Chapter 13
Chapter 13
hakuri, kowa yawatse. _washe gari_ Ahmad ne da Habeeb suka buga wanka, sunsa anko gaba ɗayansu shadda ne fari da zubin baƙi, sukasa hula baƙi da takalmi baƙi sai agogo baƙi, bakaramin kyau sukayi ba, suka shiga motar Ahmad baƙi, suka ɗau hanya sai gidansu Bintu. Suna zuwa Abdul ne yashiga daga ciki dan Ahmad yace shi baze shiga ba! Yana jiransu awaje, Abdul yana shiga ya gaida mommy afalo, mommy take bashi hakuri tace kayi hakuri Abdul wata 'yar matsala aka samu, shiyasa kaga ba'a kai maka Bintu ba! Abdul yace ba komai, mommy ce ta tashi afalon taje takira Bintu aɗakinsu, Bintu ce ta tashi tasa dogon riga, gaba ɗaya ta rame tin jiya take cikin kuka da tinani tarasa meyake mata daɗi. Goga powder tayiwa fuskarta tasa baƙin kwalli acikin Idonta tayafa baƙin gyale, ta fesa turare ajikinta masu kamshi, tasa flat shoe, duk abinda takeyi Beebah na kallonta tace ko zamuje ku gaisa ne? Beebah tace no, tace dan Allah muje, Beebah data tuna dukan rannan saita diro akan gadon tace bari nasa hijab sai naje mu gaisa. "Suna zuwa falon Beebah tafara tsayawa abaya baya dan tasan rashin kunyan datai tamishi jiya, shi kuma saiya basar yace ya kike kanwar Habeeb? Beebah tace lafiya ya gajiya? Yace babu, Abdul ne yayi gyaran murya yace amm Hassana da Hussaina? Sukace na'am yace wata alfarma nazo nema awajenku, duk da Bintu yanzu ita matatace amma dole na nemi alfarma, Sukace ba matsala kafaɗa muji in Zamu iya, Yace dama inason ku ɗibo kaya waɗanda kukayi anko, da wanda mukayi pre-wedding pics dashi, yanzu zamuje ayi sabon hoton sabida wancan akwai matsala" "Bintu ce tace ita bazatayi hoto ba! Abdul yadinga haɗata da Allah taki, da Abdul yafusata yace look Bintu karkiga dan inasonki kice zaki wulaƙanta ni, yanzu miji nake awajenki umarni nake baki kitashi ki ɗebo kayanki zamuje ayi sabon hoto! Yafaɗa cikin fushi. Bintu ce tahaɗa rai ta tashi tashiga ɗaki ta ɗebo kayan dana Beebah, Beebah ce takarɓi kayan ta tafi sawa a mota, ita kuma Bintu tashiga cikin ɗakin mommy domin sanar da ita. _Ahmad_ Shikuma ya zauna yanata jiransu amma har yanzu basu fito ba! Ganin haka yasa yajuya kanshi yadaina kallon kofar gidansu Bintun, dayaji karar buɗe kofar saiya juya yaga Beebah ce takesa kayansu aciki, tace ina wuni? Yace lafiya, daga cewa lafiya be kara komai akaiba kuma be sake juya bayanshi ba, yayi readyn jan mota idan sun fito. Beebah ce tashiga cikin motar tazauna tana kallon side view na Ahmad. Abdul da Bintu Kuwa sunata rigiman fitowa. Bintu tace sai Abdul ne zai fara fitowa shikuma Abdul yana tsoron kada yashiga gaba ta gudu, shima yace sai ita zata fara fita. Da kyar Bintu tayadda tafara fitowa rai aɓace taje ta buɗe motar tashiga wajen da Beebah take. Shikuma Ahmad ko juyawa ya kallesu baiyi ba, yana ganin Abdul yashiga, ko gama rufe marfin motan baiyi ba! Yaja motar cikin fishi yafara watsa gudu akan titi.... _✅ote, comment and share pls🙏🏻_ ✍️🗒 *Jiddah S Mapi* [6/23, 12:51 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to my Facebook fans_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *Wattpad* _Jiddah S Mapi_ Page 47&48 "Ahmad gudu yake akan titi kamar zai tashi sama, Abdul ne yayi mishi magana yace, haba Dude wannan wani irin gudu kakeyi? Baka tsoron muyi hatsari? Ko kuma mu bugu da bishiya? Shiru Ahmad yayi mishi, ganin haka yasa Abdul yaja bakinshi yayi shiru, sabida yasan halin abokinnashi" Bintu kuwa acikin zuciyarta haushin wanda yake tuka