Chapter 14
Chapter 14
hankalinta kan Hidaya ta ce, “Allah ya kyauta wannan ta kasance daga cikin zuriyarmu. Wannan da kike ganinta ba kowa ba ce face Karuwa!! irin ‘yan iskan qananan karuwan nan da duk inda suka ga kyakykyawan Matashi da kudi sai suyi ta bibiyarshi ko da ta hanyar asiri ne har sai sun cimma biyan buqatarsu a kanshi" Ta fadi hakan cikin karaji da d'aga murya don Aysha ta ji abinda ta ce. “Amma dai anyi asarar kyau, irin wannan ai zama ya kamata kiyi a gida duk kwarton daya matsu ai ya san inda zai sameki.” Hidaya ta watso mata wadannan maganganu don taya qawarta yaqi. Cikin jin dadi Yasmin ta ce, "Ya za’a yi ta zauna a gida Hidaya? Tun tana qarama ta saba hulda da ‘yan bariki irinta duk randa bata samu matayi ba kinga dole ta fito ta nema" “Amma kinyi kuskure qaramar ‘yar iska, wannan karon komarki bata kamo komai ba, kin fad'a inda zaki kwashi kashinki a hannu” Hidaya ta fadi haka, sannan ta mike ta fara daure gyalenta a k'ugu. Duk maganganun da suke yiwa Aysha tana jinsu, bata motsa daga inda take zaune ba kamar yanda bata fasa shan lipton dinta ba, sai data gama sannan ta maida hankalinta gaba daya kansu bayan ta dora qafa daya kan daya, murmushi ne a kan fuskarta domin har ga Allah maganganun da suke mata dariya suke bata. Saida ta gama kare musu kallo ta maida hankalinta kan Yasmin tace “Hajiya in tambayeki mana?" “Ina jinki qaramar karuwa" Yasmin ta amsa tana jijjiga jiki tamkar zata rufe Aysha da duka, "Menene tsakaninki da mai gidan nan? Ta tambayeta ido cikin ido da alamun nuna rashin damuwa da sunan da ta kira ta dashi. "Kanwarshi, Kuma mai niyyar zama amaryarshi nan da watanni hudu masu zuwa” Hidaya ta amsa ta cikin gadara da isa irin tasu ta gwanaye a fagen shisshigi. Sai da Aysha ta watsa mata kallon kashedi sannan ta ce “Ban kasa dake ba bare har ki tsomamin wawwaran bakinki, ki jira idan Uwardakin naki ta gaza sai ki dora daga inda ta tsaya" “Ai amsar da ta baki gaskiya ne, ko kina musu ne in qara tabbatar miki da haka ta hanyar lakad'a miki dukan kawo wuqa?” Yasmin ta amsa a fusace sannan ta mike tsaye tana gyara d'amara da gyalenta. Sai da Aysha tayi dan dariya jin amsar da Yasmin ta bata, da mamakin jin cewar da ta yi zata mata duka Aysha ta kalleta ta ce, “Kina nufin kina da qarfin iko a kan Abdul kenan?” “Qwarai da gaske.” Ta amsa tun kafin Aysha ta qarasa aje numfashin maganarta. "Da kyau! don Allah idan Abdul ya dawo gidannan ki saka shi ya koreni a gidanshi, idan kikamin haka tabbas zan gane cewar Abdul naki ne ke kadai. Kuma soyayyar shi tafi qarfina” Ta fadi haka duk da bata jin son Abdul dai dai da qwayar zarra a zuciyarta. “Lallai kam zan tabbatar miki ina da qarfin iko a kanshi, saboda isa ta ma tun kafin ya dawo gidan zan kora ki inda kika fito, bayan mun miki dukan kawo wuka ni da qawata, yanda ko a hanya kika ga Abdul ba zaki sake marmarin kallonshi ba balle har kice kina sonshi" “To bisimillah ga fili ga mai doki, kuma inda ba kasa ai nan ake gardamar kokawa” ta fada bayan ta gyara kwanciyarta a kan kushin din da take zaune. Jikin T.V Yasmin ta nufa da sauri ta fara qoqarin zaro wayoyin da zasu doki Aysha dashi, tana qoqarin ciro wayoyin tana jifanta da duk wata mummunar kalma da tazo bakinta Hidaya tana tayata. “Banza