Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

A Gidanmu Take Book 1 Complete Hausa Novel – Ahmad’s Regret and Fateemah’s Mystery 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

bintu kota gama hadin? See me next page _Wattpad_ Jiddahpretty [6/23, 12:44 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story/written_by Jiddah S mapi _dedicated to fateemahsardauna_ Page 7&8 A take suka juyo ganin yadda mommy tayi maganan da karfi Nan take jikin nabeelah yayi sanyi ganin yadda yananayin mommy yacanza a lokaci kankani Haba nabeelah wannan wace irin magana ce meyasa kike son sa shakku a zuciyar 'Yar da Nina haifeta a cikina? shin bakida labarin Akwai 'yan biyun da Sam basa Kama da juna?" "meyasa ku mutane Bakwa gane abune yanzu da ace bani na haifi bintu ba dazaki hada abinda Baza'a taba cewa ke kika hada ba" saikuma tsaya "Gsky bana son irin wannan tambayar" Kai daga yau ma kada nakara ganinki da bintu Dan nan gaba bansan mezaki ce mata ba "Kiyi hakuri hajiya in Allah ya yadda hakan bazata Kara faruwa ba...." inji Nabeela "Banason dogon magana nabeela nariga nagama magana" hajiya ta mayar mata "Bintu wuce mutafi" Tafada cikin bacin rai "To mommy" cewar bintu wacce tinda mommy tafara fada ta Sunkuyar da kai saida zasu tafi ne takuma ɗaga kai tadubi Nabila wacce duk kunyar momy ya isheta *AHMAD* Dakyar habeeb yasamu ya lallabashi yai shiru "Ahmad gobe idan Allah yakaimu kafin in tafi dan Allah inason muje asibiti Aduba lfyrka dubi yadda karame" inji Habeeb "Aa base naje asibiti ba maganin cutana bana asibi bane Maganin cutana my teemah ne idan nasameta zan warke insha Allah" inji Ahmad "Toshikenan yanzu de ka kwanta kahuta sannan karage damuwa saboda zata haddasa maka cuta" inji Habeeb "Nima Bari nakira agida nafada musu na shaida bazan samu dawowa ba sai gobe" Mommy na isowa wajen Beebah tasamu sit nata ta zauna rai ɓace Beebah bataga fuskar tambaya ba Sai takarasa wajen Bintu tace "Bintu yanaga ran mommy a bace" "babu komai sis" inji Bintu saboda tasan idan Beebah taji maganarnan bazata ɗauka da sauki "Yazakice min ba komi bayan gashi ranta a matukar ɓace" "Nace miki ba komai ke meyasa kin fiye naci ne? Inji Bintu "Ko zaki dake nine to?" cewar Beebah "Nibance zan dake kiba dan haka kimatsa min anan" Bintu ta mayar mata "Zaki fara ko beebah meyasa bakya girmama tane tagirmeki fa" inji mommy Beebah ta zumburo baki tana kunkuni wai datayi magana sai ace ta girmeta abinda baifi ƴan mintuna ba "Yanzu de kutashi mutafi gida sabida yau yayanku ze dawo" cewar mommy "Yee mommy dagaske kik?"cewar beebah "Dama nataba miki karyane?" Nan wayan mommy yafara ringing "Yawwa ga shima yana Kira" amsawa tayi takara a kunnenta "Hello my son yakake? ok se gobe? Amma meyasa yau bazaka dawo ba? Ok to Allah yakaimu goben" saikuma ta kashe wayar "Kunga yayan nakuma yace se gobe ze dawo" mommy tafaɗa musu "Kai amma naji haushi mommy" cewar beebah Mommy tace "Yau da gobe duk dayane beebah kawai muyi addu'a Allah yakawo shi lafiya" "Ameen" cewar bintu _See me next page_ _wattpad_ Jiddahpretty [6/23, 12:44 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story by_ jiddah S mapi _dedicated to fateemah sardauna_ Page 9&10 Washe gari bayan sun gama breakfast ne, Habeeb yake cewa Ahmad "To kaga ni yau zan tafi kuma bazan dawo nan dawuri ba" Saboda wannan zuwanma dakyar mommy tabarni. Acewarta bataso nayi nesa da ita Dan Allah Ahmad kada kasa tinani a ranka Sannan kuma karka gaji da Zuwa gidanku neman tuba a wajen Mommynka "Aa Habeeb bazan iya zuwa inda mom take ba gsky" Sabida mom idan taganni bacin ranta karuwa yake Har Tana barazanar Zata tsinemin