Chapter 9
Chapter 9
yake yi, ita kuma tana tsananin son sanin halin da ‘yar uwarta take ciki yasa ta dauki kofin shayin ta runtse ido ta fara sha cikin sauri, tana ji zuciyarta na tashi sabo da madarar da ya cika a shayin amma bata a jiye kofin ba sai data shanye. “Yauwa! koke fa Baby na... ashe kina buqatar mu fita....” Amman data wanke masa jiki dashi shiya katse masa maganar da yakeyi. “Oh My God.” Ya fada cikin damuwa, sannan ya fara jera mata sannu tamkar zai ari baki, sai ya lura ta gama amayar da duk wani abu data ci sannan ya tallabeta zuwa ban dakin bed room din data kwana a ciki, ya tara mata ruwan wanka ya sirka sannan ya fita yaja mata qofar. Sai daya gama gyara gurin data yi a man sannan ya nufi dayan bandakin da yake dayan dakin yayi wanka. A minti arba’in ya gama shirya wa, ganin lokacin sallar azahar yayi yasa yai alwala ya nufi masallaci ba tare da ya waiwayi dakin da take ba. Itama sallar ta yi bayan ta gama shiryawa cikin wata doguwar rigar, sannan ta hakimce a falo tana jiran dawowarsa. Basu sha wata wahala ba lokacin da suka isa Ofishin ‘yan sandan, bayan Abdul ya nuna musu I.D Card dinsa cikin qanqanin lokaci suka sada su da Ofishin D.P.O na gurin, sananne ne a gurin Abdul don haka suka gaisa cikin raha da barkwanci. “Wannan Madam ce Abdul?” Tambayar da ya yiwa Abdul din kenan bayan ya lura da yanda Abdul din ke damqe da hannunta yana kakkareta. “Eh ranka ya dade.” Amsar da ya bashi kenan a gajarce yana kallon qwayar idanun Aysha. "Da ganin irin wannan kulawar da kake bata ai nasan amarya ce, Allah ya bada zaman lafiya, gaskiya kunyi matuqar dacewa da junanku" “Amin na gode Sir.” Abdul ya amsa addu’ar da ya yi masa, bata ce komai ba illah sake daure fuska data yi, har suka gama barkwancinsu bata gaida D.P.O ba sai shine ya ce, “Madam barka dai.” Ganin yanda Abdul ya tsareta da idanu yasa tace, “Yauwa” “Ranka ya dad'e a kan case din yarinyar da aka tsinci gawarta a wani kango yau da asubah mukazo, yarinyar qanwata ce, jiya da daddare mun fita cin abinci da matata da qanwar tawa a can muka nemeta mu rasa, saboda dare yasa bamu bada cigiya ba a gidan Radio muna jiran sai yau da safe, to sai kuma ga wannan mummunan labari da muka samu, shi yasa muka zo nan kai tsaye don samun bayani a kan in da a ka tsinceta da kuma dalilin mutuwarta ta.” “Oh My God! Sister din ka ce? Allah ya gafarta mata” D.P.O ya fadi haka cikin jimami. "Amin summa amin" Suka amsa gaba dayansu. “Yanzu dai muna zaman jiran binciken likitoci ne a kan gawar, na ba babban likitan lambar wayata, idan suka gama bincike..." Ringing din wayar D.P.O shiya katse masa maganar da yake yi. "Hello Dr." Abinda ya fara fad'i kenan daga bangarensa, sannan yayi shiru yana saurare daga can 6angaren, "Ok to! gamu nan zuwa, an samu ‘yan uwan yarinyar" Nan take gaba daya suka dunguma zuwa asibiti a motan Abdul din. Suna zaune gaba dayansu a Ofishin likitan suna sauraron sakamakon binciken dalilin mutuwar Sadiya da yake karanto masu daga wata farar takarda da take hannunshi. “Wadanda suka saceta sun yi qoqarin biyan buqatarsu da ita ne ta qarfi ita kuma ta yi qoqarin qwatar kanta, sunyi artabu sosai hakan yasa sukayi mata munanan raunika a duk wani sashe na jikinta, sannan sukai mata mummunar