Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 1

Chapter 1

A Gidanmu Take Book 1 Complete Hausa Novel – Ahmad’s Regret and Fateemah’s Mystery 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

[6/23, 12:43 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story/written by_ _jiddah S mapi_ _Follow me on wattpad_ jiddahpretty Hi guys this is my first story hope I will have your maximum co-op ration ❤️ *NOTE:* Banyi wannan littafin sabida wani ko wata ba, labarin kirkirrarre ne sabida haka akula sosai. _dedicated to fateemahsardauna_ Page 1&2 "Haba Ahmad meyasa bazaka dauki kaddara ba, kasani fa kowani dan Adam da irin tasa kaddarar, na wani yafi na wani amma Sam kai baka dauki kaddaraba. Nan naga Wanda aka kirada suna Ahmad ya dago kanshi, yana hawaye fuskarshi tayi ja, buɗe baki yayi yanason yin magana amma ya kas, sai kuka yake kamar wata mace, hadda shesheka dakyar ya iya cewa "Haba Habeeb ya bazanyi kuka ba, bacin kai kasan abinda yake damuna, idan Banyi kukaba me zanyi?" Yaƙare maganar cikin sanyin murya. Gyara zama Habeeb yayi haɗe da cewa. "Addu'a ya kamata kayi Ahmad, domin itace abinda yakamata kowani musulmi yayi, a lokacin daya samu kanshi cikin yanayi na kunci." "Ya isa haka Habeeb, ka ƙyaleni naji da abinda yake damuna, bawai ka cikani da surutunka ba, sanin kanka ne nayi babban rashi a rayuwata, rashin daba zan taɓa mantawa ba, tunda narasa FATEEMAH narasa komai, na wulaƙantata, na ƙuntata mata, nayi mata abinda bazata taɓa mantawa daniba, Ina zanga Fateemah? Ina zanji labarinta? tana raye ko Tana mace?" Ɗan jinkirtawa da maganan yayi, kana ya cigaba da cewa. "Idan Tana raye Ya Allah Ka bayyana min ita, idan kuma tamutu Allah Ka kai haske kabarinta!!" Ya ƙarashe maganan yana wani irin gunjin kuka. Awannan lokacin har Habeeb ba'a barshi abaya ba, duk dauriyanshi shima seda yayi hawaye, yana me tausayawa abokinnashi. *** *** "Wai Ina kike ne BINTU? kiyi sauri dan Allah kinsanfa mommy Tana jiranmu a mota." "Ina zuwa Sis HABEEBA, gyalena nake dubawa ban gani ba." Naji wata siririyar murya Tana fada. "Kiɗauki nawa a wardrobe mana bintu." Habeeba tafaɗi haka cikin yanayi na ƙosawa. "Okay nama dauka ae ganinan." Beentu tafaɗi haka tana mai ƙoƙarin yafa gyalen ajikinta. "Okay dama koban ce kidauka ba zaki dauka kenan?" Habeeba tafaɗa tana ɗan kallon gefen da Beentun take. Nan naga Beentu na sauƙowa daga kan step, cikin takunta mai ɗauke da nutsuwa. Farace sol doguwa siririya, tana da manya manyan idanu, bakinta dan karami, ƙoƙarin gyara gyallen take, tayadda zai zauna akanta. Cewa tayi "Haba My Hussaina, Kinsan fa bama haka dake, kuma naga kema ay kinasa abuna ko my sis?" "Da ma ay haka zakice, kullum se kinwa mutum laifi kizo kina mishi sanyin murya, to yanzu de muje kinga Mom nata kirana, kusan 6 missed calls tayi min" Habeeba tafaɗi haka tana mai duban wayarta dake riƙe a hanunta. "Okay to muje" Cewar Beentu. A tare suka fito daga falon suna sauri. _see me next page_ ✍️🏻 *Jidderh S Mapi* [6/23, 12:43 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story written by_ Jiddah S mapi _dedicated to fateemahsardauna_ _wattpad jiddahpretty_ Page 3&4 Suna fita daga falon habeeba ta kwalawa driver Kira yace gani hajiya tace Ina mommy yace ay hajiya ta dade da tafiya tace bazata iya jiranku ba idan kun gama ku sameta agidan abinci ok to kaimu driver yace to nan suka shiga motar suka tafi bayan driver yayi parking naga sun shiga wani waje me kyau Wanda naga ma'aikata da uniform suna rabawa mutane abinci wasu kuma suna dafawa Wasu na wanke plates daga gani de wannan gidan abinci ne Wanda yayi suna agarin