Chapter 1
Chapter 1
A Dalilin DA NAMIJI 2 NA Shiru na yi ina kallon wani gefe tamkar ba dani take magana ba, ganin bani da niyyar amsa mata yasa ta koma mazauninta ta zauna sosai ta yi tagumi. Babu abinda take tunani illah miliyoyin da aka alqawarta mata, amma qiri-qiri ina neman yi mata buqulu. “Ya zama dole in 6ullo mata ta bayan gida, wallahi bata isa ta jamin asarar wadannan makudan kudaden ba.” Abinda ta fada kenan a zuciyarta, sannan ta fara qoqarin sakin fuskarta don kar inyi tunanin tana niyyar cutar dani. “Hajiya zan koma, tunda naga an gama bikin birth day din, Allah ya qaro miki shekaru masu albarka" Ina gama fadin haka na mika mata kyautar da na riko mata, wanda na nad'e shi a cikin leda, ban saurari godiyar da take shirin min ba na nufi hanyar ficewa daga gurin taron, karar tsinin takalminta da yake bada qara qas qas akan tiles din daya malale qasan gurin taron, ya tabbatar min da tana biye dani a baya. Ban waiga ba saida na isa jikin mota ta, abinda ya bani mamaki shine, ganin wasu mata har su shida bayan Hajiya Danasha sun iso gurin motar tawa. “Baby har zaki wuce?” wata Hajiya wacce taji kayan kudi hannu da qafa ta jefo min wannan tambayar, sai da na kalleta sama da qasa sannan nace “Eh” ciki ciki yanda bana tunanin taji amsar dana bata. “Kunsan wannan zuwan da ta yi ma tsananin sa’a naci, don haka karku damu, da sannu zumunci zai dore a tsakaninmu insha Allah" Hajiya Danasha ce ta musu wannan qarin bayanin tana kallon cikin idona, ban kalleta ba na bude motata na fada ciki ina qoqarin tayar da motar. Da sauri Hajiyar ta bude qofar mai zaman banza ta sakamin wata babbar jaka tana fadin "Aysha ki gaida gida, nagode qwarai.” Dan murmushi kawai nayi, sannan nace “Nima haka” Ina gama fadin haka naja motata na bar gurin a zuciyata ina tir da hali irinna Hajiya Danasha da qawayenta, tun a hanya na tsaya nayar da jakar da Hajiyar ta bani ba tareda na duba ko me da me aka zuba a ciki ba. Na isa gida qarfe goma sha daya da kwata na dare, shigata cikin falon naga duk sun saki ajiyar zuciya, sannan sun sauke tagumin da sukayi, dariya na tuntsire da ita daga bisani na ce, “Waye ya mutu a gidan namu?” Murmushin yaqe Baba Jummala ta yi sannan ta ce, “Alhamdulillah tunda kin dawo gida lafiya, da fatan babu abinda ya sameki ?” saida na isa kusa da ita na dafa kafafunta cikin murmushi na ce, “Babu abinda ya sameni Baba, kuma duk cikinsu babu wacce ta yi qoqarin cutar da ni, na je lafiya na dawo lafiya da taimakon addu’ar da kukemin ako da yaushe, so dukanku ku kwantar da hankalinku.” Da haka na samu suka saki ransu muka ci gaba da wata hirar daban. “Danasha wai ya kukai da ita?” “Hmmm! Kedai bari fulani, wallahi yarinyar nan tana da taurin kai fiye da yanda ki ke zato.” “Amma kin kwadaita mata irin miliyoyin kudin da zata samu?” “Qwarai kuwa, matsalar shine ita kanta yarinyar ba talaka ba ce, idan kikaga irin motocin da take hawa da yanda take kashe daloli zaki tabbatar da haka.” “Amma dai tana neman yimin buqulu, nifa har na gama tsara yanda zan tafi da ita gidana na Abuja taimin week’end, wallahi na kwadaitu da ita fiye da yanda kike tsammani" “Ki bari kawai Kumatu, wallahi tun ranar dana fara haduwa da ita a Mr. BiGS na kamu da tsananin sha’awarta, har mafarkinta nake