Chapter 11
Chapter 11
a gurin waccen motar da kuka nuna min” “Innan lillahi wa’innan ilaihir raji’un.” Abinda suke ta maimaitawa kenan har suka zauna a cikin motar da suka je neman su Aysha da ita. “Me kuka fahimta da bayanin da mai shagon can ya yi mana?” Nafisa ta tambaya tana kallonsu daya bayan daya. Siyama tace, “Kamar shi wannan mutumin yana tambaya ne a kan Sadiya don jiya baqar doguwar riga ta sanya, Aysha kuma ta sanya kananun kaya” Ta fadi hakan tana kallonsu don jin ko hasashenta dai dai ne. “Qwarai tunaninki hakane, amma abin dubawar shine miye hadin mutumin da Sadiya har yake tambayar ko anga inda ta shiga bayan ta fito daga gidan abincin? Kunga wannan maganar tana nuna ba a san in da Sadiya ta shiga ba. To idan hakane Aysha tana ina a wannan lokacin da abin ya faru? Miye hadin Aysha da wannan mutumin da har zai san Sadiya ta 6ata daga bakin Aysha? Me ya kaishi gurin motar dasu Aysha suka fita da ita? Waye ya kwashe kudi da takardun da suke cikin waccen motar? Ina Aysha ta shiga? Idan kuma tabi wannan mutumin ne mai zaisa ta bishi bayan duk irin tsanar da tayi wa ‘Ya‘ya Maza?” Rahma tace, “Ni wallahi kai na duk ya kulle, na rasa irin tunanin daya kamata inyi" Ta karasa fadin haka fuskarta na bayyana tsananin damuwa. “Ina ganin ya kamata mu koma gida, ko zamu samu nutsuwar yin tunanin abinda ya dace" Safiyya tayi wannan furuci tana kallon su baki daya. Sama Suhaila ta daga kanta tana mai fadin, “Ya Allah ka bamu ikon cinye wannan jarabawar da take tunkararmu” Baki dayansu suka amsa da "Amin" Nan take Siyama ta juya kan motar dan komawa gida. “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!” kalmar da Baba Jummala da Fatima suke ta maimaitawa kenan bayan Suhaila ta gama kora musu bayanin duk abinda suka ji kuma suka gani bayan fitarsu. Baba Jummala ta fara magana tana dubansu gaba daya “Abinda nake so ku fahimta kuma kusa a zauciyarku shine, tabbas Aysha tana nan a raye, kuma duk in da take muna zuciyarta, domin matuqar Aysha ta rasu to tabbas sai munji a jikinmu da zuciyarmu. Sadiya ce kawai bamu san tana raye ko ta mace ba, amma nasan matuqar Aysha tana raye sai tabi duk hanyar da ya kamata don ku6utar da Sadiya su dawo garemu a tare, duk in da Aysha take zata dawo garemu idan lokaci yayi, don haka daga yau ba zamu sake fita nemanta ba sai dai mu cigaba da yi mata addu’a” *** Yau Litinin wanda yayi daidai da kwanakin Aysha uku kenan a gidan Abdul-Ahad kuma a wannan ranar ce Abdul ya tabbatar mata zai fara binciken sanadin rasuwar Sadiya gadan gadan, don a wannan rana Sadiya ta cika kwanaki uku da rasuwa. Bayan gama binciken likitoci da shige da ficen da Abdul yayi ya samu aka bada gawar Sadiya don kaita makwancinta na gaskiya. Limamin masallacin da yake sallah ya samu ya yi masa bayanin komai har ya fahimce shi. Ba tare da wata matsala ba akai jana’izar Sadiya da taimakon Abdul da taimakon wannan Limamin. Aysha na sanye da sket na English wears daya daga cikin kayan da Abdul ya qara kawo mata ranar wata asabar, yana zaune a kan kushin yana shan tea cikin sauri, a lokacin agogo ya buga qarfe bakwai da kwata na safe. Sanye yake cikin kakinshi na ‘yan sanda wanda yai matuqar yi masa kyau. Aysha na zaune a qasa nesa kadan da inda yake zaune, tunda