idan harna sake zuwa inda take Ba tareda Fateemah ba Kai innalillahi wa'inna ilaihiraji'un abun haryana kai da hakane Ahmad Wlh Habeeb shiyasa kaga damuwan sunyi min yawa narasa yanda zanyi Yanzu ma tafiyar da zakayi banso ba Koba komai kana debemin kewa. Amma yana iya, idan kaje ka gaida mommy Da kannan ka duka Nagode Allah yabar zumunci Habeeb yace Ameen Ahmad yace "Kashirya nakaika airport karkayi missing flight" Ok Bintu kinga yau broh ze dawo "Kizo mushiga kitchen dakanmu muhada mishi delicious" Bintu tace "Ok sis karki sami damuwa muje" Suka tashi suka shiga kitchen suna ta hira Mommy Tana kallonsu Tana Mejin farin ciki a zuciyarta tace "Allah yasake hada kanku my twins" *AHMAD* Tafiya suke a mota suna hira shida Habeeb. Nan Habeeb yake kara jaddada masa akan yakula da kanshi yadaina yawan tinani. Ahmad yace "kaga karka dameni tin jiya kana ta maimaitamin kalma daya kamar karatu" Ohh "dama nasan bazaka taba canza haliba Ahmad" Eh naji bazan canza ba Dahaka har suka isa airport *BINTU* Bintu kuwa anata aiki a kitchen bebba se surutu take zubawa. Banda eh, aa, to, Ba abinda Bintu take cewa har suka gama hada frid rice da kaji Bintu tahada sobo me cucumber Mommy tace "yanzu natura driver yaje dauko shi a airport Wai ya karaso" Yeeeee mommy "Aida kin fadamin da tare zamu tafi dashi" Kai Beebah kin fiye gaggawa Haba mommy "yabazanyi gaggawa ba yaufa kusan 2weeks ban ganshi ba sede waya" Bintu kuma murmushi kawai tayi Horn sukaji abakin gate Nan Beebah tafita da gudu Tana oyoyo yaya oyoyo Kafin driver yagama parking harta fara Bubbuga motan Seda yafito da sauri yana oyoyo my sis Nan ta rungumeshi kamkam Tana murna Yace ina dayarki? Tana falo itada mommy Ok mushiga daga ciki Suna tafiya Tana rike da waist nashi har suka shiga falon. Tana cewa "yaya kadauko tsaraban toh" Mushiga de tukun kinsan tsarabarki ta daban ce. Mommy tace "oyoyo my son sannu da zuwa nan itama ta rungumeshi tana murna" Bintu ta tsaya Tana tayi mishi murmushi Yace "kekam meyasa bazaki Waye ba Bintu" kullum kina cikin rashin sabo da mutum. Cheww Allah yakyauta halinnan naki. Kina gani fa 'yar uwarki tazo tayi min oyoyo Amma ke kina tsaye Daga nanne Bintu taje ta rungumeshi Yahada su duka uku ya rungume sunata murna "Ahmad yana komawa gida ya kwanta agado yana tinanin mommynshi da kanwarshi" Wai yau shine Kanwarshi wanda yafi so aduniya take gudunshi? "Yau shine mommynshi take ikirarin tsine mishi" "Idan yatuna rayuwarshi na da se yayi kuka" *WANENE AHMAD*? AHMAD KABEER yarone awajen alhaji kabeer. Alh kabeer shahararren dan kasuwane "Wanda yayi suna a duniya" Alhaji kabeer de dan asalin garin adamawa ne Shi asalin fulani ne Wanda yafara harkar kasuwanci tin yana saurayi Allah kuma ya buda "mishi sabida yanda yake da kyauta da taimakon talakawa" Alh kabeer yabude gidan marayu tin yana saurayi, sabida yadda Allah yasa mishi tausayin marayu a zuciyarshi. Dan hakane har yaki yin aure " dan yana gudun kar ya auri matar dazata hanashi taimakon marayu" Iyayenshi ne suka nema mishi aure Agidan marayu Wanda shiya bude da kanshi Acewarsu zatafi jin tausayin marayu 'yan uwanta "Inda suka nema mishi wata kyakkyawar yarinya me Suna mariya" "Ba matsala a auren mariya da alhaji kabeer sabida mariya Yarinyar kirkice" Bayan shekara hudu Allah be kawo musu haihuwa ba Har abun yafara damin mariya Inda alhaji kabeer yake cemata "karki damu mariya haihuwa na Allah ne" "Idan ma Allah be bamu b! Baga gidan marayu ba, semu dau daya murike kaman mu muka haifa Mariya tace "haba Alhaji kasan fa akwai banbanci tsakanin ɗa da kuma ɗan riko"

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});