Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

A Gidanmu Take Book 1 Complete Hausa Novel – Ahmad’s Regret and Fateemah’s Mystery 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tafiya" Bayan an sallamesu ne suka koma gida, Daddy ya kira Hajiya Mariya yayi mata bayanin abinda Doctor yace, Yace "Mariya bakya ganin kawai mu haɗa Auren Fateemah da Ahmad? Tunda mun yadda da tarbiyanta, To Alhaji ne dai banƙi ta taka ba Amma baka tinanin karmu shiga haƙƙin yarinya marainiya, Kaga Ahmad shi bawani isashen hankali ne dashi ba kar muzo muyi abinda zai damemu, Haba Mariya shi Ahmad ɗin ba haifanshi akayi ba? Tunda haifanshi akayi ai munada iko dashi. To Alh Allah yasanya Alkhairi cewar Hajiya Mariya. Dahaka Daddy yasanya ranan Auren Fateemah da Ahmad, suma kansu basu sani ba! ******************** Akwana atashi ba wuya a wajen Allah yau ne Ranan juma'a wanda yayi daidai da yanda Alhaji Kabeer yasa ranan Auren Fateemah da Ahmad, Fareedah da Fateemah sai ganin mutane suke suna shiga gidan suna ta guɗa. Fareedah ta tambayi Mommy meyake faruwa mommy tace ba komai, Shi kuma Ahmad yana wajen Abokansa sunata shashancinsu, inda suketa shaye shayensu, Bayan juma'a aka ɗaura Auren Fateemah da Ahmad, akan sadaki dubu Hamsin wanda Alh Kabeer ne yabiya, Se dare Ahmad yadawo gida, Daddy ya kira wayanshi yace "kasameni a falo" Daddy yacewa Hajiya mariya takira mishi Fateemah da Fareedah, Bayan sun hallara a falonne, Alh Kabeer yayi gyaran murya yace "Da farko dai nasan yau zakuyi mamakin yanda mutane suketa zirga zirga agidannan, to yau Aure aka ɗaura, Auren Fateemah da Ahmad". A razane Ahmad yaɗago kanshi yana kallon Daddy, Ya buɗa baki zaiyi magana Daddy ya ɗaga hannu yace "Banason jin komai daga bakinka kuma babbar kuskuren da zaka aikatamin shine sakin Fateemah ko wulaƙanta ta" Sannan kuma daga gobe zata tare zuwa side naka, Idan naga yanayin zamanku ba matsala kuma idan kun fahimci junanku saiku koma gidanka na jambutu, Yace zaku iya tafiya. "Tofah dahaka suka wuce ɗaki kowa jikinshi a mace, Ita kuma Fareedah murna take kamar me, suna shiga ɗakin ta rungume Fateemah tana ta tsalle, ita kuma Fateemah shiru kawai tayi ta rasa me zatayi, Dahaka Fareedah tafara haɗa mata kayanta tana cewa gobe a ɗakin yaya zaki kwana kai ammafa i will miss you, Fateemah shiru tayi batayi magana ba tana ganin anya bazataje wajen Daddy tace a raba Aurennan ba? , Kai idan tayi haka kuma batayi daidai ba domin sunyi mata halacci" Azuciyar Ahmad kuwa yanata kulla salon muguntar daze yiwa yarinyan, Lalle zakici ubanki Ai nagodewa Allah ma dayasa babu Wanda yasani acikin abokai na dako nasha kunya, Ina yaro dani ace nayi Aure ay Akwai raini. "Haka Fateemah da Ahmad suka fara rayuwa, Inda Ahmad yake mugun takura Fateemah, idan dare yayi sai yayi ta sata tsallen kwaɗo kuma yace idan ta faɗa saiya kasheta, Haka Fateemah tayi ta hakuri dashi idan Fareedah tashigo saita saki fuska tayi ta dariya idan suna hira, Amma da zarar taji muryar Ahmad tofa zuciyarta tafara tsinkewa kenan" "Dahaka Fateemah tayi ta hakuri da Ahmad wulakancin yau daban na gobe daban haka zatayi ta hakuri dashi, babban abinda yafi daminta dashi shine shaye shaye dayakeyi, tanason tafaɗa ma Fareedah amma tana mugun tsoronshi dan yace mata idan ta kuskura tafaɗa wa iyayenshi yana shan abu saiya kasheta!" Me karatu Fateemah tasha wahala a wajen Ahmad fiye da misali. Yauma kamar kullum Ahmad ne yashigo gidan A buge yana tafiya yana tangaɗi, Fateemah kuwa tana kitchen tana itada Fareedah suna girki, Kawai se sukaji karan buga kofa Fareedah tayi sauri zata je taduba