Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Chapter 12

A Gidanmu Take Book 1 Complete Hausa Novel – Ahmad’s Regret and Fateemah’s Mystery 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mutane sai tafi sukeyi musu. "Abdul kuma yatsaya afili kamar gunki yana kallon ikon Allah, yama rasa me zeyi? Sai juye juye yake yana dariyan dole" Beebah kuwa tazage afili kamar ibada sai juya jikinta take kamar hawainiya, Da Ahmad yaga yanda take rawa. Azuciyarshi yace wannan wace irin Amarya ce?... _✅ote, comment and share pls🙏🏻_ ✍️🗒️ *_Jiddah S Mapi_* [6/23, 12:50 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to all my fans_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *Wattpad* _Jiddah S mapi_ Page 43&44 "A zuciyar Ahmad yace ay Amarya ko bata da kunya, ranar Aurenta tana ɗan jin kunyar mutane Amma ita ta zage sai tiƙa rawa taje agaban Abokan Ango? Kai wannan abu da alamar tambay" Beebah kuwa acikin zuciyarta tance kai wannan gayen ya haɗu ana gama kamu zan tambayi numban wayarshi, duk nan yafisu wanka, duk maganar dasuke acikin zuciyarsu be hanasu taka rawa a filin ba, har MC yace to mun gode Allah yasakawa amarya da ango dakuma babban abokin ango. Haka suka juya suka tafi, an gama kamu dab mangariba kowa ya watse. Ahmad ne yacewa ango yanason yabishi hotel ɗin daya sauka sabida sunada magana me muhimmanci, Abdul yashiga motarshi suka wuce Hotel. _Bintu_ Bintu tace ita wallahi daga kamu ba abinda za'a karayi a Aurenta na bidi'a. Washe gari ranar jumma'a ranar da za'a ɗaura Auren Abdul Muhammad da Bintu Umar, shirye shirye ake na musamman, kawayen mommy sunzo daga wani gari 'yan wanka ne kuma hajiyoyi ne. Bintu kuwa tasa leshi jaa me kyau tayi makeup kamar asace agudu, Beebah ma ba'a barta ba wajen kyau, kawayensu ma sunyi kyau sosai. Kawayen mommy suma leshi suka ɗinka garin mata dashi, idan kashiga gidan saika raina kanka. 2:30pm cif aka ɗaura auren Bintu da Abdul akan sadaki dubu ɗari lagadan ba ajalan ba, Anyi Aure an kammala komai da mangariba abokan ango sukazo su ɗauki amaryarsu. Tofa nan akeyinta Habeeb dayaga za'a tafi da Bintu yadinga suma kamar me farfaɗiya, har mutanen wajen suka fara mamaki, mommy ce tacewa Bintu takoma gida, Beebah ce tazama amaryan karya taje tashiga mota aka tafi da ita, bayan mutane sun watse ne mommy takira Habeeb cikin ɗakinta da Bintu ta ajiyesu, mommy ce tace Habeeb? Yace na'am tasake cewa Habeeb? Habeeb yace na'am Mommy tasake cewa Habeeb? Yace na'am, Mommy tace sau nawa nakira sunanka? Yace sau uku, mommy tace tom nataɓa kiran sunanka sau uku? Yace Aa tace inason kafaɗamin gaskiya. Meye a tsakaninka da Bintu?.. Habeeb yayi shiru sai kawai yafara kuka, mommy tace ba kuka natambayeka kayi ba, idan har nina haifeka kafaɗamin Abinda yake ranka? Habeeb yace Mommy inasonta ne!!! Kuma Aurenta nakeso nayi!!! Tass tass tass kakeji Bintu ce taɗago ta dallawa Habeeb mari tana huci... Bakada hankali ne yaya? Ko kafara shaye shaye ne? Ko ka sami taɓin hankaline? Ko bakasan ciki ɗaya muka fito dakai bane? Duk waɗannan tambayoyin tana yinsu ne cikin hawaye.. Yaya kai mahaukaci ne bakada hankali, sai yau na tabbatar da haka kanka ya taɓu. Ke Bintu kece me taɓin hankali bani ba! Kece kanki yasami matsala bani ba! Ina matsayin yayanki zaki kirani mahaukaci? Kece mahaukaciya! Yana magana yana hawaye, Kinsan iron son danake miki? Kinsan baƙin cikin danake ji idan naganki da saurayi? Kinsan yaya nake kwana acikin kwanakinnan da Auranki ya iso? Kinsan yanda nakeji kamar na kashe