Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 15

Chapter 15

A Gidanmu Take Book 1 Complete Hausa Novel – Ahmad’s Regret and Fateemah’s Mystery 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fara sanarwa ashirya jirgi zai tashi, Daidai lokacin Ahmad ya tuna cewar ya manta wayarshi agida. Kuma bai kashe ba! Yacewa Mommy "mom inason in koma gida na manta wayana" Mommy tace haba Ahmad baka ganin jirgi zai tashi yanzu ne? Yace mommy matsalar ay wayar ba'a kashe ba! Za'ayi ta kirana aji switch off, Mommy tace kodai karya kayimin ne Ahmad? Yace haba mommy taya za'ayi nayi miki karya, Mutafi ma kawai, Haka suka shiga jirgi sukayi tafiyarsu. _Adamawa_ Sauri suke suga sun bar gari yola, daidai zasu fita a fire away from yola, Habeeb yacewa mommy, "Mom munyi babban mantuwa" Mommy tace me muka manta? Yace mommy mun manta da Abdul, baizo yabamu takaddan sakin Bintu ba! Mommy kar mubar garinnan da Aure akanta, Mommy tace hakane fa kuma, yanzu kiramin shi awaya ka tambayeshi ina yake, Habeeb yaciro waya yakira Abdul, Yacewa Abdul ina kake? Abdul yace ina Airport, Habeeb yace me kakeyi a Airport? Ina jiransu Ahmad ne yau zasuzo, ok gashima sun karaso. Ok idan kaɗaukesu kasamemu a fire away mana akwai wata muhimmiyar magana dazamuyi, Abdul yace to bari sai nazo. Ba'a daɗe dayin wayar Abdul da Habeeb ba, saiga su Ahmad sun karaso, Abdul ne yaɗaukesu amotershi, yace musu suyi hakuri zasu biya ta Fire away kafin su dawo Su Ahmad sukace ba komai, Ahmad ne yacewa Abdul idan mun dawo gidansu Bintu zaka kaimu, Abdul yayi mamaki sosai, ganin Ahmad dasu mom nashi sunzo wai yakaisu gidansu Bintu, Gashi abunda yafaru jiya. Sai kawai ya kawar da zancen. _Bintu_ Ita tarasa waɗannan wasu mutane ne? Tin jiya a asibiti sukeyi mata magana, Ita bata sansu ba! Hasali ma tanason ta tambayesu meya kawota nan? Wannan wani gari ne? Amma takasa Tambaya, Dataga sun shiga mota zasu tafi wani gari, azuciyarta tace Alhmdllh zasu kaini garina, may be ma satoni sukayi, Da Wannan tinani taji karan tsaiwar mota. Tana juya baya taga wani mutum yafito daga wajen zaman driver, Daga baya taga an buɗewa wata Mezata gani? Sai taga mommy tafito a motar, daga baya saiga Fareedah. Bubbuga motar datake ciki tafara Alamun tanason tafita. _Not Edited_ _✅ote & comment pls_ ✍️🗒️ *Jiddah S Mapi* [6/23, 12:52 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to my fans_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *WATTPAD* _Jiddah S Mapi_ Page 53&54 "Habeeb ne yaga alamunta, dasauri yabuɗe mata marfin motar tafita. Sai gani sukai Bintu ta tashi dagudu taje tarungume wata kyakkyawar mata da 'yarta, Bintu kuma acikin zuciyarta daɗi takeji tunda gasu mommy da Fareedah, tana ganin mommy tana hawaye tafara tambayanta mommy meya faru kike kuka? Ko Daddy ne ba lafiya? Alamun mamaki ne yabayyana afuskar su Mommy da Fareedah, Har Ahmad ba'a barshi abaya ba! Wajen mamakin tambayoyin da Bintu take. Basu tashi jin mamaki ba, saida Bintu tace "Mommy waɗancan mutanen satoni sukayi ko? Allah yataimakeni dannaji yana waya da wani wai a filin jirgi, dabaku zo dawuri ba, dasunana gawa!!! " Wannan maganar ya girgiza mommy [6/23, 12:52 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to my Eeshart much love habibty❤️_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *WATTPAD* Jiddah S Mapi Page 55&56 "Bintu kuka tafara kamar ba gobe, ita gaskiya batason Ahmad bata kaunarshi, idan ta tuna zagin dayai tamata lokacin datake gidansu sai taji ta tsaneshi, Hasalima tsoron shi takeji, wanda yayi niyan kasheka Amma kayadda kaci