Chapter 10
Chapter 10
ba! Ki ƙwace Beebah tafara ƙwatar Wayar suka kwashe da dambe! _HABEEB_ Habeeb suna waya da Beebah yaji duk Abinda sukeyi yanatayi Musu magana su daina amma ina sai ihun Beebah yakeji alamun tana dakuwa, aranshi yace me hakuri fushinshi babu kyau! Beebah bakaramin duka takesha ba awajen Bintu, gashi bakinta baya shiru, tana ta zagin Abdul, da Bintu taga Beebah ba shiru zatayi ba saita fita falo ta tsinƙa sucket na TV tashiga ɗakin da gudu... ✍️🗒️ *jiddah S mapi* _pls share🙏🏻_ [6/23, 12:49 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* *dedicated to my love❤️* *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *Wattpad* _Jiddah S Mapi_ Page 37&38 "Abdul ya saki baki yana kallon Beebah a Azuciyarshi yace wataƙila ma sabon salon iskancine takoya zatayi mishi, taƙara cewa ina wuni yaya Abdul, Abdul yace lafiya kanwar Habeeb ya kike ya gida? Tace lafiya lau yaya, Yace ina zuwa haka? Beebah tace Mommy ce ta aikeni G.R.A zan kai aika, yace ok dama nima tafiya zanyi me zai hana na sauƙe ki acan? Tace tom nagode, Abdul sukayi sallama da Bintu yashiga motar Beebah ma tashiga suka tafi" A hanya Abdul yake tambayar Beebah yace "ƙanwar Habeeb meyasa kika sauya alokaci ƙanƙani? " Beebah tanason tayi mishi rashin mutunci Amma tana tsoron karya faɗawa Bintu takara shan dukan mutuwa. Tace mishi babu komai yace "ok" yaje ya ajeta a G.R.A yayi tafiyarsa. _Ahmad_ "A kwana biyun da Habeeb yazo wajenshi yaɗan samu sauƙin abunda yake daminshi, Amma har yanzu bai dawo daidai ba, yau yaɗan buɗe data yace bazi yaɗan ganin Abunda yake tafiya a social media, yana buɗe datan yaɗan aje wayar sabida messages ɗin sugama shigowa, bayan wasu 'yan mintuna yaɗauki wayar yana duba messages na abokai da kuma 'yan uwanshi saiya shiga message na Abdul wanda yaga hotone yatura mishi, yana buɗewa yaga hoton wata faran yarinya doguwa tsiririya ta rufe fuskanta tana dariya da Alama batason hotonne aka ɗauketa, Duk yanda yaso yaga fuskarta yakasa" Yabuɗe voice chat ɗin da Abdul yayi mishi yaji Abdul yace "dude ga hoton matana danake Auran" Ahmad yayi mishi reply da Allah yasa ka Aureta dude, yatura mishi. _Bintu_ "A duniya ba abinda takeso sama da Mommy dakuma Abdul yanzu har maganan Aure yashiga, domin Abdul yaturo iyayenshi anyi magana, ansa rana, wata biyu masu zuwa, idan an ɗaura Aure kuma a kaduna zasu zauna". ************* "Yau Da daddare mommy tashiga ɗakin Habeeb Tanason tambayarshi maganin ciwon kai, Amma me? Tana zuwa ɗakin taga Habeeb yarungume hoto yana kuka Kamar ƙaramin yaro, be maji shigowarta ba! "A hankali tajuya tafita a ɗakin ta tsaya a window tana leƙanshi, sai kuka yake harda sheshsheƙah, yana kukan yatashi yaje wajen kayanshi, ya ɗauko wani frame pink colour me kyau yasa hoton aciki ya buɗe kayanshi yasa frame ɗin ya fesawa kayan turare ya juya yashiga toilet". Mommy tana tsaye tana kallon ikon Allah, nan ta tuna wata rana datazo takamashi yana kallon hoto, yana ganinta yayi sauri ya ɓoye hoton abayanshi, Mommy tagaza ganewa Habeeb wani irin mutum ne? Idan tace ya kawo matar daze Aura sai yace mata "A GIDANMU TAKE" tarasa gane me kalman yake nufi. Amma koba komai yau saitaga hoton dayake ɓoyewa ko ta halin ƙaƙa! Tajuya tayi tafiyarta takoma falo. Habeeb yana shiga toilet ya wanke fuskarshi yayi alwala yazo yayi sallah, yana idarwa yatafi falon mommy yana zuwa yatarar da ita da 'yan biyunta suna hira, yafara murmushi yace kaga Mommy da 'yan