Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

A Gidanmu Take Book 1 Complete Hausa Novel – Ahmad’s Regret and Fateemah’s Mystery 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

rayuwarta zai kasance ba! Tana cikin tinani taga Ahmad ya iso wajenta, A hankali ya tsunkuya ya rike hannayenta duka biyu. Ya sassauta murya Yanda ba wanda zaiji daga ita sai shi Yace "Wifey meyasa kikemin haka? Kodai baki yafe min bane? Kisani fa Allah ma muna mishi laifi ya yafe bale mutum ɗan Adam, Dan Allah na roke ki, ki taimakawa rayuwata Kece farin cikina Rabona danaji farin ciki acikin rayuwata tin ranan da wancan abun yafaru, Daga ranan Na daina ganin haske a rayuwata, ki tausayamin my Teemah. Inasonki!!! Inasonki!!! Inasonki!!! I love you with all my heart, Zan iya rasa rayuwata idan kika gujeni. My teema inason ki manta komai mu gina sabon rayuwa, Wallahi idan kika gujeni bazan taɓa gane hankalina ba! Yafaɗa cikin hawaye. Bintu dataga yana mata kuka gashi mutane sunata kallonsu, saita fara kokarin tayar dashi. Shi kuma yazauna akasa yaki tashi sai hawaye dayake kamar Amarya, Ganin haka yasa Bintu tace "na yafe maka duk abinda kamin, kuma bazan taɓa manta halaccin da iyayenka suka min ba! Ahmad na yafe maka duniya da lahira" Ahmad ne yafara dariya kuma yana hawayen farin ciki. MC. Ne yafara magana yace "ana neman duk Amaren da ango a fili, suzo su nuna mana farin cikin Dasuke ciki ayau. Ahmad ne yarike hanun Bintu, Habeeb yarike Hanun Fareedah, Abdul kuma yarike hanun Beebah, Tafiya suke suna ɗan rawa, yayinda mutane suka sa tafi suna ihu. Wakar biki yayi biki akasa musu, inda suka fara rawa Amma banda Bintu data tsaya tana dariya. Ahmad dayaga zata badashi afili, sai ya rike kwankwason ta yafara rawa, Bintu kamar kasa ya tsage tashige tsabar kunya. Tafara kokarin cire hanunshi ajikinta Amma ina yaki saima kara janyota jikinshi dayake. Dataga haka saita fara kuka tana tureshi. Ahmad ne ya rungumeta afilin yasa bakinshi daidai kunnenta yace "Haba wifey mutane fa suna kallonmu ki daina kukannan kinji wifey" Tafi sukaji anayi musu, Ahmad yasaketa! Taga ba kowa afili daga ita sai shi su Beebah sun tafi! Dj ne yasake musu wakan Romantic, Bintu kamar gunki sai juye juye tafara, Ahmad ne yarike kwankwasonta yana rawa da ita. Dj yace atafa musu Akasa tafi Awajen. Dahaka har aka gama lunching kowa yashiga motan mijinshi aka wuce dasu gidansu Beebah. Suna zuwa Bintu ko cire takalmi batayi ba! Ta kwanta akan gado tana nishin gajiya, Beebah ce tace "dama ya lafiyar kura bale takama zawo" Bintu tace yanzu nice kuran Beebah? Nafa lura kin fara rainani a 'yan kwanakinnan, dan kinga zakiyi Aure ko? To bara nafaɗa miki har yanzu ke yarinyace awajena ehen. Fareedah tace "wayaga Babba kema ai ba Auran kikayi ba! Tare dai zamusan komai" Bintu tace wannan magana taki tafi karfina! Kinga namayi bacci, Dukka suka kwashe da dariya. _Ahmad_ Jinshi yake kamar wani sabon halitta, suna zuwa gida yakwanta akan gado yafara tunanin wai yau Fateemarshi ce tazama mallakinshi? Yanzu gobe war haka suna tare da ita amatsayin mata da miji, Can't wait to see yafaɗa da murya. Habeeb dake gefe yace "Wai me kake faɗa ne Ahmad?" Wallahi ina ganin kamar karya ne wai gobe nida my Teemah a ɗaki ɗaya kan gado ɗaya? Can't wait to see wallahi cewar Ahmad, Habeeb ne yaji zuciyarshi tabuga!!! Yanzu gobe Bintu a ɗakin Ahmad zata kwana? Kuma kan gado ɗaya? Dasauri yafara faɗin Astaghfurullah Ashe yanzu ita matar wani ne. Ahmad ne yaga yanayin shi yace "lafiya Habeeb?" Habeeb yace lafiya lau ba komai Kai dai kafiye zumuɗi, Ahmad yace ba dole nayi zumuɗi ba! Rabona fa