Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

A Gidanmu Take Book 1 Complete Hausa Novel – Ahmad’s Regret and Fateemah’s Mystery 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

har yanzu, Tashi ya tashi Tace muje, Yashiga gaba suka fita! Suna fita yaga Fareedah a kwance lub abakin kofa kamar ba Rai, Da gudu Mommy taje wajenta tana kiran sunanta amma shiru, mommy ta kwala ihu tana kiran sunanta, shi kuma Ahmad ya rikece yarasa me zeyi. "Suna cikin haka Daddy ya sauko da sauri yana tambayan meyake faruwa? Mommy tace mishi Fareedah ce ta suma! Yace wa Ahmad kawo ruwa. Ahmad yatashi da gudu ya ɗebo ruwa aka Zuba mata a hankali tafara buɗe idonta tace ina Fateemah? Da alama taji duk maganganunsu, Ahmad yayi shiru Daddy yace wace Fateemah? Mommy tace Fateemah ce Ahmad yaje ya yadda ita!" Daddy yace what are you saying Mariya? Mom tace katambiyeshi kaji mana wai ta kulleshi a ɗaki shine yarama, Daddy ya ɗago idonshi yana kallon Ahmad Yace me nakeji, Yayi shiru, Daddy yace tashi muje suka ɗunguma duka suka shiga mota. Ahmad yajasu suka tafi sunata tafiya sukaga wajen yayi nisa mommy tana ta Addu'a a ranta, Har suka iso bayan gari kafin yatsaya, Daddy yace ananne? Ahmad yace eh ok ina take yayi shiru, Mommy kuwa tazuba ma wani dutse ido Taga kamar jini ne akai, tacewa Alhj kalli can, Daddy yana kallo yaga jini ne awajen! Suna zuwa sukaga jini dayawa akan dutsen harya fara bushewa, Daddy yace Wannan jininfa? Ahmad yayi shiru Daddy have ba tambayanka Nake ba? Daddy Nina ban Sani ba! Tass Daddy ya wankeshi da Mari. Ina kakai 'yar mutane? Inji Mommy yayi shiru... Ba tambayanka ake ba? "Shikamma yarasa ya zeyi idan yayi magana su mareshi yayi shiru suyi ta tambayanshi ya rasa ya zaiyi" "Suna cikin dubawa sukaga wani mutum yana zaune dagacan gefe, Daddy yaƙarasa wajen mutumin yace mishi, bawan Allah bakaga wata yarinya Acan Akwance ba? Tsohon yacewa Daddy, eh ai ɗazu wasu mutane sunzo sun ɗauki wani gawa acan kuma a yadda nagani gawan kamar mace ne........." Ai kafin yaƙarasa Daddy yafaɗi awajen, da gudu suka ƙaraso wajen suna tambayan tsohon meya faru? Yayi musu bayanin komai, kafin yakarasa zancanshi ai Fareedah ma tayi ƙasa, mutumin yarasa meyake faruwa. Mommy tadinga zabga ihu shikuma Ahmad atake jikinshi yafara rawa da ƙyar suka ɗaukesu zuwa Asibiti ************** Tun daga wannan rana Alh Kabeer yazama bashi da lafiya harya kasance jikin yayi tsanani hawan jini yake daminshi, Ɓangaren Fareedah ma bawani lafiyane da ita ba tazama shiru bata da yawan magana. Shikuma Ahmad yarasa meyake mishi daɗi Abu kamar wasa gashi yazama gaske, shima yazama shiru shiru dama gashi miskili. Alh Kabeer jiki yayi tsanani yana jinya sosai, yau kam jikinma yafi na kullum an kaishi Asibiti rai yayi halinshi saide muce Allah yagafarta mishi da duk musulman da suka mutu "Ameen" ✍️🗒️ *jiddah S Mapi* [6/23, 12:47 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _Story/written by_ Jiddah S MAPI _dedicated to my daughter Afrah_ _✅ote me on wattpad Jiddahpretty_ Page 21&22 "Tun daga Wannan ranan Hajiya Mariya tadaina yiwa Ahmad magana, Fareedah ma ba magana take mishi ba ko yayi musu magana ɗauke kai kawai suke Abun duniya yayi mishi yawa ya rasa ina zesa kanshi shi fa a Azuciyarshi yanaji bata mutu ba! Haka yazama kamar wani mahaukaci duk inda yaji ance Fateemah saiya juya yaga meshi, abokansa sun kasa gane kanshi baya zuwa club yadaina bin mata ko ankirashi awaya baya ɗauka sai shaye shaye yake kamar mahaukaci" Akwai wata rana daya kira Fareedah yace tazo tasaya mishi magani Fareedah batayi magana ba sai yaga kamar