Chapter 3
Chapter 3
sama ya kasa saukewa, don gani yake a ko wane lokaci ya sauke zaiji saukar bindiga a qwaqwalwarsa. “Ranka ya dad'e lafiya kuwa?” Masinjanshi ya maimaita tambayar a karo na biyu tare da qwanqwasa teburin gaban Alhajin da qarfi, firgigit ya yi tamkar wanda ya tashi daga barci, bai ce da masinjan komai ba ya dauki makullin motarshi da wayarshi ya nufi gida, hularshi ma a nan ya barta saboda tashin hankali. “To fa! Kome yake damun Oga? Da alamun wannan baquwar ta zo wa da Oga mummunan saqo. Allah ya kyauta….” Abinda masinjan ya fad'a a zuciyarshi kenan ya janyo qofar ofis din tare da sanya kulle kofar ta waje. “Ina fatan bai yi yunqurin bada matsala ba?” Nafisa ta tambayeni lokacin da muke tsakiyar gow slow bayan dawowarmu daga Office din Alhaji Musa kawun Fatima. “Ba a yanzu ne zan san haka ba sai kwanakin da na bashi sun cika ba tare da ya aiwatar da abinda na umarceshi ba” Na amsa mata kai tsaye, idanuna yana kan titi. “Bana tunanin zai bada wata matsala, domin shi kanshi ya san ba dukiyarshi ba ne, kuma idan ya miqa dukiyar ga mai ita ai an sauke mishi nauyi ne.” Nafisa ta fadi haka tana qoqarin sakawa motar da take gefenmu signal domin ta daga mana qafa mu shiga gabanta. “A ganin ki kenan ko? Idan ya na tunanin haka meyasa tun da can bai miqa dukiyar ga Fatima ba?” “Kuma fa hakane.” Ta fadi haka tana gyada kai cikin gamsuwa. “Mutane akwai su da son kudi, don haka basu da damu da ko wace hanya zasu bi don samun kudin ba, su dai kawai suyi mugun kudi, a kirasu masu kudi….” Karaf idanu na a cikin nashi, ashe shine mai motar gefenmu, dauke kai nayi ba tare da na sake kallon inda yake ba, amma a jikina ina jin har a lokacin da ya daga mana qafa muka shiga gabanshi ni yake kallo. “Dan sandan nan ne.” Na fada a zuciyata, ina tunanin haduwarmu dashi kwanaki uku da suka wuce a bikin birth day din Hajiya Danasha. *** Tsananin damuwa da tashin hankalin da yake ciki shiya hana shi ganin rama da bak'in da babban aminin shi Alhaji Muhammd ya yi. Sama sama suka gaisa ya fara kora masa bayanin yanda sukai da yarinyar da ta ziyarci Office dinshi dazu da rana. Bai katse shi ba sai da ya lura ya gama fadin abinda ya kawo shi sannan ya saukar da ajiyar zuciya ya fara da cewa. “Nifa Alhaji banga wani abin tashin hankali a wannan maganar ba, lokaci yayi da ya kamata ka tsakarke dukiyarka, idan har zan ba ka shawara ka ji ya kamata ka tattara duk dukiyar da kasan ta Fatima ce ka damqa mata, sannan ka qara da roqonta gafara. Ni yanzu da ka ganni na gane kuskure na, a kullum addu’a na ke Allah ya hada ni da Fatima in roqi gafara a gareta, domin Allah ya bayyana min duk wani abu da yake 6oye wanda ban sa ni ba, shi yasa nake bin duk wanda na san na cuta ina mayar masa da haqqinshi tare da roqon gafara….” Baki bude yake kallon shi tunda ya ji ya fara wadannan maganganun masu kama da soki burutsu. “Alhaji kasan me ka ke fada kuwa? In ba Fatima dukiyarta fa ya na nufin rasa biyu daga cikin uku na dukiyata.” “Qwarai nasan da haka, domin miqa mata dukiyar tata shine samun kwanciyar hankali a gareka a nan duniya da ranar gobe qiyama.” “Gaskiya bazan iya ba, yanda na saba da juya naira