ko menene, Fateemah tayi saurin katseta. Tace ki bari zanje naduba dan ita tasan halin Ahmad may be yaje yasha abune yadawo, Tana leƙa ɗakinshi taga ya kwanta rub da ciki. Ai kuwa tarufeshi a, Dataje kitche tacewa Fareedah ay ba kowa. "Tofah har dare Fateemah kwata kwata ta manta da ta rufe Ahmad a ɗaki, haka Har tayi abincin dare ta ci tayi wanka ta kwanta har bacci yafara ɗaukanta, amma taji zuciyanta yanata tsinkewa tarinka cewa astaghfurullah! Shi kuma Ahmad lokacin da ya dawo hankalinshi yayi wanka yanason yaje club amma me yana buɗe kofan yaji gumm! Ya rasa yanda zeyi gashi yanajin yunwa kuma ana ta kiranshi awaya club yacika saura shi kawai ake jira, Yadinga buga kofan yana kiran sunanta amma shiru. Haka ya zauna yana tuna abinda zeyi mata yau idan ta buɗe kofan, Wato raini yafara shiga takaninsu kenan! tana zaune kawai ta tuna yau Ahmad be zageta ba anya lafiya kawai seta tashi tafita tace bara na lekashi nagani, Tana zuwa taga kofanshi a rufe, taɗan buga ƙofan kaɗan. Kamar jira yake yace waye tayi shiru, yace oya open the door Sai alokacin ta tuna abundance yafaru da rana😳ta zaro manya manyan idanunta tace kayi hakuri zan buɗe na mantaka ne wallahi, Cabɗi ni ta manta? ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:47 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *jiddah S mapi* _Dedicated to my lovely daughter AFRAH_ _✅ote me on wattpad Jiddahpretty_ Page 19&20 "Yace taɓɗi ni ta manta lalle zataci ubanta, ai kuwa da gudu Fateemah taje taɗau malullin ɗakin tazo ta baɗeshi" Tana buɗewa taji mari tass, dan ubanki ni kika manta! Gidan ubanki ne? Dazaki rufeni kice kin manta yau sena nuna miki kuskurenki! Ya rike hanunta da karfi yana janta Yabi ta kofan baya da ita ya buɗe motarshi yasata aciki, yafita da gudu acikin gidan, "Yana gudu tanata bashi hakuri shi kuma hakurin datake bashi yana kara bashi haushi" Dahaka har ya iso wani gida, Tangameme me Ƙaton get yayi parking, Yafita agidan da kanshi ya buɗe get ɗin yashiga cikin gidan yace mata fita! Tafara cewa dan Allah kayi hakuri wallahi mantawa nayi. Yau zakisan kin manta ni! Haka ya ɗauke ta a motan Ya fita da ita Yana ɗaukan ta be ajeta ako ina ba se a wani bedroom wanda ya kayatu da abubuwan kyale kyale, Haka tana gani yafara yayyaga kayan jikinta tana bashi hakuri amma ina. Haka Ahmad yayiwa Fateemah fyaɗe (eh mana ai wannan fyaɗe ne), Haka Ahmad ya ɗauki Fateemah A sume yasata a mota ya kama hanya, Saida yayi tafiya me nisa kadin ya tsaya ya buɗe motar yana daga ciki ya cillar da ita waje yaja motarsa ya tafi. **************** "Bayan Ahmad yakoma gidane ya fara wani tinani me ze faɗawa Daddy idan ya tambiyeshi ina Fateemah, kai anya bazan koma in ɗaukota ba! Kodai nabarta ne! *(Nace duk kai kaɗai)*" Haka yayi wanka ya kwanta yayi baccinshi, Washe gari da safe Fareedah tazo ɗakin dan takirawa Mommy Fateemah, Tana zuwa tayi knocking, yace waye? tace Fareedah ce yace mene ne? Tace mommy ce take kiran Fateemah! Dumm yaji zuciyarshi ta buga, Kije ina zuwa tace toh, Yana zuwa ɗakin mommy yace "inakwana mommy" Tace lafiya ina Fateemahn? Yace Fareedah fita ki bamu waje, Fareedah tafita yasamu bakin gado ya zauna, Yace Mommy wato yarinyannan ta rainani ne jiy ta kulleni a ɗaki har dare wai ta manta ni, Shine me? Inji mommy, Yace shine itama nakaita inda za'a manta da ita! kana hauka ne ko ka fara shaye shaye ne? Yayi shiru, Ina ka kaita? Yace bayan gari, Ji kake tass tass tass Mommy ta wanke shi da mari har sau uku, kayi hauka ko? Yayi shiru ba magana nake maka ba? Shiru

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});