Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

A Dalilin Da Namiji Book 2 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

maida idanunshi hanyar harabar fita gurin cin abinci, da yake ba ya sanye da uniform don haka babu wanda zai yi tsammanin shi jami’in tsaro ne. Minti daya minti biyu har zuwa minti talatin bataga dawowar Sadiya ba, jikinta ke bata ba lafiya ba amma duk da haka bata miqe daga kujerar da take zaune ba, kuma bata ta6a komai ba daga cikin kayan abincin da service ta kawo musu, Shi kanshi da yake tsaye ya lura da rashin dawowar abokiyar tafiyar tata, don haka bayyi sanya gurin bin bayanta ba, babu ko alamarta a harabar gurin, babbar matsalar ita ce bai san da wace iriyar mota suka je gurin ba, motoci ne sama da ashirin a gurin don haka ya tsaya yana tunanin abinda zayyi, minti daya tsakani ya koma cikin gidan abincin, yaga service din da takai mata abinci cikin dakin da take zaune don haka gurinta ya nufa. Bill din kudin abincin da takaima wadannan ‘yan matan ya tambayeta, nan take ta fada masa ya biya sannan ya koma ainihin gurin zamanshi na farko ya zauna yana fuskantar qofar dakin da take zaune. Qarfe tara dai dai na dare agogon dakin da take ciki ya buga, hakan shi ya tabbatar mata da awa daya kenan dai dai Sadiya bata dawo ba, da kuzari ta miqe da nufin ta fita ta duba domin tabbas babu lafiya, bata kalli abincin ba ta fice daga dakin, yana ganin fitarta yabi bayanta domin dama fitowarta yake jira. Motar da suka zo da ita tana na a ajiye a inda take, amma abinda ya bata mamaki shi nen ganin motar a bude, wayoyinta suna a jiye a inda ta barsu, data bude aljihun motar inda take a jiyar kudi komai yana nan a inda yake, babu alamar an ta6a wani abu, amma babu alamar Sadiya a gurin, kanta a kulle yake sam ta rasa irin tunanin da zata yi. “Me yake shirin faruwa dani ne.” Tambayar data yiwa kanta kenan jikinta a sanyaye ta zauna a kujerar gaba ta motar ta dafa kanta da hannu biyu tana jin kamar juwa tana dibarta. “Aysha me yake faruwa ne?” Abdul ya tambayeta yana tsaye jkin motar ta inda take zaune. Shiru ta yi bata da niyyar amsa masa tambayarsa har tsawon minti biyar, kuma ta ji tambayar daya yi mata. “Aysha don girman Allah kiyimin magana.” Ya fada cikin salon roqo da marairaicewa. A hankali ta dago da kanta idanunta sun kara canza launi sosai. “Nima ban san abinda yake faruwa ba, banga ‘yar uwata da mukazo nan gurin tare da ita ba” Ta amsa masa daqyar tana lumshe idanu tana budewa. Motoci ne fiye da ashirin a gurin amma sai da yabi lungunan motocin yana dubawa amma ba Sadiya ba alamarta. Qofar gidan abincin ya koma ya tambayi wani mai shagon ice cream ko yaga wucewar wata yarinya tana sanye da doguwar riga? “Yan mata nawa ne masu dogayan riguna da suka fice ta nan? ai suna da yawa ranka ya dad'e, don haka ba zan iya gane wacce kake magana a kanta ba.” Amsar da mai shagon ya basa kenan ya koma kan sana’arsa. “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un, me yake shirin faruwa ne?” Ya fada a fili lokacin da agogon hannunshi ya buga qarfe goma sha biyu na dare a wannan lokacin motocin gurin duk sun gama watsewa, sai ‘yan dai dai ku da ba za’a rasa ba. Motar ta ya koma don ganin ko a wane hali take ciki, tana zaune a inda ya barta amma idanunta a rufe