da mace tun muna tare da Bash. Habeeb ne yayi dariya yatashi yashiga toilet da niyan Alwala. Beebah ce tacewa su Bintu ku baza kuyi sallah bane? Bintu tace nifa bana sallah tin jiya! Fareedah ma tace ita sai jibi zata fara. Ita kuma Beebah yau period nata yazo! (Tofa kunga Amare da period ranan biki) *Washe gari* Mommyn Habeeb da Mommynsu Ahmad ne suka tarasu babvan falo, Sukayi musu nasiha me tsima zuciya. Daga karshe Mommyn Beebah takira dukka Amaren a ɗakinta, tayi musu nasiha irin na zaman Aure Sannan ta basu wasu sirrikan yanda zasubi da mazajensu. Ta ɗauko wasu turare acikin jakanta, tace "ga wannan ku tabbatar sai idan zaku kwanta kafin ku shafa kada ku kuskura kushafa idan zaku fita anguwa" Turaren matan Aure ne! Sukace "to" Suna fita bayan kofa Beebah ta makale ta buɗe turaren tashafa kafin ta rufe tafita. Taje tasamu kowa yahaɗa kayanshi, musu suke, wai mommynsu Ahmad tace a motar haya zata tafi bazata bi motar mijin kowa ba! Sunyi sunyi tabisu amotar Ahmad taki, Haka suka hakura, kowacce tashiga motar mijinta Suka ɗau hanyar Kaduna garin gomna. Bintu ce take kukan rabuwa da mommy acikin motar, Ahmad juyawa yake yana kallon yanda tarufe ido tana zuba kuka kamar karamar yarinya. A hankali yarike hanunta me laushi da tsantsi yafara wasa dashi, Ta sauke ajiyar zuciya jin hanunshi cikin nata yana murzawa! "Beebah kuwa uwar kauɗi, tana shiga Abdul yazuba mata ido Yana kallonta, jin kamshin turaren data shafa yasashi lumshe ido. Tazauna agefenshi kamar mutuniyar kirki, Yace matso! Tayi shiru tana kallonshi, gashi Idonshi arufe amna yana mata magana. Yasake cewa matso mana A hankali ta matso wajenshi Yarike hanunta yace "wani irin turare kika shafa?" Tace "turare nane" Yace ban yadda ba! Kifaɗamin gaskiya, Tace gaskiya nafaɗa maka, Yace "ok". "Fareedah kuma tana shiga motar Ta sunkutar da kanta tana wasa da yatsun hannunta, Habeeb yace "kisaki jikinki ni mijinki ne" ✍️🗒️ *Jidda S Mapi* [6/23, 12:52 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to all my fans_ *WATTPAD* Jiddah S Mapi *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *Godiya dubu ga masoyana masu bibiyar littafin Agidanmu Take!!! Banso labarin tazo muku a short story ba! Amma ya na iya Haka Allah yatsara, nagode da nuna soyayyarku gareni, banyi tsammanin first Novel ɗina zan samu masoya har haka ba! Sai gashi Allah yasa nasamu, alhmdllh ina godiya gareshi sannan ina godiya gareku* *Special thanks to mrs sardauna bazan manta dake ba!* *godiya ga Eeshart tnx for your comment i really appreciate* *Bazan manta dakai ba! Aliyu Ibrahim* *Much love to my Sister walidation S Mapi* *Ina miƙa gaisuwata da kuma godiyata ga ɗaukakin jama'ar kungiyar KAINUWA dashen Allah* *kuna raina kanne na! Walidation S Mapi da Hafsat Ibrahim Khalil* *Godiya ga ɗaukakin jama'ar group na Agidanmu Take!!! Bazan manta da kuba!* Page 57&58 🔚🔚🔚🔚 "Fareedah taɗan saki jiki kaɗan da Habeeb, ahanyansu nazuwa kaduna ansha love amota musamman Beebah data rikita ɗan mutane da turare, Bayan sun iso ne kowa yafito amotar a gajiye kamar an dakesu. Ahmad ne yanunawa Habeeb wasu gidaje tsararru kerarru haɗaɗɗu, guda uku yace "Habeeb kazaɓi gida ɗaya acikin waɗannnan" Habeeb yace "kowannema nagode basai nazaɓa ba! Allah yasaka da alkhairi sannan yabar zumunci" Ahmad yace "Ameen" To tinda gidan uku be kuma ajere komai naciki kala ɗaya ne nizan zauna a tsakiya tinda nine karami Dukka suka kwashe da dariya Habeeb ne yarike hanun matarshi yace sai kun karaso. Ahmad yace daɗin Abin dai baza'aci fuskarmu ba! Kowama yanada tashi.

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});