wulaqantacciya, karuwa! da idon Allah haka zaki qare abin dakin mazaje kwararo kwararo har daga qarshe ki samu wanda ya fiki gogewa a bariki ya sanya miki cuta mai karya garkuwar jiki ki mutu a wulakance." Kaf wadannan maganganu a kunnen Abdul daya bude qofar falon ya shigo cikin sauri. Ranshi a matukar 6ace yake kallonta, “Yasmin ashe baki da mutunci?” ya fada cikin mamakin maganganun da ya ji suna fita daga bakinta. Da matukar fushi ta tare shi da cewa, “Akwai babban mara mutunci daya wuce kai Abdul? Idan ka matsu da yawa ai bai kamata ka kawo karuwa irin wannan ba, sai ka je can Yola ka samu Ardo ka yi masa bayanin a matse kake, kaga daga nan sai a sassauto da daurin auren mu zuwa nan da sati daya...” Da matukar mamaki a fuskarsa yake kallonta, ya ce, “Haka kika ce ko?” "Qwarai kuwa.” Ta amsa tana girgiza kafada cikin tsantsar rashin kunya. Ya gyada kai alamar ya fahimta, ya kara mata da cewa “To wannan karuwar da kike gani aurenta zanyi, kuma nafi sonta dake fitsararriya mara tarbiya, idan kuma kin cika ‘yar iska ki qara tanka mini idan ban farfasa miki jiki ba.” Ya fadi hakan bayan ya zare belt din wandonsa, sanin da ta yi tsab zai aikata abinda ya fada yasa ta dauki gyalenta da jakarta ta nufi qofa, Hidaya kuwa dama tunda taga shigowarshi ta sa6e ba tare da kowa ya lura da fitarta ba sai Aysha. “Zaka gani wallahi, wanda ya daure maka gindi shi zan samu inyi masa bayanin duk iskancin da kake yi.” Da gudu Abdul ya bita tuni ta fice daga falon a guje, Hidaya tana ganin fitowarta da gudu ta rufa mata baya, ko motarta bata dauka ba sai me keke Napep suka dauka ya kaisu har gidan su Yasmin. Yana zaune a kan kushin yana sauke numfashi cikin tsananin fushi da qunar zuciya, baqaqen maganganun dasu Yasmin suka ringa jifan Aysha dashi musamman kalmar nan ta (Karuwa) yaqi 6acewa daga zuciyarsa, saboda tsabagen kunya ya kasa had'a idanu da ita, ita kuma ko ajikinta wai an yakushi kakkaura. tunawar da ta yi ko sallar azahar bata yi ba gashi har la’asar ta kawo jiki yasa ta miqe da sauri ta nufi cikin Bed room din da take kwana. Tana bada baya ya bita da kallo yana tunanin ko jakar kayanta zata dauko ta ce dashi lallai ya maida ita inda ya dauko ta, dan haka tagumi ya yi yana tunanin kalmomin da zai rarrasheta dasu, ganin ta dauki tsawon lokaci bata fito ba ya sashi sakin a jiyar zuciya, ya nufi dakinshi ya watsa ruwa sannan yai sallar azahar da la’asar a cikin dakin, don yana tsoron fita zuwa masallaci ita kuma ta fice daga gidan. Yana zaune a falo ya shirya cikin qana nan kaya sai baza qamshi yake yi, Aysha ta shiga falon da siririyar sallama a bakinta, ta yi matsakaiciyar kwalliya cikin doguwar riga pople da dan siririn mayafi a kanta, ita kanta tasan ta yi kyau don dama ita din mai kyau ce, kallo kawai ya bita dashi a zuciyarshi tasbihi yake ga Ubangiji daya kyautata halittar Aysha. “Yarinya kamar ita ta halicci kanta. ya Allah ka azurtani da wannan kyakykyawar yarinya a matsayin matar aure (Amin)" ya yi addu’ar da iya le6anshi ta tsaya sannan ya amsa a zuciyarshi. “Aysha don Allah ki yi haquri da duk maganganun da su Yasmin suka fada miki" Ya fada bayan ya gama kame-kame ya rasa ta inda zai fara bata haquri. Dan Murmushi tayi masa tace “Laaaaa... Babu damuwa fa"
Table of Contents