Chapter 8
Chapter 8
TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *jiddah S Mapi* _Dedicated to All my fans💋_ *WATTPAD* Jiddahpretty Page 29&30 "Polina tana ganin mutum ta buɗe ƙofa kuma ta faɗi kasa take, sai kawai tadiro akan gadon ta tsala ihu, Alokacin Bash yadawo daga siyan abinci yaji ihun polina amma shi yazata iskanci ne kawai" Polina takara zabga ihu tana cewa azo ataimaketa, Bash yatashi da sauri yaje bedroom ɗin, yaga mom akwance ƙasa kamar ba rai, ai da gudu yaje frij ya ɗauko ruwan sanyi yazo wajen datake kwance. *BINTU* "Bintu ce kwance akan gado tana chatting awayarta kirar samsung, yayinda Beebah take kwance agefenta tana bacci., Bintu ce tanaɗawa Beebah duka tace ke tashi kiga nayi saurayi sabo Haɗaɗɗe, Beebah ta tashi tana matsifa Waike bakida hankali ne Bintu? ya mutum yana bacci zaki tadashi? Bintu tace ke dallah tashi kiga wani saurayin dana haɗu dashi a IG. Beebah ta tashi tana tsaki". Bintu tace kalleshi fa gayen ya haɗu wallahi yashiga raina lokaci ɗaya. Beebah taga hoton gayen ya haɗu gashi kamar ɗan india, atake taji zuciyanta ya buga, Sai kawai tayi tsaki ta tashi tabar ɗakin Bintu kuwa tayi shiru tana mamakin halin 'yar uwar tata. ******************* "Bash ya zubawa Mommy ruwan sanyi ahankali tasauke ajiyar zuciya, tafara buɗe idonta tana salati. polina kuwa sai rarraba ido take, Ahmad kuma baya hayyacinshi amma yaji an fara lasa mishi zuma kuma an daina, kawai saiya fara kiran sunan Polina a hankali, dayaji shiru saiya tashi akan gadon yana dafa bango har ya iso inda polina take ita dasu mom. polina tace my Ahmad sai kawai Ahmad ya rungumeta yafara shafa jikinta, polina tanajin haka tafara biye mishi a idon mommy, mommy kuwa tana ganin Ahmad abuge yana neman mace a idonta takara sumewa awajen". Bashir yatsaya sokoko yana ganin ikon Allah, yakara zubawa mommy ruwa afuska tana farfaɗowa tacewa Bash yakaita Asibiti, da kyar take iya tafiya harta shiga motarta tabawa Bash makulli suka ɗau hanyar Asibiti. Suna zuwa Asibitin Doctor yagwadata yace "gaskiya Hajiya am sorry to say kinada hawan jini wanda yayi chronic ajikinki idan har kikasa damuwa aranki zaki iya rasa rayuwarki!" Mommy tace nagode Doctor insha Allah zan kiyaye. "Alokacin da Ahmad yadawo hankalinshi sai yaga Bash bayanan amma yaji karan ruwa a toilet, kuma yasan Bash bazeyi wanka ahalin yanzu ba sai dai idan 'yammata yakawo. Yana wannan tunanin yaji karan buɗe kofa a hankali yaɗago kanshi yana kallon kofan, nan yaga polina tana fitowa daga ita sai towel, taƙaraso kan gadon tana yauki, tace "well done my Ahmad gaskiya yau ka jiyar dani daɗi sosai" Ahmad yayi shiru yasan polina ba karamar karuwa bace ba abunda bazata iya ba gara yayi maganinta tunda wuri. "Yatashi akan gadon kamar be damuba yaje wajen kayanshi yacire belt" Polina tana son tamaida kayanta taji duka kamar tayi hauka tsabar zafi Ahmad yadinga watsa mata Belt tana ihu, Dataji zafi yakai zafi ta kwasa da gudu tayi hanyar waje, Ahmad yasa mata ƙafa tafaɗi ya taka ruwan cikinta sai kawai ta suma yaje frij yaɗauko ruwan sanyi me ƙanƙara yazo ya buɗe marfin goran yana tsaye yafara watsa mata ruwan, ta buɗe idonta da karfi tana ihu yakara watsa mata belt yace kimin shiru. Ubanwa yakiraki? Tace Bash ne, yace me kikamin? Tayi shiru ya kara watsa mata belt, dataji azaba saita fara faɗa mishi duk abunda yafaru, Ahmad yanajin haka ya haukace da dukan polina idan taji azaba saita suma idan yawatsa mata ruwan sanyi ta farfaɗo yakara fara dukanta, da kyar polina taja jikinta tafita agidan. "Yana ganin tafita yaɗau makullin mota yanufi hanyan gidan Mommy, Yana zuwa yayi parking a kofan gidan domin yasan ko yayi horn megadi baze buɗeba dan Mommy tahana" Yana fita a motanshi yaga motar mommy ma ta tsaya abakin kofar, sai kawai ya daƙe ze wuce cikin gidan, yasa kafarshi na dama kenan yana shirin sa nahagu acikin gidan yaji muryan Mommy tana cewa "idan ka kara taku ɗaya daga inda kake kashiga gidannan Allah yatsine maka Albarka!!! Ahmad yatsaya da ƙafa ɗaya asama ɗaya akasa, ya kasa sauke ɗayan kafarshi..... ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:48 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to all my fans_ *WATTPAD* Jiddahpretty *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* Page 31&32 "Ahmad yakasa juyawa, mommy tace Ahmad ta sanadin baƙin cikinka mahaifinka ya mutu, ka kashe 'yar mutane yarinya me hankali, sannan nima yanzu naje an gwadani ance inada hawan jini, kaga saura ni idan ka kasheni, saika kashe Fareedah ko? To baka isaba, kayi kaɗan bazaka kasheni ba! Ahmad idan ka kara taka gidannan Saina tsine maka! Kafice kabar anguwannan ma gaba ɗaya banson ganinka, Ahmad ya durkusa akasa ya rike kafan mommy yana rokon gafara". Mommy ta tureshi tashiga gida tana me taƙaicin Ahmad, Haka Ahmad yatafi gida yana kuka kamar ranshi yafita, Yana zuwa gida ya buɗe frij ya ɗauko kwalban giya yafara sha kamar ba gobe. *HABEEB* Habeeb tin ranan daya bar gidan Ahmad yashiga bincike kullum yana hanyan gidan marayu yana tambayansu ko akwai wacce aka tsinta? Domin shi jikinshi yana bashi Fateemah bata mutu ba! Ko Mommy batasan yana bincike ba haka ze shirya yace ze tafi makaranta Amma yana fita ze tafi nemawa Ahmad Fateemah, karatunshi yaɓaci baya attending na class, yazama busy wajen nemawa abokinshi matarsa. Duk da shima yanada nashi damuwan amma yana ganin damuwan Ahmad yafi nashi. "Yau takama ranar juma'a babbar rana Habeeb ne yayi shiri yacewa mom ze koma makaranta mommy dasu Beebah suka haɗa mishi kayanshi, suka rakashi wajen motarshi yatafi" Habeeb gidan Ahmad yanufa A Kaduna yana zuwa yatarar da Ahmad yana bacci Alamun yashawu, haka ya zauna yayi musu girki ya zuba a flask yashiga toilet yayi wanka yayi alwala, yana sallah Ahmad yatashi daga bacci, yace wow suprise Habeeb agidana yau kai naji daɗi, shima yatashi yashiga toilet yayi wanka yayi alwala yazo ya tada sallah, bayan sun idar da sallah ne Habeeb yakalli Ahmad yace "Ahmad kayi min alkawarin bazaka kara shan abu ba! amma nazo naganka a buge meyasa? Ahmad yayi shiru, Habeeb yace tambayarka fa nake? "Ahmad yace Habeeb bazaka ganemin bane, haka yabashi labarin duk abinda yafaru, Habeeb shiru yayi dan Ahmad yamugun bashi tausayi, yaƙarasa dacewa Habeeb mommy ta tsane ni! Gara nayi ta shan giyar ina neman matan ko zanji sauki a raina. Aa Ahmad karkace haka shan giya ko neman mata baya ragewa mutum baƙin ciki da damuwa karatun kur'ani shine idan kayi zaka samu sauki aranka." *BINTU* Bintu sunyi nisa a soyayyarsu da saurayin data haɗu dashi a IG a halin yanzu har maganan aure yafarayi mata, inda tace mishi yashigo gidansu asanshi tukunna. Yace mata insha Allah zai shigo ayi magana. Beebah idan taga Bintu tana chat da mutumin sai taji ranta yana ɓaci tarasa meyasa Gashi kuma Bintu kullum suna tare awaya. Yau suna zaune afalo da mommy, Bintu tacewa Beebah zokiga hotunan my Abdul kinga yanda yayi kyau, Beebah tamatsa kusa da ita tana kallon hoton, taja tsaki tace "kiga yanda yake dariya kamar ɗan tsintuwa yasamu gidan masu kuɗi"... Afirgice
Table of Contents