Chapter 3
Chapter 3
Aa mariya ɗa na kowa Ne! Ganin yahau matsifane mariya tayi shiru "To dahakane har Allah yakawo ranar haihuwanta inda aka sha shagali akayi murna" Akasawa yaro sunan baban alhaji kabeer wato AHMAD. Ahmad de yasamu gata dan kota ina anaji dashi "Ahmad kyakkyawa ne" Fari Ne shi, dogo, da dogon hanci, ga karamin baki, Atakaicede shi yayi kama da larabawa. Sede kuma matsalar shi nada yawa Yanada girman kai sosai Ga kallon banza "Ga zama da abokan banza" Wasu abubuwan dayake yi abokai ne suke zigashi "Sai yayi ta tsula rashin kunya son ranshi" Dafarko yasamu daurin gindi awajen iyayenshi Se daga baya abun yafara damunsu *bayan wasu shekaru* "Dahakane har allah yasake basu haihuwa" "Yarinya taci sunan wacce take kula da gidan marayu na mahaifinsu wato FAREEDAH" Fareeda de kykkyawa ce tana Kama da Ahmad sosai. "Sannan kuma tinda aka haifi fareeda Ahmad yakara bude sabon rashin kunya" Shi adole yana da kanwa Bayan haihuwar fareeda fareeda ne Alhaji kabeer yafara diban yaranshi suna zuwa gidan marayu kai tallafi. Acewarshi idan sun girma suma zasu taimaki marayu. "Ranar farko dasukaje gidan marayun" Ahmad yasa fararen kaya masu kyau yanata Hada rai danshi beso zuwa ba. "Bayan an tara yara ana raba musu kudi ne" Alhaji kabeer yahango wata kyakkyawar yarinya. "Tana zaune a gefe tana kallonsu tana murmushi" Alhaji Kabeer yaɗan tsaya da rabiyar yana kallonta. Se ya yafito ta da hannu yace zo! Yarinyan ta tashi a hankali tana tafiya Harta iso su, seta durkusa tace gani. "Alhaji Kabeer yayi mamakin wannan yarinya batafi shekara goma ba" Amma take da natsuwa haka gata dakyau. Shi kuma Ahmad se harara yake tayi wai ana bata mishi lokaci Alhaji yace "ya sunanki?" Ahankali tace "sunana Fateemah" ✍️🗒️ *JIDDAH S MAPI* [6/23, 12:45 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by Jiddah S mapi _dedicated to walidation S mapi_ Wattpad Jiddahpretty Page 11&12 Wow nice name inji Fareedah, Gsky Daddy yarinyannan kyakkyawa ce, gata fara ga ido wow. Daddy yace meyasa ana raba kudi amma baki zo kin karɓa ba? Tace "banada bukatar kudinne shiyasa, duk abunda nake so mama tana bani. "To ay zaki iya ajiye kudin sabida watarana cewar Fareedah" Shi kuma Ahmad se duba agogo yake yanata tsaki, ba abun yacewa Daddy ze tafi ba, se harara yake ta bankawa yarinyan. Gani yake kamar ita take kara delaying nasu. Daddy ya ciro kudi masu yawa ya bawa yarinyan, ta girgiza kai tace "aa nagode abawa sauran" Kikarɓa ni na baki ay, a hankali tasa hanu ta karba tace"nagode Allah yasaka da alheri" Ameen ************* Tin daga wannan rana idan daddy yaje gidan marayu sai yace a kira mishi Fateemah yadau kudi yabata. To fa dahaka suka saba da Fareedah sosai watarana ma Fareedah takan zuwa gidab Marayun suyi ta hira da Fateemah, har yazama idan Fareedah bataje taga Fateemah! ba batajin dadi a ranta, sunyi muguwar shakuwa da Fateemah.. Ta ɓangaren Ahmad kuma yana dada lalacewa sabida abokai dayake tare dasu, mutane suna yawan kawowa Alh Kabeer karan Ahmad amma baya taɓa yadda se yace suyi hakuri yaranta ne daya girma ze daina. Abun yana taɓa zuciyar Mariya taya za'ace yarinta bacin yaro yakai shekara 29 ina maganan yarinta anan? yauma kamar kullum Alh Kabeer ne da yaranshi zasuje gidan marayu, yayinda Fareedah take ta rokon mom tashirya suje taga kawarta kuma Bestyn ta. To Fareedah naji tashi muje yawwa Mom ko kefah A hanyarsu tazuwa gidan marayu ne Alh kabeer yake tambayan Ahmad "Wai kai son yaushe ne zakayi Aure? Ahmad