biyunta, mommy tace eh wallahi Habeeb Amma meya sameka naga kamar kayi kuka? Habeeb yace wallahi mommy yau bacci nayi tayi, Mommy tace ok. "Da safe Mommy takira Habeeb awaya tace yazo falo zata aikeshi, Habeeb yana zuwa Mommy tace GRA zakaje ka karɓomin saƙo yace tom Mommy, Habeeb yana fita agidan Mommy taje ɗakinshi ta buɗe kayanshi daidai inda taga jiya ya ajiye hoton, Tana ganin hoton ta ɗauka ta tafi ɗakinta dashi, tana zuwa ɗaki ta buɗe frame ɗin. Ta ɗauko hoton tana gani. Amma me? Tana kallon hoton jikinta yafara rawa hanunta yakasa rike hoton kawai sai hoton yafaɗi. itama tabi bayan hoton a sume... *Share, vote and comment🙏🏻* ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:49 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to My love_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *Wattpad* _jiddah S mapi_ Page 39&40 "Mommy takai minti talatin Asume, kafin Beebah tashigo falon tana sallama taga Mommy Akwance ƙasa ba Alamun numfashi, Ta tsala ihu tana kiran Bintu, dagudu Bintu tashigo ɗakin ganin Mommy asume tayi gudu taje frij ta ɗauko ruwa suka shafa mata afuska" A hankali tasauke Ajiyar zuciya, tafara buɗe idanunta. Ganin Beebah da Bintu tsaye akanta cirko cirko, tafara Addu'an Allah yasa basuga hotonba. Tajuya tana dube duben inda hoton yake Amma bata ganiba, ta rikice tana neman hoton can taga hoton Agaban Bintu daidai ƙafarta, Bintu kuma bata lura da hoton ba burinsu suji me ya sumar da mom? Mommy dataga Alaman basuga hoton ba tayi sauri ta kwanta rub da ciki akan hoton tana cewa wayyo cikina! Tafara ja da cikinta har ta iso wajen gado tatura hoton babu wanda yagani. Bintu da Beebah suka rinƙayi mata sannu harta samu tayi bacci, Beebah ce takira Habeeb tace mishi "yaya mommy ba lafiya harta suma" Habeeb yace meya sameta? Tace babu komai muma dai haka muka shigo muka ganta a sume, yace "ok" ina izuwa. Habeeb yana zuwa yaga mommy akwance tana bacci yafara tambayan Bintu meya sameta? Bintu cikin sanyin murya tace nima dai haka nazo naganta a sume! Amma naji tana cewa cikinta ne yake ciwo! Yayi shiru yana kallonta yace "ok". Habeeb yazauna awajen mommy harta tashi daga bacci, tana tashi tacewa "yaushe kadawo?" Yace mommy ay tin Ɗazu nadawo tace ok cikin sanyin murya tace inason kaje kasiyaminmagani yanzu yanzu basai kawani canza kaya ba! Yace tom mommy, yatashi yafita mommy ta tsunkuya taɗau hoton a ƙarƙashin gado Kana tasa a frame ɗin ta ɓoye a rigarta tabi bayanshi. Tana fita taganshi yana ƙoƙarin buɗe ɗakinshi, da sauri ta ƙarasa wajenshi tace kai Habeeb mezakayi kuma a ɗaki bayan kasan banida lafiya harda suma? Amaimakon kayi sauri kasiyomin magani? Habeeb yayi mamakin yanda mommy takeson korashi amma be kawo komai aranshi ba!. Yace mata mommy kuɗi zan ɗauka sabida kuɗin hanuna yakare, Mommy tace kaje ɗakina kacire acikin jaka, yace tom Mommy. Saida Habeeb yabar gidan kafin Mommy tashiga ɗakin ta ajiye hoton yanda tagani ta gyara wajen kamar ba'a taɓa komai ba. Harda fesa turare. *_Ahmad_* Tin bayan tafiyan Habeeb yashiga damuwa kamar da dama acikin abokananshi daga Habeeb sai Abdul ne kaɗai suke kwantar mishi da hankali saɓanin Bash dayake bashi giya yasha kuma yakawo mishi mata. *_Bintu_* Bintu kuwa da Abdul soyayya tayi nisa idan Abdul beji muryan Bintu ba To ranan akwai tashin hankali. ****************** "Bayan wata ɗaya da sati uku, wanda yayi daidai da kawo kayan lefen Bintu Daza'ayi ayau juma'a, gidansu Bintu
Table of Contents