Chapter 4
Chapter 4
ka kwantar da hankalinka, duk yanda a ke ciki nan da kwana bakwai insha Allah zan tuntu6e ka.” Da haka ya baro garinsu Yola cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, a zuciyarshi yake jin qwarin gwiwar da bai ta6a ji ba a kan al’amarin Aysha. “Yarinyar da duk wannan aikin da ka ke bata san kana yi ba.” Inji wani 6angare na zuciyarshi. “Da sannu zata sani Insha Allahu.” Ya fada a fili don qarawa kanshi qwarin gwiwa tare da watsi da maganar da sashin zuciyarshi ta fara yi masa a kan Aysha. Wayar shi ya ciro daga aljihun rigar shi ya qurawa fuskarta idanu a zuciyarshi yana jinjina tsantsar kyau da kwarjini wanda Ubangiji ya halliceta da su. *** “Gidajen sayar da man fetur guda uku, gidajen haya guda uku, daya a Abuja, daya a Kaduna, daya a Kano, har da tsabar kudi Naira miliyan arba'in. Sai gidajen gona guda biyu a cikin garin Kaduna. Wadannan sune dukiyar Fatima da yake hannun Alhaji Musa, kada ku bari sai an kwana bakwai, ku koma gobe idan Allah ya kaimu da misalin qarfe biyu na rana. Duk wasu takardu da zasu tabbatar da mallakar dukiyar ga Fatima suna ajiye a Office dinshi, ya tura duk kudaden zuwaga account dinki Aysha. Allah ya ba da sa'a, ni da 'yar uwata muna muku fatan alkhairi." Saqon dana samu a wayata kenan daga 7777 don haka washe gari da qarfe biyu na rana a Office din Alhaji Musa ta yi mana. Ganinmu a daidai wannan lokacin ba qaramin fadar masa da gaba yayi ba, a niyyar shi sai gobe idan an kwana biyar saura kwanaki biyu kenan a wa'adin da na dibar masa zai sanar da hukuma. Duk da bayyi tunanin zanzo a daidai wannan lokacin ba yayi wa Masinjan shi kashaidi da jan kunne mai tsauri ba a kan ko mai kama da ni ya gani karya bari ta shigo Office dinshi. Ba zato ba tsammani sai ya ga mun turo qofa mun shigo mu uku ba tare da mun turo masinjan shi neman izini kamar yanda yake a qa’ida ba. Yau kam ba ni ce nai arresting dinshi da bindiga ba Safiyya da Rahma ne suka dora masa bindiga a saitin qwaqwalwar shi suna jiran umarnin sakin kunamar bindiga daga gare ni. kamar wancan lokacin ya daga hannu biyu sama cikin sallamawa. Ina zaune na dora qafa daya kan daya ina kallon yanda yake makyarkyata. “Ka yi mamakin ganin mu a daidai wannan lokacin ko?” Ban jira ya bani amsa ba na ci gaba da cewa, “Kwanakin dana dibar maka ne naga sunyi yawa saboda sanin da nayi komai da muke buqata yana ajiye a cikin ofishinnan, don haka minti goma na baka idan kana buqatar rayuwarka ka miko mana duk wata takarda da zata maida dukiyar fatima zuwa gare ta, idan kuma ka nemi yi min gardama zan cika alqawari na, na huda duk wani shashi na jikin ka da alburushi a yanzu- yanzun nan!” sannan mu dauki duk abinda muke bukata hankali kwance” Bai ja da nisa ba domin yana da tabbacin duk abinda kyakykyawar yarinyar mai kyan dan miciji a gurinshi ta fada zata iya aikatawa, domin duk abinda ya faru lokacin da suka kai hari gidan yari domin sace fatima yaji a redio kuma ya gani a T.v. Tsawon awa daya mukai a ofishin Alhaji Musa kafin ya gama tattaro komai yasa hannu a duk wata takarda da muke bukata, sannan ya tura kudaden zuwa cikin asusu na na banki, muna daf da ficewa na juya na kalleshi nace, “Aikin da ya rage maka shine ka sallami duk ma’aikata da masu