Chapter 2
Chapter 2
vacewa daga fuskarta ba. Yanda ya kusanto da hoton kafin ya dauke ta yasa tamkar ya kirata ta amsa. “Me suke niyyar yi mata don su samu biyan buqatarsu na maida ita ‘yar qungiyarsu na ma’abota neman jinsi?” Nan take ya fara addu’ar Allah ya tsare mishi ita a zuciyar shi, a wannan dare idan ya ce yayi barci to tabbas ya yi qarya domin bayan ya gama tunani alwala ya dauro ya fara jera nafilfili ya na roqar mata kariyar Ubangiji a duk inda take. “Ya zama dole insan matakin da zan dauka tun kafin wankin hula ya kaini dare” Ya fada a zuciyar shi lokacin da yake hanyar dawo wa daga masallaci sallar asubahi. *** Yau kwana goma kenan cif daya samu labarin wasu ‘yan bindiga mata sun sace Fatima daga gidan yari, hankalinshi yayi mummunan tashi, domin ya na ganin bai cika alqawarin daya daukarwa gawar danshi Nasir ba, babban burin mahaifin Nasir Fatima ta fuskanci hukunci a kan zaluncin data aikata, dauwamarta a gidan yari a matsayin hukuncin daurin rai da rai shine daukar fansar rayuwar danshi Nasir. Don haka ne yasa a kullum sai ya ziyarci ofishin yan sanda don jin ko an samu wani qarin bayani a kan Fatima da wadanda suka sace ta, amma har yau babu labari, daga qarshe ma sai yan sanda suka fara yi mishi hanya hanya da cewa ya saurara da zuwa ofishin na su idan suka samu wani qarin bayani daga ‘yan sandan ciki zasu sanar dashi har gida tunda sunada adreshinshi. Yayi kukan baqin ciki sosai, ko a mutuwar Nasir baiyi irin wannan kuka ba, ita kuwa mahaifiyar Nasir bata zafafa a kan al`amarin ba, illah cewar data yi ta bar komai a gurin Ubangiji. Ya samu malamai suna mishi addu’a a kan Allah ya bayyana ta don tabbatar da hukuncin alqali a kanta, shima a ko wace sallah tashi baya gajiyawa gurin roqon Allah ya tona asirin inda Fatima ta shiga da asirin wadanda suka sace ta. Yana cikin tashin hankali matuqa, domin a cikin kwanaki biyun nan sam ba ya samun wadataccen barci, mafarki yake da margayi a cikin wani mummunan yanayi. Nasir din yayi baqi ya fita daga hayyacinshi, wuta ce take cin farin likafanin jikinshi fatarshi ta yi baqin qirin. Yana ihu da kuka yake fadin “Daddy ka jefani a cikin uquba da bala’I…. ka nemi Fatima ka roqa min yafiyar ta ko zan samu sassaucin azabar da na ke ciki…” Maganganun da d'an nashi yake fada mishi kenan a duk mafarkin da zaiyi dashi. Hankalinshi a tashe ya ziyarci limamin masallacin unguwar su yana sanar dashi halin da yake ciki. Kwanaki uku liman din ya buqaci ya bashi domin yin istahara kamar yanda Manzon Allah S.A.W ya koyar damu. Bayan cikan kwanaki uku ya koma gurinshi, zaune a gaban malamin yana saurarar bayanin da yake mishi. “Dan ka yana cikin wani irin mugun yanayi kamar yadda Allah ya fahimtar dani, haka shi ya tabbatar min da waccan yarinya da kake fadin ita ce silar mutuwar danka sam bata da haqqi a kanshi, kuma shi yaron na ka bai kasance mai aikata ayyukan alkhari ba a duniya, don haka duk inda wannan yarinya ta shiga zaifi kyau ka nemo ta domin roqarma danka yafiya a gareta ko zai samu sassauci a halin da yake ciki, kuma ka ji6anci ba da sadaqa a na roqar mishi yafiya a gurin Ubangiji, kuma ka dage da addu’ar Allah ya yafe mishi da kai da duk wani wanda ya zalunci wannan yarinya" Da wannan bayanin ya bar gurin