Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

A Dalilin Da Namiji Book 2 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Yasmin da Iyayenta suna yiwa Hidaya manyan kyautuka na kudi da kayan masarufin da har suke samun rufin asiri ita da mahaifanta. Yasmin ce ta koyawa Hidaya mota har ya zama a lokuta da dama Hidaya ce take jan mota zuwa duk in da zasu. **** Duk yanda yaso ya 6oye damuwar shi a gaban Likitan ya kasa samun nasarar haka, abinda ya qara fadada damuwarshi shine yanda yayi ta kiran wayar Yasmin har sau biyar "Is Swich Off!" Kamar yanda Computer take fada mishi. Likitan ya sake kallonshi yace, "Inspector lafiya kuwa?” Cikin mamaki yake masa wannan tambayar ganin daga amsa waya matashin dan sandan ya shiga damuwa. Dan Murmushin yake yayi yace, “Ba matsala Dr. ci gaba da bayaninka. Ina saurarenka” Ya fada cikin qarfin hali bayan ya yi kakarin fadada fuskarsa da murmushi. “Wadannan sune takardun duk wani bincike da muka gudanar a kan gawar yarinyar.” Ya fada bayan ya miqa masa fararen takardun hannayenshi, ya zazzaga File din sai ga wata sarqa irin wadda gayu suke sakawa a wuya ta fado. “Wannan kuma a hannun gawar muka samu ta damqeshi kam a hannunta na dama, da qyar muka samu nasarar bude hannun muka cire shi, amma kuma bana tunanin sarqar zai taimaka maka gurin gano wadanda suka aikata laifin” Likitan ya fadi haka bayan ya miqa masa sarqar hannunshi da file din da takardun da suke ciki. Sama sama Abdul ya kalli sarqar sannan ya hada komai ya maida cikin file din kamar yanda likitan ya dauko da farko. Gaba daya hankalinsa yana kan Aysha don haka yayi gaggawar sallamar likitan tare da yi masa godiya a kan lokacin da ya bashi. Shima likitan godiya yayi ma Abdul gami da yi masa fatan samun nasara a kan abinda yasa gaba, sannan ya yi alqawarin baiwa Abdul din hadin kai a duk lokacin da ya neme shi. Qarfe biyu saura kwata agogon motar tashi ya nuna, hakan shiya bashi tabbacin awa hudu da minti arba’in da biyar kenan da fitowarsa daga gida. sallama suka yi da Sajent Nalado, bayan ya ba Sajent din kudi masu yawa a kan yaje ya wanko masa hotunan nan, ya ci abinci ya koma Office ya jira dawowarsa. Gudu yake da motar kamar zai tashi sama, burinshi da addu’arshi ya isa gida kafin su Yasmin su isa duk da yasan hakan ba abune mai yuwuwa ba, tun dazu Yasmin ta ba shi tabbacin suna hanyar gidan nashi, kuma daga lokacin zuwa yanzu an samu tsawon minti arba’in da biyar. Suna shiga gidan suka watsar da jakunkuna da mayafansu a falo, kichin Yasmin ta nufa tadauko musu kofuna ta dawo sannan ta bude frij din falon ta dau lemo, suka dararrashe suna sha suna hira, babu wata alama da suka gani a falon wanda zai tabbatar musu da wata halitta a gidan, hankali kwance suke hirar son da Yasmin take yiwa Abdul, labari take bawa Hidaya a kan irin salon soyayyar da zata gwadawa Yaya Abdul dinta idan aka daura musu aure “Kuma kinsan abin da ke qara kwantar mini da hankali?" Ta tambayata fuskarta dauke da fara’a Girgiza kai hidaya tayi alamar A'a, ta kara da cewa "Sai kin fada farin watan Abdul Ahad" Fati tayi da Idanunta ta cigaba da cewa “Mu a familynmu sam ba a auran mata biyu, duk iyayenmu Maza matansu dai dai ne, kuma duk ‘yan uwan juna, kakanmu ne kawai mai mata hudu. kuma tun daga kanshi ya haramtawa ko wane da Namiji da yake zuri’armu auren mata biyu. Kinga aurena