hayar daka zuba akan dukiyar Fatima, idan kuwa kaqi ai’kata hakan na qara kawo maka ziyara a karo na uku... *kwafa nayi cikin salon jan kunne nace* Ka tabbatar harsashina ne zai shiga ta kunnenka na dama ya fita ta kunnan hagu, kaga daga wannan lokacin an shefe babinka a doran qasa” Ina gama fadin haka mika fice ba tare da mun sake kallonshi ba. Muna fita ya dora hannu a kai ya rushe da kuka tamkar mace, sai da yayi mai isarshi sannan ya fito don ganin ko a wane hali macinjan shi yake ciki? Yana kwance a sume a qasa war-was! A wannan halin ya tarar dashi. Qarfe biyar da rabi muna zaune muna hira a falo dukan mu “Gobe ya kamata Nafisa da Sadiya kuje ku bude wa Fatima account a banki” Da mamaki take kallo na, da yake duk abinda yake faruwa bata da masaniyya. “Account kuma? Ni da ba kudi gare ni ba me zanyi da account?” Ta tambaye ni tana zaro idanu. Da murmushi na kalleta, sannan na warware mata bayanin duk abinda ya faru, na kara da cewa “Shiyasa nace a bude miki account, domin in tura miki kudadenki kar in kashe in rasa hanyar biya.” Su Safiyya ne suka tuntsire da dariya, yayin da Fatima ta saka kuka tana sambatun fadin! “Ashe ina da wadannan makudan kudaden nake ta shan wahala a rayuwata? Ashe a kwai lokacin da zan mallaki Naira miliyan daya tawa ta kaina? Ubangiji Allah ya saka muku da alkhairi Aysha, Baba Jummala ki taya ni da godiya a gurinsu, sun yi mini komai a rayuwata bansan da me zan saka musu ba.” Tana kuka Aysha ta janyo takardun dukiyarta da suke ajiye tun dazu a gefenta ta miqa mata, amma ta kasa kar6a sai Baba Jummala ce ta amsa tana cigaba da rarrashinta. *** Suna zaune a dan tsurkin zaure a kan ‘yar qaramar tabarmar kaba da ya yi duqun duqun saboda rashin wanki, gaba dayansu sun zubawa qasar da take cikin wani faranti a gaban Malami ido, tun dazu yake zane yana sharewa su kuma sun zuba ido duk da ba fahimtar komai suke ba. Can ya dago kanshi yana kallonsu ya hada gumi kashir6an, ganin hakan ya fara fadarwa da Hajiya Maryam gaba. Domin tunda ta fada harkarsu ta masu neman jinsi wannan shine malaminta da take tsananin ji dashi, duk ayyukan da take kawo masa bai ta6a bata fad'i ba, shiyasa ko da gaddama taqi qarewa tsakaninta da Aminiyarta HAjiya Danasha a kan Aysha aljana ce ko bil’adama yasa ta dauko Danashar zuwa gurin mai gobe da nisa domin raba gardama, duk iya tsawon lokacin da ya dauka yana mata aiki bata ta6a ganin ya dauki tsawon lokaci irin wannan bai mata wani qarin bayani ba, kuma qarin fargabar shine yanda ya haxa zufa sharkaf shima wannan yanayin baqo ne a gurinta. Ajiyar zuciya ya sauke mai qarfi sannan ya dago yana raba idanu a kansu daya bayan daya. "Tabbas wannan yarinya da ku ke magana a kanta mutum ce! amma…” Fuskarta cike da fara’a take kallon Hajiya Mariya da sauri tace, “Daman na fada miki mutumce.” “Saurara Hajiya ki bari ya gama bayaninshi" Hajiya Mariya ta katse ta ba tare da ta saki fuskarta ba. “Malam muna jinka.” Ta fada tana kallon Malamin. Saida ya sauke ajiyar zuciya ya cigaba da cewa “Tabbas Mutumce amma a kwai wani babban al’amari a tattare da ita, tana da tsari a jikinta mai matuqar girma wanda zayyi wuya wani bil’adama ko aljani ya iya cutar da ita, ke Hajiya Mariya mun saba harka da ke
Table of Contents