motar takeji, mutuminnan wani irin mugu ne? Yana gani muna cikin motar amma yake irin wannan gudun? Duk yanda akayi wannan baisan darajar mutum ba, mugu azzalimi, duk acikin zuciyarta take wannan maganar. Beebah kuwa duk gudun da akeyi batama saniba sabida hankalinta duk ta tattarashi akan Ahmad, gayen yamatuƙar tafiya da imaninta, Haka har sukayi parking awani waje me kyau, saman wajen an rubuta "Adamawa special photos" Ahmad yanayin parking ya buɗe motar yafita ko juya bayanshi baiyi ba, yana fita su Bintu ma suka fito, dukansu suka shiga cikin ɗakin da ake ɗaukan hoto, suna zuwa sukayiwa me hoton bayanin yanda akayi, yace musu ba matsala za'asan yanda za'ayi. Duk maganar dasukeyi Ahmad ya sunkuyar da kanshi baya kallon kowa, har suka shirya dukansu, Bintu da Beebah sunsa anko na riga da skirt atamfa suka ɗaura kansu, sunyi kyau bana wasa ba, Me hotone yafara ɗaukansu hoto, dukansu, idan An ɗauka ɗaya saisu janza kaya. An ɗauki Beebah da Ahmad tarike wuyanshi, sai kuma akace za'a ɗauki Bintu da Ahmad. Ahmad yana zaune akan kujera tunda aka fara ɗaukan hoton bai ɗaga kanshi yakallesu ba, saidai yakalli me ɗaukan hoton, Bintu ce zasu ɗau hoto da Ahmad sai me hoton yace saikin rike wuyanshi idan har kunaso kar mutane sugane, Bintu ce taɗan sunkuyo kaɗan tarike wuyan Ahmad, jikinsu ne yayi shocking atake! Bintu tasake shi da sauri tayi baya, shima Ahmad yaji wani shocking ajikinshi harya kusa faɗowa kasa. "Me hoton ne yace ku muke jirafa". Bintu ta iso wajen jiki amace tarike wuyan Ahmad aka ɗaukesu hoto, ana gama ɗauka suka tara kayansu aka tura musu hotunan awaya. A hanyansu ne nakomawa gida motarsu tasamu matsala, Ahmad ne yace duk su fito, Beebah uwar kauɗi itace tafara fitowa daga motar, sai Abdul yabi bayanta, sai Bintu ce karshe, Ahmad ne yace wata tabamu ɗankwalinta mana zamusa awani waje. Beebah ce tahaɗa face alamun koza'a kasheta bazata bada ba! Bintu ce tacire ɗan kwalin kanta ta mika mishi tace gashi. Ahmad Azuciyarshi yace ashe tanada hakuri bara kawai mu gaisa da ita, ɗago kanshi yayi dan su gaisa saiyaga ta sunkuyar da kanta tana gyara gyellen ta, sai kawai yaɗauke kai, ita kuma tana Gama gyaran gyalle tajuya zata kalleshi taga ya ɗauke, saita basar, Ahmad kuma tin ɗazu addu'a yake acikin zuciyarshi domin tin jiya yakejin tsinkewar zuciya. Bintu ce ta ɗago kanta tanason yiwa Beebah magana daidai lokacin Ahmad ma yaɗago kanshi. Suna haɗa ido, Bintu tafara jujjuya ido alamun akwai matsala, Ahmad ne yafara ja da baya yana nuna Bintu, ita kuma Bintu ta tsala ihu tace "ku taimakeni zai kashe ni" Abdul ne yariketa da karfi yana tambayanta meya faru? Ta juya da karfi tafara gudu akan titi tana ihun ataimaketa, Abdul da Beebah ma suka rufa mata baya suna binta da gudu, Ahmad kuma ya bushe awajen sai nuna waje ɗaya yake da yatsa! Gudu take Akan titi bata lura da yanda motoci suke wucewa. Abdul da Beebah sai binta suke suna kiran sunanta Bintu!!! Bintu!!! Bintuu!!! daidai wani dutse bintu tafaɗi kasa sabida ta gaji, tana faɗuwa kanta ya bugu da dutse atake kan yafara jini, Daidai lokacin Abdul da Beebah suka iso wajen, suna zuwa Abdul ya ɗauketa yatare Napep yace Asibitin specialist, suka shiga me Napep yakaisu. Suna zuwa aka karɓi Bintu akayi Emergency Room da ita. _Ahmad_ Shikuma Ahmad yakai minti talatin hanunshi asama yana nuna waje ɗaya, bakinshi kuma yana rawa kamar mejin sanyi, saida yaɗan fara dawowa natsuwarshi kafin ya buɗe mota
Table of Contents