ADAMAWA Ina daga kaina naga an rubuta HASSY and HUSSY'S KITCHEN suna fita a motar idanun mutane suka dawo kansu Ana tacewa kaga 'yan biyun hajiya bada kunku asare Kuje gida kuce yafadi habeeba ce kadai me cewa sannunku Samarai barka da war haka ita kuma bintu sai murmushi take nan naga sun nufo wata kykkyawar mata wacce zatakai shekara 40 habeeba tafada kan cinyar matar Tace mommy shine kikayi tafiyarki kika barmu matar da aka Kira da mommy naga tayi murmushi nan naga tsananin kamanta da habeeba tace ba dole natafi ba Kun tsaya kunata shirme kuma kunsan yau ranar biyan ma'aikata ne Mommy ai bintu ce ta tsayar damu kinsan yanayinta dayin Abu kamar karkashi Aa karki sake kizagammin ya zo maya my bintu kizauna anan Bintu tayi murmushi tace mom inason yau zanyi stew da kaima Mom tace Haba bintu yazaki gajiyar da kanki kizauna kihuta kinji my bintu Aa mom kibari zanyi Toshikenan bazan hanakiba jekiyi Ahmad dama nayi niyan tafiya yau amma bazan iya tafiya nabarka awannan yanayin ba Nagode habeeb Allah yabarmin kai dan Allah habeeb ko bayan na mutu idan kasamu my teemah dan Allah ka aureta sabida kai Kadai nayadda dakai Kai Kadai nasan zaka riketa da amana tinda kasan bakar wuyar datasha kasan na zalinceta naci amana dan Allah kayimin wannan alkawarin🙏🏻 _see me next page_ [6/23, 12:44 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story/written by Jiddah s mapi _dedicated To fateemahsardauna_ _wattpad_ Jiddahpretty Page 5&6 Ahmad kadaina irin wadannan maganganun Banajin dadinsu Sam meyasa kake maganar mutuwa bayan bakaga fateemahn kaba Ahmad insha Allah Bazaka mutu ba seka ga fateema Ka nemi yafiyanta Sannan ku Gina rayuwa me kyau Kuma inada tabbacin fateemah zata yafe maka Habeeb bana tinanin my teemah Zata yafemin koda bayan raina ne Habeeb babu abinda yake damina kamar yanda mommy tadau Zancennan da zafi ka duba kagani Yau kusan shekara daya ban sa mommy a idona ba Yazanyi da rayuwa ta ya karashe maganan yana me hawaye Abin tausayi Habeeb kam ba bakin magana Shi mamaki ma abun yake bashi wai ace yau Ahmad ne yake kuka yana fada mishi damuwanshi Shida magana ma be dameshi ba Gsky dayana da yanda ze taimaka mishi daya yayi Amma shi besan ma ta ina ze fara ba Allah ka gaggauta kawo mana karshen Matsalarnan Ameen *BINTU* Mommy wai meyasa bintu take zubar mana da class ne Kiduba fa yanzu wajen masu aiki zataje suyi tare Gsky mom abinda takeyi bata kyautawa wannan aji down ne😏 Habeeba kibi rayuwa a hankali Ita duniya a hankali ake binta Wanda batazo bama Tana jiranshi bale muda muke cikinta Ni gsky mom kina daurewa bintu gindi dama nasan Niba sona kike ba Bawai bana sonki bane beebah babu Wanda ze haifi da Yakishi sede idan kaddara ne mom tafada idonta yana cika da hawaye A hankali tajuya kanta yanda bintu bazata ganta ba ta goge idonta Bintu kuwa iyayen son aiki tanata girki suna dan hira da ma aikatan Dan ita ba ma'abociyar son magana bace Cikin hiranne wata Wanda suka dan saba da bintu Take tambayan bintu Friend dama inason inyi miki wata tambaya Ok nabeela inajinki Amma Allah yasa ranki baze baci ba Aa ba komai yi maganarki ok Dama inason tambayanki tum bayau ba Hajiyace ta haifeki!!!? Haba nabeela wannan wace irin magana ce yazakimin wannan tambayar? Bacin kinsan mu 'yan biyune nice babba Gsky bintu ba kowane ze yadda ba Duba da irin yanayinki Kiga beebah mana Tana Kama da hajiya Amma ke Sam babu abinda yahadaki da hajiya ta kamanni ko hali gsky akwai abun dubawa anan What are you saying nabeela!!!? Cewar mom Wanda tin farkon maganarsu takejinsu Ta taso tambayar

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});