Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

A Dalilin Da Namiji Book 2 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kuma babu wani aiki da kika ta6a kawomin wanda baki samu nasara a kanshi ba, don haka bazan 6oye miki ba, wannan yarinya duk wani malami na duniya da ya ce zai miki aiki a kanta qarya yake yi, don haka zaifi kyau ku haqura, domin idan kun matsa a kan a cutar da ita to tabbas aikin zai juye a kanku” Da wannan bayanin suka fita daga gurin Mai gobe da Nisa, amma da alama Danasha bata saduda ba, domin babu alamar sanyin jiki ko kadan a tattare da ita. Abinda ta dauka a zuciyarta kawai Hajiya Mariya sun hada baki da Malaminta don su yi mata wayau akan Aysha, don haka a gobe zata fara ziyartar nata malaman har sai ta cimma biyan buqatarta a kan Aysha. Yau tunda ta tashi da asuba take jin jikinta a wani irin yanayi wanda sam bata ta6a tsintar kanta a cikin irin wannan yanayi ba, jikinta a sanyaye yake matuqa, ko falo ta kasa fita har agogo ya buga qarfe goma sha biyu na rana, tana jin hayaniyar su Safiyya a falo amma sam ta kasa fita, haka kawai ta ji qirjinta yana bigawa, don haka ta cigaba da fadin “Inna lillahi wa inna ilaihirraji’un” Bata sauka daga kan gado ba saida ta daidaici lokacin sallah azahar ya yi, wanka ta fara yi sannan ta yi alwala, tana fitowa daga bandaki wayarta ta qwala kiran sallar azahar. Sai da ta idar da sallah sannan ta zura doguwar riga ko mai bata shafa ba balle powder ta nufi falo. “Aysha lafiya kike kuwa.” Tambayar da Baba Jummala ta jefo mata kenan lokacin da ta gaisheta sama - sama ta kwanta a kan doguwar kujera, shiru ta yi kamar bazata amsa ba tsawon minti uku sannan ta ce, “Kawai jikina ne ba dad'i sosai, amma karku damu.” Daga haka bata qara tankawa ba da qyar ta amsa gaisuwar da ‘yan uwanta suka yi mata. “Ya kamata ki daina kwanciyar nan haka ki tashi ki zauna ko ruwan Lipton in hado miki kisha.” Rahma ta furta hakan lokacin da agogo ya buga qarfe biyu da rabi na rana. A hakali ta bude idanunta da suka fara canza launi daga farare kar zuwa jajaye, Baba Jummala ta kalla tace, “Baba yau kada ki yi girki da daddare, zamu fita mu yi take away.” Maganar bata ba ta mamaki ba domin a wasu lokutan sukan yi irin haka, duk kansu suke fita da yamma zuwa gidan abinci don cin abinda ransu yake so. Baba ce kawai take zamanta a gida sai dai ta fadi abinda take so su taho mata dashi. “To na ji, amma maganar Rahma abin dubawa ce, ya kamata kisa wani abu a cikinki domin zai taimaka miki ki samu qarfi a jikinki. “Nagode! amma bana jin zan iya cin komai.” Ta fada idanunta a rufe kuma bata tashi daga kwanciyar da ta yi ba. “Ko asibiti za’a kaiki?” Fatima ta fadi idanunta suna kanta, fuskarta dauke da damuwa. “Ka da ku damu, nifa lafiyata qalau. Amma…Bana son hayaniya, ku barni na huta don Allah.” Ta katse Safiyya data fara magana cikin marairaicewa. Qarfe bakwai na yamma bayan sun idar da sallar Magariba tana zaune a kan darduma a falo da casbaha, a hannunta tana ja ta kalli Sadiya ta ce, “Kishirya yanzu mu fita zuwa gidan abinci, ko wacce ta yi list din abinda take so, yau ba zamu fita gaba daya ba.” Tana gama fadin haka ta nufi dakinta ba tare data sake kallon ko daya daga cikinsu ba. Yau shine karo na farko data umarci suyi list ba dukansu za su fita ba. Da madaukakiyar