Abdul idan naganku tare? Duk nasan baki sani ba. "Mommy ce ta tsaya awajen ba bakin Magana sai zazzare ido datakeyi kamar wata taɓaɓɓiya, idan wannan yana magana tajuya ta kalleshi idan wannan yanayi ta juya ta kalleshi tarasa ya zatayi da duniyarta tarasa ina zatasa kanta ayau, jitake kamar ta tara kayanta tabar gidan kafin su fara mata tambayoyi, juyawa tayi zata bar musu ɗakin taga mutum akwance kasa ba alamar numfashi! Beebah ce kwance kasa, wanda ta daɗe da dawowa ta dalilin faɗa dasukayi da Abdul bayan ankaita gidanshi ta tsigeleshi tayi gaba abinta, tana dawowa shine ta tarar da abinda yafi karfin kunnenta. Jin kalaman Habeeb yasa tafaɗi ta suma! Mommy ta tsala ihu ta iso wajen da Beebah take kwance ƙasa!... _✅ote comment and share pls_ ✍️ *Jiddah S Mapi* [6/23, 12:50 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to all my fans_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *WATTPAD* _Jiddah S Mapi_ Page 45&46 "Mommy ce tayi kan Beebah dagudu tana ihu, ganin haka yasa Bintu tayi sauri ta ɗauko goran swan a frij tazo aka shafawa Beebah afuska, a hankali ta sauke ajiyar zuciya tana buɗe idonta tafara tambayan Habeeb, yaya me naji kana cewa? Kamar naji kace kanason Hassana kuma da Aure? Kamanta mu 'yan biyu ne da ita? Ko ka manta ciki ɗaya muka fito da ita? Allah yasa dai wasa kake, duk tabayoyin datake mishi tanayine cikin hawaye sannan ta Zubawa Habeeb ido, Mommy tayi shiru tanayi wa Habeeb kallon tuhuma. Da Habeeb yaga duk shi suke kallo, ciki kuwa hadda Bintu, sai kawai yafara kame kame, yajuya yafita a ɗakin. _Ango_ Abokansa ne suke ta zagin Abu wai an raina musu hankali, yaza'ayi ranar Aure a nemi Amarya arasa, Abdul yatsaya yakasa yin komai sai gyara gari yake tin ɗazu da goge zufa, Yakira numban Bintu yafi sau 20 ba'a ɗaga ba! Azuciyarshi yace kodai yaudarana dama takeda niyan yi? Ahmad ne yadafa kafaɗan Habeeb yace "kadaina tunani dude" insha Allah gobe Zamuje gidansu Amaryar tafaɗa mana meyake faruwa, domin kasan lamarin Aure yanzu, kowa yana kokarin yaga an ɓata, Abdul ne yace "Haba Ahmad kana gani fa yarinyannan tadinga wulaƙanta ni a idon duniya, Aure wasane? Hakafa ranan kamu ta tafi tabar wajen saida ɗayar 'yan biyunta tazauna awajen, yanzu kowa yazata Beebah ce Matata!... Wani irin magana ne kake faɗa dude? Kana nufin wannan ba itace kake Aura ba? Kuma ai naga pre-wedding pics ɗin da ita akai. Abdul ne yayi mishi bayanin duk abinda akayi, Ahmad yayi shiru yana tunani can yace "Amma Abdul ka tabka kuskure Babbah! Meya kaika ɗaukan hoto da 'yan biyun wacce kake Aura kuma kace Ba itace matarka ba! Kana ganin mutane baza suyi maka mumunan fahimta ba? agaskiya ka aikata Babban kuskure! Abdul yace "hakika Ahmad na aikata kuskure to amma tayaya zan wanke wannan kuskuren danayi"? Ahmad yace mafita ɗayane garemu shine kaje gobe ka ɗauko matarka koma muje tare, kacewa kanwarta ta ɗauko duk kayan da kukayi hotunan dashi saimu tafi tare dukanmu huɗu, Ita matarka saitasa kayan da wancan tasa ranar dazakuyi hoton koda shike ai su 'yan biyu ne, bazasu rasa kaya kala ɗaya ba, Idan munje wajen ɗaukan hoton, ni saina ɗauka da Beebah kai kuma ka ɗauka da matarka, sannan muɗauka dukanmu huɗu, kaga zamu juya kan mutane, ba kowa ne zai gano bakin zaren ba, idan aka tambayeka saikace ai Bintu itace matarka! Abdul wani sanyi yaji azuciyarshi, yacewa Ahmad to insha Allah haka za'ayi, nagode da wannan shawarar. Suka sallami abokanansu suka basu

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});