Chapter 4
Chapter 4
tsakanin Fareedah da Fateemah, Dan Fareedah sosai takeson Fateemah har cikin Ranta komai za'a siya mata zatace sai an siyawa Fateemah. Shi kuma Ahmad a duniya babu abinda yatsani gani kamar Fateemah, kwata kwata Allah be haɗa jininsu da ita ba, Ko abinci Fateemah ta dafa baya ci idan har ya san ita tadafa. Yauma kamar kullum Fateemah ce take goge goge a falo, tana kan goge TV ne taji ance mata "ke baki da hankali ne ko kin taɓa ganin inda ake goge TV da tsumma? Koda shike ba laifinki bane laifin iyayenki ne dasuka haifeki a titi, daga baya suka yadda ki" Nasan da agaban iyayen ki kike, dakin iya goge TV. Wawiyar banza. Tunda Fateemah take a rayuwarta ba'a taɓa faɗa mata maganan daya ɓata mata rai irin ta yau ba, Ahmad ne farko yafara kiranta da shegiya. A hankali ta ɗago kanta tace "kayi hakuri zan gyara insha Allah " Ai kuwa yaja tsaki ya fita a ɗakin yanaji kamar ya shaketa ta mutu kawai. Wato yarinyannan duk abunda za'ayi mata bazatayi kuka ba, saide tayi tabada hakuri kamar marokiya, sai nayi maganinta ay. Ita kuma Fateemah yana fita tasa kuka me cin rai, Tana cikin kuka ne taji muryan Fareedah tana, Besty ina kike? Ta share hawayenta tace "gani nan" Fareedah ta rungumeta tace "meya sameki naga kamar kinyi kuka? tace "Aa babu komai kaina ke ciwo" Ayya sorry kinsha magani? Eh nasha, Ok muje ɗaki to ki kwanta. Da daren ranan Fateemah takasa bacci, data rufe ido sai tana tuna maganganun Ahmad na ɗazu. _ba laifinki bane_ _Laifin iyayenki ne_ _Dasuka haifeki a titi_ Wato ni shegiyace? A titi aka haifeni? To ina iyayena suke!? Meyasa suka yadda ni? Shine tambayoyin data kasa amsawa kanta, Data kara tunawa seta fashe da kuka, Jikinta yafara zafi, tana kokarin ta tsaida kukan amma ta kasa. Da haka har tafara tari, jikinta yafara rawa taja bargo ta lulluɓa jikinta amma har yanzu tana jin sanyi. Tana cikin wannan halinne Fareedah ta tashi zatayi fitsari, Taga Fateemah acikin bargo jikinta yana rawa gashi fuskanta yayi ja, A razane ta iso wajenta tana tambayanta meya faru Fateemah ba bakin magana se ido kawai, Ta fita da gudu taje ɗakin mommy ta kirata, A tare sukazo da mommy, Mommy tana ganin halin da Fateemah take ciki tace akira mata Alhaji, Ai kuwa Alh Kabeer yana zuwa yace aje akira Ahmad yazo su tafi Asibiti. Fareedah ce taje kiranshi tana zuwa tayi knocking yace "yes waye? " Tace Yaya Fareedah ce, Yace me kikeso? Tace "Daddy ne yace nakiraka" Daddy kuma? Meya faru? Nima ban sani ba! Ok ina zuwa, Ahmad yana zuwa Daddy yace "oya ɗauke ta da wuri mu tafi Asibiti kar dare yayi sosai. 😳Daddy wani Asibiti? Dama wani Asibiti muke zuwa? Inji Daddy Daddy Ai yanzu dare yayi abari sai gobe mana da safe.... Kai Ahmad baka da hankali ne? Ko baka ganin halin da take ciki? Ko da Fareedah ce zakace abari sai gobe? Yayi shiru dan besan me zecewa Daddy ba ganin yahau 90, A haka badan yaso ba ya ɗauketa yakaita mota, Ji yake kamar ya shaketa tamutu ko ze huta ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:45 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story/written by_ Jiddah S mapi _dedicated to my lovly sister_ @walidation Page 13&14 "Alh 'yarka tana cikin matsala" zai fi maka sauki ka kirata ka lallaɓata, ta faɗa maka meke damunta, sabida hakki ne a kanka. To fa nan Daddy yafara share zufa, yanason yace ba 'yarshi bace, amma yana tsoron kar likitan yace mishi makaryaci. "Yace toh doctor nagode" yanzu ya ake ciki? Doctor