi tafiya da imaninta, MC. Ne yasake cewa muna jirnku, Ahmad ne yafara fitowa kowa sai kallonshi yake, nan Beebah da Abdul suka shigo, Beebah tana shiga fili tawuce wajen Ahmad tana rawa da jikinta kamar wata 'yar india, Ganin haka Ahmad yafara rawa shima yana watsa mata kuɗi,

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});