Chapter 20
Chapter 20
zan iya barci ba” Dariya ta qyalqyale da shi, ta ce “Abdul ni fa yanzu na zama surukarka, don haka dole girma da kunya ya ringa shiga tsakaninmu.” “Haka ne kuma fa Aunty, to dan taimaka ki ba ni diyarki a waya in yi mata sai da safe.” Murmushi ta yi daga bisani kuma ta katse wayar tana shafa gashin kan Aisha da ke kwance a jikinta. "Babyna Abdul yana tsananin son ki sosai, a yadda na tausaya miki a tarihinki da kika ba ni kin ga yanzu A DALILIN DA NAMIJIN kin samu waraka daga duk wani qunci da DA NAMIJI ya dasa miki a zuciya. Ina tabbatar miki Abdul sai ya zame miki bawa a kan soyayyarki. Kin ga NAMIJI ya yi miki rauni, sannan Da NAMIJI ya warkar da ke. Don ba duka suka taru suka zama daya ba.” “Haka ne kam Mummyna. Ni ma a yanzu na yarda da batunki. Tabbas a maza akwai gurbatattu kuma akwai na kirki. A DALILIN DA NAMIJI na ga duhu da haske a cikin rayuwata… QARSHEN KASHI NA BIYU
Table of Contents