Malam jikinshi a sanyaye, bai 6oye wa mahaifiyar Nasir komai ba a kan abinda Malamin ya sanar dashi, kuma baiyi sanya ba gurin aikata shawarar da Malam ya bashi. A kullum mahaifiyar Nasir ta na dafa abinci mai yawa a kai makarantu na almajirai a na rabawa sadaqa a na addu’ar Allah ya gafartawa Nasir, ya bayyana Fatima. *** Ya na zaune a tanqameman Office dinshi yana shan A.C masinja yake sanar dashi yana da baquwa, yayi matuqar mamaki jin cewa mace ce baquwar tashi, a saninshi bashi da ajenda da wata mace a ranar yau sai dai da yake shi din mai jama’a ne sai ya kauda mamakin da yake, yayi Umarnin a shigo da ita. Numfashinsa ne ya kusa dauke wa don ganin kyakykyawar budurwar da ta kasance baquwar tashi. Ina shiga Office din na maida qofar na rufe tare da sanya key ta ciki na kulle na zare makullin na saka a aljihun wando na. Da rausaya na karasa kujerar gaban teburinshi na zauna, sannan na dora kafa daya kan daya ina kallon yanda a ka qawata ciki da waje na Ofis din amma da dukiyar haram. Tunda a ka sanar dashi zuwana yake mamaki, da ganin shigowa ta irin kyan da nake dauke dashi da shigar da nayi na riga da wando sun fitar da ainihin surar jikina duk mamaki suke bashi, ganin na rufe qofar tare da zare dan key din shine abu mafi mamaki a tare da ni. Ban ce komai ba tsawon minti biyu illah wurga lumsassun idanu na da nake yi daga wannan kusurwa zuwa wancan kusurwa. “Yan mata lafiya dai ko?” Ya katse shirun daya ratsa tsakaninmu don ganin bani da niyyar magana. Tsawon daqiqa talatin ina jan fasali kamar bazan tanka ba, daga bisani na watsa idanuwa na a kanshi tare da fadin. “Alhaji Musa koh?” Sai da ya sauke ajiyar zuciya jin tattausar muryata sannan yace, “Qwarai kuwa ni ne, me yake tafe dake?” Numfashinshi ne ya tsaya cak na wasu ‘yan daqiqu ganin bakin bindigar da nayi arresting dinshi da ita, nan take ya daga hannuwa sama, duk jikinshi ba inda ba ya kyarma, tsananin tsorata ya hanashi furta komai. “Ka san me ya kawo ni gurinka a daidai wannan lokacin?” Na tambaye shi har a wannan lokaci ban janye bindigar daga kanshi ba. “A’a… Don Allah karki kashe ni, duk abinda ki ke so zan baki.” Ya fada bakinshi na rawa da alamun miqa wuya. “Good! gara da kai tunanin zan iya fasa qwaqwalwar ka idan kai qoqarin yi min gardama, na san kana da labarin ‘yan bindiga mata da suka shiga gidan yari suka sace Fatima, kuma nasan kaga yanda muka yi da masu gadin duk da dai bamu kashe ko maigadi daya ba. Ba wani abu ya kawo ni gurinka ba illah buqatar dukiyar gadon Fatima da yake gurinka, nasan komai a kan dukiyar ta da yake hannun ka wanda dan uwanka ya mutu ya bar mata, ka dad'e kana shanawa da dukiyar da ba taka ba, don haka lokaci yayi da zaka miqa komai ga mamallakinta kaima ka huta. Sati daya na baka ka gama tattara komai zan dawo in amsa, kuskure daya da za kai shine ka yi qoqarin yi min taurin kai ko kuma ka shigo da hukuma cikin al’amarin, idan kai haka zamu kar6ii dukiyar ta qarfi sannan in huda ko wane sashe na jikinka da alburushi, idan kunne ya ji…” Ina gama fadin haka na maida bindigar aljihun wando na sannan na bud'e qofar na fice ba tare da na qara kallonshi ba. Tsawon minti talatin baisan ina kanshi yake ba, har a wannan lokacin hannunshi yana d'age a
Table of Contents