fyade, duk ciwukan jikinta yafi qazanta a matancinta, har yanzu da babu rai a jikinta matancinta yana fitar da jini, ba mutum daya ko biyu ne suka yi mata fyade ba, zasu kai mutum biyar zuwa bakwai. Al’amarin ya qazanta sosai gaskiya, domin a binciken da muka yi mun gano tun kafin su gama aikata masha’a da ita rai ya fice da jikinta. Duk in da masu laifin nan suke ya kamata a nemo su donsu fuskanci hukuncin daya dace dasu. A yanzu mun gama duk abinda ya dace muyi, saura naku na jami’an tsaro" Ganin gawar Sadiya shine abinda yasa ta jingina jikinta sosai da na Abdul hankalinta a matukar tashe, zuciyarta a bushe take ko digon hawaye ta kasa fitarwa. Shima qara tallafeta ya yi, domin ya lura da yanda jiri yake diban ta. Duk sassan jikin Sadiya ciwo ne har da su yakushi bayan yanka da wuqa, basu iya kallon matancinta ba saboda bayanin da likita ya yi musu. Basu jima a asibitin ba Abdul ya yi sallama da D.P.O a kan cewa zai maida Madam gida ya dawo. A mota babu mai cewa wani qala, idanun Aysha sun bushe qyamas ko a lamar hawaye babu, zuciyarta a dake take. Aysha a zuciyarta take fadin cewa ya zama dole su dauki fansar mutuwar Sady koda hakan shine abu na qarshe da zata gudanar a rayuwarta. Suna shiga gidan taja ta tsaya a falon, kallon qwayar idanunta kawai yayi ya san rigima ce fal a cikinta. Kiran da ya shigo wayarsa ne ya katse mata hanzari, shi kuma Abdul din ya nemi guri ya zauna a nutse, daga yanda yake amsa wayar ne ya bata tabbacin da wani mutum mai muhimmanci yake magana, ganin yanda yake kallonta yana amsawa da “To ard'o! Eh muna tare da ita tun jiya, a tayamu da addu’a…To…na gode! sai munyi waya.” Duk da Aysha bata san me ake fada masa daga can 6angaren ba ta san maganarta ake yi, hakan yasa duk taji ta tsargu, ba shiri ta nemi guri ta zauna. Kallonta yayi, sannan yace, "Yanzu kin yarda da abinda nake gaya miki ko? Ina bin diddigin al’amuranki tare da sawa ayi miki addu’a tun ranar da na fara haduwa dake, kuma hakan ya samo aSali ne daga irin tsananin son da nake miki. Kya6e baki kawai tayi, alamun ko a jikinta, kamar bazata amsashi ba sai kuma tace, “Ina son in koma gida, don in sanar da ‘yan uwana halin da ake ciki, kuma mu yi shawarar ta inda zamu fara bincike domin gano wadanda suka aikata mana wannan zaluncin" “Ki bar maganar bincike a hannuna, domin da ni yafi dacewa, kuma ‘yar uwata ce kamar yanda na sanarwa D.P.O" Abdul ya fadi hakan ba tare da ya kalli inda take ba, saina ya cigaba da danna wayarsa "To ni dai ina son tafiya gida" Ta sake fadin haka bayan ta watsa masa wani mugun kallo. Fuskar Abdul a daure yake kallonta ido cikin ido, “Ki daina maganar komawarki gida, domin sam bazan bari ki cigaba da aiki irin na jaruman maza ba” “To saboda me? Wai ma ina ruwanka dani ne da kake neman takurawa rayuwata??” Aysha ta fada cikin masifa tana riqe da kugu bayan ta miqe tsaye. “Saboda sam bai dace dake ba" Abdul ya fada daga inda yake zaune, babu damuwa ko kadan a fuskarsa. "To ina ruwanka? Ina ruwanka da rayuwata? nifa wallahi ka takura min, ban sanka ba, bansan daga inda ka fito ba, haka kawai ina gudunar da rayuwata zaka zamemin qarfan qafa. Bayan duk A DALILIN DA NAMIJI muka tsinci kanmu a wannan hali da muke ciki. dole
Table of Contents