yahada fuska yana hararan Fareedah wai ana tambayanshi Aure a idon yarinya karama. Ba tambayanka nake ba?. Am daddy insha Allah very soon zan kawo muku matar dazan Aura. Mommy tace "udan ma be kawo ba mu sai mu nema mishi"Fareedah tace "yess mommy nizan nema mishi ma dakaina. Daya juya ya banka mata harara tayi tsitt Bayan sun shiga gidan marayu ne Fareedah tafara neman Fateemah a inda tasaba ganinta amma bata ganta ba! Ta tambayi wasu yara su biyu suna wasa tace"ina Fateema? " Sukace Fateemah batada lafiya tanata kuka tin ɗazu taki amata allura. A wana ɗaki take? cewar Fareedah cikin tashin hankali tayi tambayar? muje nakaiki cewar wata yarinya Suna shiga dakin taga Fateemah tana ta kuka tana rawan sanyi Da gudu tafita tana kiran mommy! Mommy naganin Fareedah ta fito da gudu, tafara tambaya lafiya? Fareedah batayi magana ba se nuna daki take! Mommy tace kiyi magana, dakyar tace Fateemah, wace Fateeman? Cewar Daddy..... Nan suka shiga dakin da gudu. Suna zuwa sukaga Fateemah bata motsi nan Fareedah ta tsala ihu Mommy tace kira yayanki awaje Fareedah ta taso da gudu tana kiran yaya yaya Ya dago kanshi yace ke me haka? Kinata kiran sunana kamar wani sa'anki "Yaya wai kaje inji mommy" Yaja wata doguwar tsaki yace muje Suna zuwa Daddy yace oya Ahmad dauke ta dawuri mutafi asibiti😳 Haba Daddy kaduba fa farin kayane ajikina ta yaya zan fara daukanta? Dubi jikinta fa duk datti....... Zaka dauketa ne ko sai ranka ya ɓaci cewar daddy. A hankali yaɗauketa yana yatsina fuska Yariketa kamar kashi ya ɗauka sai yayi sauri sauri ya wurgata a motar da iya karfinshi. Har saida kanta ya bugu Daddy yace shiga mutafi, dakyar yadaure yashiga yanata kunkuni. Ita kuma Fareedah sai kuka take tana kiran sunan Fateema tana cewa ta tashi karta mutu A haka har suka iso specialist hospital. Suna zuwa ba ɓata lokaci aka karbesu Likitoci suka shiga ciki da ita, Ahmad yace dama daddy inason naje wani waje na karɓi sako, babu inda zaka kana gani mun kawo yarinya ba lafiya rai a hanun Allah kace zaka tafi, baka da imani ne? Ahmad ya haɗa rai yasamu waje ya zauna yanata kunkuni me haɗi na da ita da za'a hanani yin uzirina akanta? Yarinya kucaka ma da ita Suna cikin zama wata nurse ta fito tace doctor yana magana dakai. Alh kabeer yace to, nan yashiga ciki, doctor yace kaine baban yarinyan daka kawo? Alhkabeer yace eh nine Ok amma kasan da ciwon dayake daminta? Yace Aa Doctor yagyara zama yace Alh rayuwar 'yarka tana cikin matsala "Ka taɓa zama da ita ka tambayi matsalarta? Daddy yace Aa Tofa akwai babbar matsala! Am sorry to say, 'yarka tana dauke da ciwon zuciya wanda idan har aka barta cikin tunani tayi nisa zata iya rasa ranta a ko wani lokaci. ✍️🗒️ *JIDDAH S MAPI* [6/23, 12:45 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story written by_ Jiddah S mapi _dedicated to my lovly sister @walidation_ _✅ote me on_ _wattpad Jiddahpretty_ Page 15&16 Da kyar Fareedah ta janye Fateemah zuwa gefen hanya ta kwantar da ita tace "ki zauna anan bara naje na kama mana Napep" A haka ta kama musu Napep ta rike Fateemah suka shiga se gida. Shi kuma Ahmad yana jan motarsa ya wuce carwash yace a wanke mishi ita, Alh Kabeer kuwa da mariya suna zuwa gidan marayu yacewa mama yanason magana da ita, Tace "ok ba komai ina jinka Alh" Yace dama so nake na ɗauke Fateemah na ɗan wani lokaci idan ba matsala, Mama tace ba komai Alh. Ay duk an zama ɗaya, Da haka suka tafi gida. *************** Shakuwa me tsanani ta shiga
Table of Contents