ta daga kai ta kalleshi sau daya bata sake kallonshi ba. Ba a yi minti biyu ba ta fara hamma saboda tsananin barci da take ji, kusan kwana ta yi tana kuka duk idanunta sun kumbura shi yasa bata son hada ido da shi. “Aysha?” Ya kira sunanta a sanyaye gami da katse mata tunanin da take yi. A sanyaye ta amsa da “Na’am!” ba tare da ta kalle shi ba “Ki dago kanki ki kalleni mana, magana mai muhimmanci nake so muyi" Ya fadi haka yana daga inda yake zaune. Bata dago kai ba kuma bata kalleshi ba illah sake kauda kanta gefe data sake yi. Har kusa da inda take zaune ya matsa ya sanya hannu ya dago fuskarta, idanunta a cikin nashi da sauri ya saki fuskarta yana fadin "Subhanallahi me yake damunki Aysha? kuka kikai a daren jiya ko?” Wani sabon hawaye ne ya gangaro a Idanunta tayi shiru ba tare da ta furta komai ba. “Oh My God menene ne haka? Ki fada mini damuwar ki mana?” Ya fadi hakan cikin tsawa yana zaro mata idanu. A tsorace ta dago ta kalleshi, cikin rawar murya ta ce, “Ni….Ni…Ni barci nake so nayi kuma barcin ya qi zuwa….saboda….saboda ban sha maganin da na ke sha…ba.." Da mamaki ya kalleta, sannan ya ce, “Kina nufin sai kinsha wani magani ki ke iya barci?” Kai kawai ta iya daga masa, alamar “Eh” Daki ya shiga da sauri ya fito da Memo da Biro ya miqo mata “Rubuta irin maganin da kike sha da duk wani abu da kike buqata in je in kawo miki.” Tafe Abdul yake a cikin mota cikin tsananin tashin hankali da sanyin jiki, me yake shirin gani ne? Aysha tana shaye shaye ne kenan? Kuma duk tsawon wadannan kwanaki ukun da tayi a gidanshi bata iya barci saboda rashin shan kayan maye? Hasbunallah wani’imal wakil. Wayarsa ya janyo ya kira Number Ardo bayan ya faka motar tashi a gefen titi, a hannunshi na hagu peper da Aysha ta rubuta masa irin maganin da zai siyo mata ne. “Hello Ardo ni fa ina cikin rudani a kan al’amarin wannan yarinyar, kaina yana neman bugawa…” Abinda ya fara gayawa Ardon kenan bayan sun gama gaisawa. Saida tsohon yayi dariya irin tasu ta manya sannan ya ce, “Na sani Modibbo, ka kwantar da hankalinka, kuma duk wani baqon al’amari da zaka gani a tattare da ita kada ka tsananta bincike, kai mata duk abinda take so, amma kada ka sake ka barta ta koma cikin ‘yan uwanta. Lokaci ya kusa da zaka samu duk wani amsar tambaya a kan rayuwar Aysha. Ka qara haquri har zuwa wannan lokacin.” Da haka suka yi sallama da Ardo bayan ya fada masa maganganu masu sanyi da kwantar da hankali. “Zan tafi Office Aysha. ki kwanta ki yi barci idan kinsha maganin, duk wani abu da kike da buqata ki duba kichen ko kan dining ko kuma Bed room suna nan. Yau ne zan ziyarci unguwar Zango, dan bincike na musamman a kan wadanda suka kashe Sadiya, buqatata kawai ki yi mini addu’a.” Tsawon minti biyu Aysha tana jan fasali kamar bazata tanka ba, shikuma har wannan lokacin bai gaji da tsugunno a gabanta ba. “Allah ya bada sa’a” Ta fada a gajarce, saboda lura da ta yi idan har ba ta amsa masa ba ba zai tafi inda za shi ba. “Lokaci yana qara tafiya fa" Ta fada a sanyaye sannan ta dago Fuskarta a hankali ga zube Idanunta cikin nashi. “Amin.” Ya amsa yana qoqarin kwaikwayon irin maganarta, yana ja da baya yana qoqarin ficewa daga falon ta sake juyo da fuskarta tana kallonshi, karaf suka hada
Table of Contents