yi idan ina barci, amma duk yanda naso janyo hankalinta taqi yarda dani, kuma abinda zai baku mamaki shine a rayuwarta ta tsani DA NAMIJI, shiyasa da farko nai tunanin bazan sha wahalar shawo kanta ba, amma a kwanakin baya dana matsa mata saida taimin wankin babban bargo na rashin mutunci" “Karki damu Danasha, ai ba ita ce yarinya ta farko mai tsananin taurin kai da muka fara haduwa da ita ba, kuma ba za ta zamo ta qarshe ba, kawai mika sunanta zamuyi da lambar motarta ai mana maganinta.” “Qwarai kuwa Hajiya Talatu, ni kaina shawarar dana yanke kenan da dazu da nai mata magana amma ta yi iskar kare dani.” “Wai anya kuwa yarinyar nan mutum ce?” “Me kike nufi Mariya, wannan ai ni ki ke nema ki ciwa mutunci ni dana kawo ta cikinmu.” “Ba haka bane Danasha, kin san kafin ki fara ba kowa labarinta a wannan qungiya ni kika fara bawa labarinta saboda kusancinmu, kuma ni na fara miki alqawarin miliyan biyu a kanta kafin ki samu masu yi miki qari a kan haka, tunda ki ka ji na fadi haka ina da dalili" “Mene dalilin naki Mariya, kada fa ki kushe min Baby a kan dalilin da bai taka kara ya karya ba" “Hmmm! Fulani kenan! dazu idan baku manta ba ina zaune a kusa da ita ne a high table, tsananin zumudi da sha’awarta yasa na kasa haquri na qara matsawa kusa da ita nace ya dai Baby ina fatan baki takura ba, tare da dora hannuna a kan cinyarta, wallahi shoking ne ya jani hannuna ya na sauka a kan cinyarta, ba shiri na sauke hannuna ina makyarkyata tareda hada zufa duk da sanyin A.C da ya wadaci gurin nan! Dana qara kallon fuskarta kuma sai naga fuskar wani mummunan gardi ya na min kashedi da dan yatsa, ba shiri na tashi daga gurin na koma cikin jama’a ina maida numfashi, ban sake marmarin kallon inda take ba har ta fice daga dakin taron nan" Dariyar da suka tuntsire da yasa ya kashe dan karamin Radion da ya yi recoding din maganganun nasu ya na tunani a zuciyarshi. Tun da qarfe takwas na safe kwamishinan ‘yan sanda ya ba D.P.O umarnin a tura ‘yan sanda suba matan da zasuyi taro a SHEHU USMAN KATSINA HOUSE tsaro, ya yi matuqar mamaki da ya samu labarin umarni ne daga sama, kuma shi ne Inspector da a ka daurawa alhakin kula da gurin. Samun labarin da ya yi na cewa wata ce zata gudanar da bikin birth day yaju zuciyar shi bai yarda da manyan matan ba. Don haka ba tareda sanin kowa a cikin jami’ansu ba ya maqala ‘yar qaramar abin daukar magana a cikin gurin taron, hankalin shi bai qara tashi ba saida yaga Aysha a gurin, a kan idanunshi duk motocin da suka halarci gurin manyan mata ne, ita kadaice yarinya qarama daya gani kuma abin mamaki uwar gayyar da kanta ta tare ta lokacin da ta isa gurin, a kan idanunshi ta fito domin tafiya, kuma yaga yawan matan da suka rako ta, don haka bai dauki abin recording din nashi ba saida duk matan suka watse lokacin qarfe sha biyu da minti arba’in da biyar, wannan tattaunawar kuma sunyi ne bayan tafiyar Aysha. “Innalillahi wa inna ilahi raji’un! Abinda ya ringa maimaitawa kenan ya na safa da marwa a tsakar dakin barcinshi. “Wacece Aysha???” Wannan shine tambayar da yake ta amsa kuwwa a qwaqwalwarshi, nan take ya dauko wayarshi ya bud'o hotunan daya dauke ta dazu ba tareda saninta ba, ta yi kyau matuqa fuskarta dauke da murmushin daya lura bai cika
Table of Contents