da Yaya Abdul mutu ka raba, bani babu fargabar zaiyi mini kishiya balle har hawan jini ya kamani” Da matuqar mamaki Hidaya take taya qawarta ta murnar ita da Abdul mutu ka raba, amma a zuciyarta dariyar wauta da wawancin qawarta takeyi, domin a zuciyarta take jin Abdul bazai ta6a zama da Yasmin a matsayin mata ita kadai ba, domin babu wani alamun mugun son Yasmin a tattare dashi. Agogon Bed room yana buga qarfe biyu dai dai Aysha ta bude qwayar idanunta daga barcin da ta dauki awanni biyar tana yi, bala’in yunwa take ji don haka ta fada bandaki da sauri ta yi brush, tana sanye da best fara kar da gajeren wando Three quater baqi, tunanin da tayi a kan sai yamma Abdul zai dawo don haka ta saki jiki ta yi shigar da take so sannan tasha magani ta kwanta, dukda taga lokacin sallah yayi amma tayi niyyar shan ruwan lipton sannan ta dawo daki don sauke farali. Hayaniya da dariyar da Aysha take jiyowa a falo baisa ta fasa nufar falon ko kuma ta koma daki ta canza kayan jikinta ba, ita sam ta ma manta da wane irin kaya take sanye dashi, gashin kanta ya sauka har qasan kafad'unta yana kwance luf luf gwanin ban sha'awa, siririyar sallama tayi sannan ta sanya kanta cikin falon. Dif suka dauke wuta, suka k'ame k'am tamkar masu shirin daukar hoto, kallo daya Aysha ta yi musu ta kauda kanta ta nufi kan dining table donjin da ta yi ko sallamarta basu samu sararin amsawa ba. Ta hada lipton ta sanya qaramin cokali a ciki ta koma kan kujerun falon ta zauna a daya daga ciki bayan ta kunna T.V da rimot din da ta dauka a kan hannun kujerar da take zaune. Hankalinta kwance tamkar bata san da wasu halittu a falon ba, bata sansu ba, kuma mai gidan wato Abdul bai fada mata zai yi baqi ba don haka bata yi shirin tarbarsu ba, a zuciyarta take rayawa tunda ta gansu a gidan a falo tabbas mai gidan yasan da zuwansu, zata iya yuwuwa ma shi ya kawo su lokacin da take barci, don haka kowa tasa ta fissheshi. Ta fada a zuciyarta gami da ta6e baki ta ci gaba da shan lipton din tana kallon T.V. Hidaya ce ta fara farfadowa daga suman ido biyun da tayi, sannan ta sanya hannu ta jijjiga Yasmin don dawo da ita cikin hayyacinta. “Wannan balarabiyar fa Yasmin? Ko qanwar Abdul ce don naga Familyn ku irin kyau ne” Kallo daya Yasmin tayi mata ta gane ita ce yarinyar da kamanninta suka qi 6acewa daga ma'adanar hotunan zuciyarta. Ita ce yarinyar da Abdul ya fara kalla da idanun So sa6anin ita da zasu yi aure tana gama makaranta. Ita ce yarinyar da taja mata zama a gida har na tsawon sati uku ba tareda ta leqa koda qofar gida ba. Ita ce yarinyar da ako wane lokaci ta samu dama zata iya hallaka har lahira saboda tsananin tsanar da tayi mata. Amma saboda tsabar wulaqanci Abdul ya rasa karuwar da zai kai har cikin gidanshi kuma kan gadonshi sai wannan mai kyan dan macijin? Yarinyar da kallo daya ta yi mata ta ji ta tsaneta tsana mai tsanani? Ashe saboda wannan karuwar ne dazu Abdul yake ta yi mata kwana kwana don kar taje gidanshi? “Lallai lokacin daukar fansa ta yazo" Ta fadi hakan a zuciyarta. Dukda wani sashi na zuciyarta na tunatar da ita karon battarsu da yarinyar a lokacin haduwarsu a plaza. 'Amma ai sarkin yawa ya fi sarkin qarfi.” Wani sashi daga zuciyarta ke qara mata qarfin gwiwa. Dan haka cike da tsana ta watsawa Aysha wani mugun kallo ta maida

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});