ta rainashi ne haka yarike Fareedah yayi ta dukan ta. Mommy tana dawowa taga Fareedah jiki a fashe tace meya sameki? Fareedah tace Ahmad ne ya daketa! Mommy tafita a ɗakin taje ta sameshi a kwance kan gado, mommy tace Ahmad bazaka kashe 'yar mutane ka kashe mahaifinka sannan kazo ka kashe Ƙanwarka ba, baka isa ba kayi kaɗan Katashi kabar gidannan cikin minti goma idan kasake dawowa saina tsine maka Albarka!!!Ahmad yabuɗe baki zaiyi magana amma Mommy tace idan ya kuskura yayi magana Allah ya isanta haka ya tattara kayanshi yabar gidan. Ahmad ya rame bashi da tinani saina Fateemah a halin yanzu yafara tuninin yana son Fateemah ne idan ya tuna da hakurinta da juriya, Sai yayi ta kuka kamar me, haka Habeeb yazo ya tarar dashi haka, Yace meya sameka Ahmad yayi mishi bayanin duk abinda yafaru. ********** *cigaban labari* "Yaune ranar zagayowar haihuwan Bintu da Beebah an haɗa party wanda kawayensu na makaranta dayawa suka hallara, inda Bintu da Beebah suka sa anko na skirt pink da top black suka ɗaura kai da black na ɗankwali, Faɗin yanda sukayi kyau ɓata lokaci ne domin yau 'yan biyun Mommy sunyi mugun kyau kamar asace a gudu, kawayensu kuma sunsa dogon riga baki sunyi kyau suma sosai an yanka cake ansa waƙa a speaker Inda Beebah tayi ta dansewa ita da ƙawayensu Bintu sai video kawai take yi musu tana dariya." Habeeb kuwa ya kira Beebah yace mata sweet sis ki hau watsapp kituramin hotonan da kukayi yau zansa a status ɗina tom broh bari na buɗe Data.... ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:47 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written By *jiddah S MAPI* _dedicated to my daughter AFRAH_ _follow ne on wattpad Jiddahpretty_ Page 23&24 "Beebah ta buɗe data ta turawa Habeeb hotonan su da videos ɗin dasukayi, habeeb yana ganin videon yace mata wow sweet sis kunyi kyau gaskiya tace thank you broh, Se mangariba dab suka gama partynsu suka raka duk ƙawayensu kowacce tashiga motarta suka tafi, Bintu ce ta kwashe musu gift dasuka samu daga wajen ƙawayensu tashiga musu falon mommy dashi". Ahmad yau ya tashi da tsananin ciqon kai inda yayi ta birgima yana riƙe da kanshi, dakyar yasamu yasha magani yaɗan samu sauƙi, ya zauna a gefen gado yana tinani azuciyarshi yace "da ace my teemah tana nan data bani magani da kanta nasha, komai nayi mata zatayi hakuri dani wayyo my teemah ina kike dan Allah ki bayyana min kanki nasan kina raye baki mutu ba! Ki fito dan Allah naganki zan nuna miki soyayyar dabaki taɓa jin labarinshi ba ko a Novel. Haka ya karashe tunanin shi ya tashi ya shiga wanka, bayan yafito daga wankane yashafa mayukanshi masu kamshi ya taje gashin kanshi me laushi kamar na indiyawa, ya buɗe wardrobe nashi yaɗauko wani riga pink colour da bakin wando ya ɗauko picap baki yasa ya dubi kanshi a madubi yaga ya rame sai de yayi fari sosai, a hankali ya rufe idonshi yace oh god help me out. "Habeeb bashi da damuwan daya wuce damuwar abokinshi Ahmad, kullum idan ya zauna sai yayi tagumi yana tinanin ta ina zai fara taimakawa Ahmad, har Mommy tagano yanayin shi da daddare suna zaune a falo suna kallo, Bintu tana ɗan danne danne awaya ita kuma Bebbah ta kwantar da kanta akan cinyar Habeeb tana mishi rigima wai sai yayi mata tsifa, Mommy tace Habeeb inason in tambayeka wani Abu mana? Yace to Mom ina jinki Mommy tace meya sameka ne naga tin ranan daka dawo daga Kaduna kashiga damuwa ko wani Abunne yasamu Ahmad? " Habeeb yace gaskiya mom Ahmad yana cikin matsala nan yafara faɗa mata duk abunda ya faru Amma ya ɓoye mata yanda Ahmad

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});