gaba da zama dashi? Wata zuciyar tace mata karkiyi haka, ta sanadin ki babansu yarasu idan kikace bakya sonshi ai kinyi butulci. Kiduba irin son da kanwarshi take miki" Mommy tace ke muke sauraro, Duk ɗakin sunyi shiru bakajin komai sai kukan Bintu, Ta ɓangaren Ahmad kuma ji yake kamar yaje ya rungumeta! Ya tsani yaga tana hawaye zafi yakeji acikin ranshi. Bintu tace "bazan iyaba!!!" wlh Mommy bazan iyaba!!!! Ahmad ne yafara ɗaga hanunshi sama alaman zaiyi roko, Mommy ta dakatar dashi. Mommynsu Habeeb ne tace "menene bazaki iyaba Bintu?" Bintu tace "bazan iya musu daku ba!" Alhamdulillah inji duk mutanen ɗakin, Ahmad ne yace mommy inada magana, Mommy tace muna jinka. Yace mommy inason kuzama shaida Kamfanina na takalma da jakunkuna nabarwa Fateemah halak malak yazama nata! Sannan akwai gidajena dake G.R.A a Kd guda biyu wanda nayi niyan zamu zauna da Fateemah aciki, sannan idan Fareedah tayi Aure zasu zauna da mijinta a ɗayan Yanzu ma haka Za'ayi, shikuma Abdul zan siya mishi gida agefen namu duk muzauna tare! Mommy tayi murna sosai sannan Habeeb da Abdul sunyi godiya sosai Su Ahmad kuma sunce gobe zasu koma, yayinda akasa ranan Aurensu Abdul da Beebah, Habeeb da Fareedah, sannan Ahmad da Bintu sati mai zuwa idan Allah yakaimu ****** yau akeyin ta! yaune ranan ɗaurin Auran su Abdul da Beebah, Habeeb da Fareedah! Amare sunyi kyau sabida sunyi dilki Idan kagansu kamar daga kasashen larabawa! Musamman Bintu data zama kamar 'yar india. Yau za'ayi lunching Amare dukka uku sunsa Dogayen riguna pink color me yalki da bakin roses suka ɗaura kansu, Me yi musu makeup na musamman aka ɗauko inda ta fesa musu kwalliya kamar ba gobe! Idan kaga waɗannnan Amaren zakace babu Amaren dasuka kaisu kyau. "Babban hall aka kama musu, inda akayi decoration na wajen da kayan ƙyaleƙyale na zamani, Kujeru uku me zaman mutum bibbiyu akayiwa kwalliya irinna gidan sarauta! _Ahmad, Habeeb da Abdul_ Suma ba'a barsu abaya ba wajen kyau, Sunsa Fararen shadda me ɗauke da zibin baƙi ajiki, Takalmi baƙi sukasa, sai agogo ma baƙi da bakaken hula. Subhanallah!!! Idan kaje kaga yanda aka tsara wajen da ƙawayen Amare da Abokanan ango da Amaren da angwayen, Sai ka raina kanka! Abinci kuma kamar ba dafawa akai ba! Drinks kuma babu kalan wanda babu, Amare sun zauna akan kujerun da aka kayata dominsu, Da angwayensu. Kuyi imagine yanda Amaren da angwayennan zasu bada light Awajen. An jera kawaye kamar cinnaka sunyi layi dukkansu da anko, dogayen rigane marun color sukayi anko sun ɗaura kai da peach na roses. Sumafa ba'a barsu abaya ba! Wajen kyau. Beebah ce taga ba'a kira Amare ba har yanzu gashi kawaye sai caskalewa suke afili, Sai kawai tamike Abdul yasan hali,, yasan mezatayi Yarike hanunta ta janye hanunta tafara tafiya tan rawa. Daidai lokacin aka sake wakan "Ahmad shanawa" Me taken agirgiza baya baya a karkaɗa ayi kamas Beebah ce tafara girgiza jikinta tana rawa kamar ba Amarya ba! Kowa ya juya yana kallonta rawa take tana juya jiki kamar hawainiya. Da Abdul yaga yanda take girgiza jikinta sai ya tashi shima yabi bayanta, Suka fara rawa atare dama Abdul ma ba daganan ba! MC. Yakira Amaren dukkansu da angwayen suka shiga fili. Ahmad yarike hannun Bintu. Sune agaba! Suna shiga tsakiya Bintu ta wapce hanunta tafita! Ahmad yatsaya yana kallon ikon Allah. Bintu kuwa acikin Zuciyarta idan ta tuna abinda Ahmad yayi mata sai taji ta tsaneshi, Batason Ahmad!!! Ta tsaneshi Amma bazata iya musu da mutanen dasuka taimaketa ba! Da yanzu tana gidan marayu, batasan ya

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});