mamaki Baba Jummala ta bita da kallo harta qurewa ganinta, don haka sai ta maida kallonta zuwaga Rahma tace “Gaskiyta a kwai matsala a tare da Aysha, ban ta6a ganinta cikin irin wannan yanayin ba tunda nake tare da ita, Allah dai yasa ba wani mummunan abu ne yake shirin faruwa ba.” "Amin summa Amin, ni kaina al’amarin ya fara daure mini kai Baba, ban ta6a ganinta a cikin irin wannan yanayin ba.” Rahma ta amsa tare da zabga tagumi hannu bibbiyu. “Yanda idanun Aysha suka juye daga farare zuwa jajaye kadai ya isa ya tabbatar bata da lafiya.” “Nima na fahimci haka, amma ta ce lafiyarta qalau.” Siyama ta fadi hakan fuskarta dauke da damuwa. “Qila yanayin jikinta ne kawai ya canza kamar yanda ta fada, kunsan a kwai yanayin yau da gobe, dole Ubangiji ya jarabci bayinsa.” In ji Suhaila. “Qwarai kuwa, zancen ki gasikya ne.” in ji Nafisa. “Allah ya bata lafiya, amma yanayin sam bai dace da ita ba.” Fatima ta fadi haka, sannan ta kwa6e fuska kamar zatai kuka. “Ka da ku damu zata dawo dai dai in Allah ya yarda, canjin yanayi ne kawai.” Baba Jummala ce ta fadi haka a daidai lokacin data sako kanta cikin falon, watsa idanu ta yi a kansu bataga Sadiya ba, hakan ya tabbatar mata tana can waje tana tada motar da zasu fita da ita. “Ina fatan kun bada list din abinda kuke so gurin Sady?" Ta tambaya tana kallon Fatima. “Eh yana gurinta.” Ta amsa mata tana kallonta cikin kulawa. “Baba Jummala sai mun dawo, ki yi mana addu’a…” Ta fada ba tare da ta kalleta ba ta nufi matattakalar da zata sada ta da harabar gidan. “Allah ya dawo mana daku lafiya, Ubangiji Allah ya tsareku Aysha…” kadan daga cikin addu’o’in data jiyo muryar Baba Jummala tana jero masu kenan, a zuciyarta ta amsa da “Amin.” Duk ‘yan matan suna tsaye a harabar gidan suna jero musu addu’ar dawo wa lafiya har motarsu ta fice daga harabar gidan suna daga musu hannu. ***** Minti daya da zuwansu a kan kujerun gurin cin abincin service din gidan ta iso garesu, abinda take buqata ta sanar da ita sannan Sadiya ma ta fadi abinda take da buqata. “Oh My God, Sadiya na manta da wayoyina a mota, pls kwaso min. Sannan ki bude aljihun motar ki debo kudaden da kike tunanin zasu ishemu" Nan take ta dauki mukullin motar domin ta cika umarninta, tana wucewa ta sanya hannu biyu ta dafe kanta tare da lumshe idanun ta. Tunda suka shiga gurin idanun maza da matan gurin ya koma kansu, basu zauna a cikin jama’a ba daki na musamman suka nufa don haka a ka bisu da idanu. Yana daya daga cikin wadanda suka bisu da kallo har suka shige cikin dakin, haushi ya cika masa zuciya ganin har suka qulewa ganin jama’a wasu daga cikin mazan gurin basu daina kallon hanyar da suka bi ba. Kamar kullum yau ma tana sanye da irin shigar da yake yawan ganinta da ita ta kayan turawa, sanye take da wani wando kalar peank wanda ya amshi kalar fatar jikinta, wandon mai fadi ne amma wannan baisa ya boye ainihin shape din mazaunanta ba, rigar ce ta yi matuqar kama jikinta, wanda ya fito da shatin damammen cikinta da dukiyar fulaninta da suke tsaye qyam masu matuqar jan hankali, ta yi kyau fiye da yanda ake zato, kallo daya ya yi mata jikinshi ya bashi bata jin dadi, domin idanunta sun dan canza launi duk da cewa dare ne. Ganin abokiyar tafiyarta ta fito yasa ya

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});