bazai yuwu lokaci daya in koma mai rufin asiri ba.” Ya fada cike da tsananin damuwa yana jujjuya kai. “To me ka ke tunanin za ka yi? yaran nan tunda suka fasa gidan prison su ka fitar da Fatima ba qaramin shiri suke da shi ba.” “Duk shirinsu ai hukuma tasha gabansu, don haka zanje in samu hukuma tun kafin kwanakin da suka d'iba min ya cika.” “Ka manta kashaidin da tayi maka kenan?” Alhaji Muhammad Abban Nasir ya fada yana mamakin tsaninin san zuciya da taurin kai irin na aminin nashi. “Sam ban manta ba, amma ba zan iya miqa musu duk dukiyar nan ba, dole in dauki mataki don kare kaina.” “Wallahi ba zaka ta6a samun nasara ba, tunda ba a kan gaskiya ka ke ba.” Alhaji Muhammad ya fad'a ranshi a 6ace. “Fatan da kake min kenan?” Alhaji Musa ya tambaya yana kallon aminin nashi a fusace. "Ba mugun fata na ke maka ba, illah gaskiya da nake fada maka kuma wannan shi ne aminci na gaskiya.” Alhaji Muhammad ya fada cikin sigar rarrashi da kwantar da hankali. “Ka riqe gaskiyar ta ka, ina tabbatar maka ni zan yi Nasara a wannan karon battar tamu, kana zaune zaka samu labarin an damqe ‘yan bindigan da suka fasa gidan yarin mata, tare da mai laifin da suka sace” “Idan kuwa hakan ya faru ni da kaina zan sake shigar da qara in wanke Fatima daga zargin da a ke mata tare da tabbatar wa kotu cewa d'ana ne yai qoqarin keta ma ta haddi ita kuma ta kare kanta” Tsaki mai qarfi Alh Musa yaja sannan ya mike a fusace ya nufi hanyar ficewa daga falon baqin na Alhaji Muhammad ba tare da ya qara tankawa ba. “Allah yaba mai gaskiya sa’a” Kalmar qarshe da Alhaji Muhammad din ya rakashi da ita kenan.! **** **** Zaman da sukai a kan Capet kusa da kusa su na fuskantar juna shi zai tabbatar akwai shaquwa da qauna mai tsanani tsakanin shi da dattijon. A hankali kuma cikin nutsuwa ya gama warware masa duk abinda yake tafe da shi, sa’an nan ya qara da nuna masa hoton ta wanda ya mamaye gaba daya fuskar wayarshi. Tsawon minti biyu yana kallon hoton. "Lallai ta na da tsananin kyau, kuma ta cancanci ta ja hankalin Modibbo" ( ya kirashi da sunan da shi kad'ai yake fad'a masa a duk Familyn su) Murmushi Abdul ya yi, sannan ya gyara zama yana sosa kai ya ce, “Ba haka ba ne Ardo, wani ne abu yake fisgar hankali na a duk lokacin da na dubi qwayar idanunta, hakan shi yasa na dangano ga kakana duk da muna tsaka da aiki” “Bani da sani sai abinda Allah ya sanar dani Modibbo, ka koma gurin ai kinka, kuma ka kwantar da hankalinka, zan yi istahara na kwana bakwai kamar yanda Manzon Allah (S.A.W) ya koyar damu, duk abinda a ke ciki zan tuntu6e ka ta waya, kai ma sai ka ci gaba da addu’a.” “Addu’a a kullum cikinta na ke Ardo, kuma kada ka manta…” Yayi shiru ya na sosa qeya tare da sunkuyar da kanshi qasa cikin kunya, ya kasa karasa maganar da yai niyyar fad'a. Sai da tsohon ya yi dariya sannan ya bugi kafadar Abdul din ya ce, “Oh! yau a karo na farko Modibbo ya na jin kunyata a kan wannan kyakyakyawar yarinyar, kada in manta da me?” A kunya ce ya bud'e baki yace “Da hajiyoyin da suka yi alqawarin bin duk hanyar da za ta kaisu ga ci domin gur6ata ma ta rayuwa…” “Karka damu! ba za su iya cutar da ita ba da izinin Ubangiji,
Table of Contents