yace "a halin yanzu de an ɗaura mata ruwa, saura na rubuta muku magungunan da zaku saya" Ahmad kuwa abokanshi sunata kiranshi awaya, yana ta tsaki wannan wani irin abune? Bamu santa ba! Ba dangi ba! Ba 'yan uwa ba! Amma ahanani yin komai chewww.... Yasake jan wani dogon tsaki ganin ana sake kiranshi. "Dan Allah karka dame ni Bash, ka kyaleni na huta wannan wana irin Bala'i ne?" naji da matsalar Da Daddy yasani yau ne ko da naka? Ɗittt ya kashe wayar. Zo nan my son! "To" Yawwa dama zuwa zakayi ka siyo magunguna acikin asibitin, to Daddy ya karɓi papern yana tafiya yana tsaki. Fareedah kuwa takasa zama, da zarar taga likita yana wucewa sai tace doctor ya jikinnata? tin suna amsawa har sukayi shiru ***************** Da ahmad yakawo maganin suka ɗunguma gaba ɗaya suka shiga ɗakin, suna shiga suka tarar da Fateemah ta farfaɗo, Fareedah tayi gudu ta rungumeta. "Ita kuma Fateemah ta lumshe ido" Ahmad kuwa yau kamar ido ya faɗo tsabar harara *nace oho de* Ya jikin naki inji Daddy a hankali tace "da sauki" tom Allah yakara sauki tace "Ameen" Daddy Yace idan kika ɗan samu sauki bazaki je gidan marayu ba gida zamu wuce, tnx Daddy gaskiya nima nafison taje gidanmu zamufi kula da ita. A take Ahmad ya ɗago kanshi yana kallon Daddy, yace "Daddy wani gida zata wuce? " Wani gida kake ciki? Cewar Daddy, nan yai shiru yana kallonsu. ************* Washe gari bayan an sallamesu ne daddy yace "Ahmad ka kaisu gida ni zan wuce gidan marayu nafaɗawa mamansu nacan bazata koma ba sai ta samu sauki", to Daddy. Mommy tace "Alhj tunda ga Fareedah me ze hana su tafi tare mu kuma muje gidan marayun tare", ok ba matsala ay Ahmad kaisu gida, to Daddy Da kyar Fateemah take tafiya, sabida tanajin jiki. Fareedah ce ta riketa har suka shiga motan a hankali. Bayan sun ɗau hanya suna tafiya ne "Fateemah tafarajin Amai, A hankali tace inajin Amai! Fareedah tace yaya kayi hakuri ka tsaya tanajin Amai, yai shiru kamar bai jita ba, ta sake cewa "yaya Amai takeji", nanma shiru ba amsa sema kara gudu dayake. Nan Fateemah tafara sheka Amai kamar ba gobe, tofah nan yaja birki ya tsaya. Yace "fitah" sukayi shiru dan Fateemah ta galabaita, ya sake cewa "nace kufita" Fareedah tace "haba yaya baka ganin Amai take ne kabari mana tagama". Zaku fitane ko sai na Ɓata muku rai, ya daka musu tsawa!!. Fateemah tafara yunkurin tashi Amma ina ba dama, da kyar Fareedah ta riketa suka fita, suna fita a motar Fateemah ta faɗi dan bata da karfi ko kaɗan. Haka yana gani yaja motarsa yabar wajen _wattpad_ Jiddahpretty ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:46 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *jiddah S mapi* _Dedicated to my lovely sister walidation_ ✅ote me on wattpad *Jiddahpretty* Page 17&18 "Suna shiga cikin Asibiti Likitocin sukayi kansu da gudu suka karɓe ta sai Emergency Room", Daddy kuwa hankalinshi duk a tashe yanata zagaye Asibitin. Azuciyarshi yana tunanin to me ya tadawa Fateemah ciwon tane haka, Dahaka har likita yafito daga ɗakin yacewa Daddy yana buƙatar magana dashi, Daddy yace to. "Bayan yashiga ɗakinne likita yace mishi Alh idan har kanada daman dazaka Aurar da 'yarka to kayi mata Aure, kaga idan har agidan miji take bazata rinƙa yin wasu tinani barkatai dahar ciwonta zai tashi ba. Daddy yayi shiru yana tinani, se daga baya yace to nagode Doctor. Doctor yace "yau zamu sallameku sabida anyi mata Allura ansa mata drip idan ya kare zaku iya
Table of Contents