suke. “Aysha… Aysha… Aysha… sai da ya kirata sunanta ya fi a qirga amma bata amsa ba. “Aysha don Allah ki yi mini magana mana.” Nan ma dai shiru ta yi bata bashi amsa ba. Tabbas bata da lafiya domin duk miskilancinta idan ya hadata da Allah tana amsa masa, don haka ya yi tunanin ko ta yi barci ne. *** Yana zaune yana jan casbaha bayan ya idar da nafilfilin dashi kanshi bai san iya adadin raka’o’in da ya yi ba, lokaci zuwa lokaci yana mai da idanunshi kan faffadan gadon dake gefensa qirar Italiya, inda ya kwantar da ita ba tare da ta san a wane hali take ciki ba. Kallon a gogon bangon dake maqale a dakin yayi wanda ya nuna masa qarfe hudi daidai na asubahi, hakan shiya tabbatar masa da awanni uku kenan da kwantar da ita a kan gado, domin bai bar gidan abincin ba sai wajen qarfe daya saura kwata na dare, bayan duk jama’a sun gama watsewa. Motoci biyar suka rage a gurin biyu daga ciki tasu ce shi da Aysha, uku kuma baisan mamallakansu ba, motarshi ya matsar kusa da in da ta faka tata motar, da bisimillah ya dauko ta cak ya kwantar da ita a bayan tashi motar, idanunshi a runtse, yana jin wani iri a zuciyarsa. Sannan ya kwashe wayoyinta da kudi da duk wani abu muhimmi da yake cikin motar Aysha. Haka nan ya bar motar tata a gurin kuma a bude, a zuciyarshi yake addu’ar “Ya Allah ga ajiyar motar Aysha nan.” Har ya isa muhallinshi bata san a ina kanta yake ba, don haka ya sake daukarta cak kamar ‘yar qaramar yarinya har zuwa Bed room dinsa, a zuciyarsa yana ta istigfari. Tashi yayi daga kan dardumar da hanzari kamar ya yi mantuwar wani muhimmin abu yana buqatar ya je ya dauko. Kofi ya dauka a saman frig sannan ya dauki robar ruwan Swan mara sanyi ya nufi gadon da take kwance, fuskarta fayau a idanunsa sai yaga ta qara masa kyau fiye da da domin bai ta6a mata kallon qurilla irin na yau ba. Addu’o’I yake ta tofawa kala kala a ruwan da ya zuba a cikin kofin da yake hannunsa, sai da ya dauki tsawon minti goma yana addu’a sannan ya fara shafa mata ruwan addu’ar a fuskarta bakinshi dauke da Bisimillah, tsawon lokaci yana shafa mata ruwan addua har ladanin unguwarsu ya kwad'a kiran sallar farko na asubahi, kan frige ya ajiye kofin sannan ya nufi bandaki ya sake dauro alwalar sallar asubahi. Tana zaune daram a kan gadon tana bin lougo da saqo na dakin da kallo don tantance shin a ina take? Bata tantance ba ta ji motsin bude qofa don haka ta maida kallon ta gurin don ganin mai shigowa, idanunta a cikin nashi sukai musayar kallo tsawon minti daya, shine ya fara saukar da kwayar idanun shi sannan ya qara fadada fara’ar fuskar shi yana fadin, “Alhamdulillahi kin tashi?” Har a wannan lokacin bata sauke qwayar idanunta ta daga kanshi ba, kallo daya ta yi mishi ta gane shi, dan Sandan nan ne da yake neman takurawa rayuwar ta. Daure fuska ta yi dam! sannan ta watsa masa harara cikin masifa tace “kai malam! menen gaminka dani kake neman takura min? Ina yar uwa ta Sadiya?" Ta watsa mishi tambayar duk da bata da tabbacin ya ganta ko bai gan taba. Saida ya tatusasa muryarshi kasa-kasa sannan ya fara magana da cewa “Ki kwantar da hankali ki don Allah Aysha, wallahi bani da nufin cutar da ke, yanzu dai kinga na yi alwala zan tafi masallaci, ki bari idan na dawo sai muyi maganar" Da baya da baya

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});