Chapter 10
Chapter 10
ne in koma cikin ‘yan uwana, domin samun qwarin gwiwar aikatawa wadanda sukai mana wannan zalauncin abinda ya dace da su" “Kun zama hukuma kenan?” Abdul ya fada hankalin shi kwance cikin rashin damuwa da duk abinda ta fad'a. “Hukumar banza, hukumar wofi…ai mu munfi hukuma, domin ba wanda ya isa ya hana mu aikata abinda muka so kuma a lokacin da muka so…” “To! Ai ban hana ki tafiya ba, ko na daure ki ne?bismilla ga hanya nan.!” Ya fada yana nuna mata kofar fita, sannan ya maida hankalin shi ga danna remot din TV. Cikin fushi da karin tsananin bakin ciki ta sake cewa “Wai ana dole ne a rayuwa? bana sonka, ko soyayya dole ce? Ka bani wayoyi na mana kaga in ban bar maka gidanka ba” Kallonta ya sake yi sama da kasa, cikin fada shima yace “Ya zama dole ki zauna da ni, kuma ki so ni, ke karya kike yi ma kice ko kadan bakya so na, ni ba irin namijin da ake k'i bane” Yaraf ta zauna a kan kushin, rashin abin cewa yasa ta fashe mishi da kuka mai tsananin karfi. Tashi yayi ya nufi wata hanya a cikin falon da bata san ko ina zata 6ille ba, can sai gashi ya dawo da cofin ruwa a hannun shi ya nufo gurin da take zaune tana kuka, kallonta kawai yayi, da sanyin murya yace “Yi haquri ki sha ruwan sanyi sai muyi magana ta fahimta” Da farko Aysha qin amsar ruwan tayi, sai da taga ya nufo bakinta gadan-gadan da kofin ruwan sannan ta kar6a a fusace ta sha, bata a jiye kofin ba saida ta shanye ruwan gaba daya. A hankali sanyi ke kwarara a cikin zuciyarta da duk sassan jikinta, wata nutsuwa ke kwarara a ruhinta, shiru tayi ta jingina bayanta da jikin kujera gami da lumshe idanun ta. “Me yasa kake neman zamowa mai qarfi a kaina ne? me yasa kake samun nasarar ta6a jikina bayan babu 'Da namijin daya ta6a samun nasarar haka? Me yasa kake neman canza min aqida ta ne? me yasa kake neman juya min alqibla ta ne? me yasa kake neman….” Da sauri yace, "Saurara Aysha ki saurare ni don Allah, duk wadan nan tambayoyi maki amsarsu guda daya ce, saboda soyayyar gaskiya nake yi miki, kuma sam bani da niyyar cutar dake, nine wanda Ubangiji ya turo don kawo qarshen matsalolinki, ki bani dama sau daya kawai Aysha, ki bani damar zamo wa mai share miki hawayenki. Wallahi bazan ta6a baki kunya ba, zan tsaya a kan al’amarin mutuwar Sadiya kamar yanda zan tsaya a kan mutuwar qanwata, ki bani dama don girman Allah. idan kin amshi roqona daga yau bana buqatar ki sake musanta umarni na, ina sane da al’amarin ‘yan uwanki. Kuma zaki koma garesu amma ba yau ba, kin amince da duk abinda nace?” Ya karasa da tambayar yana kallon cikin idanunta. Kallon kallo suka rinqa yiwa junansu har na tsawon mintina goma, qoqari take ta gano gaskiyar maganganun da ya yi mata, yayinda shi kuma Abdul din yake qoqarin tabbatar mata da abinda ya fada gaskiya ne har zuciyarsa. Bata san mai yasa zuciyarta take saurin karaya da amincewa Abdul ba, ada babu wani Namiji daya isa ya nuna mata yatsa ba tare da ta karya ba, amma a kan Abdul-Ahad zuciyarta da gangar jikinta masu rauni ne. Kai kawai Aysha ta daga wa Abdul din alamun ta yarda da maganganunsa ganin da ta yi har a wannan lokacin jiran amincewarta yake yi. Murmushi yayi fuskarsa na bayyana tsantsar jin dadi da amincewar da tayi dashi. Yace, “Me kike son ci don kar in kawo miki abinda zuciyarki bata so?" Murmushi kawai Aysha ta yi don ta gane yana tsoron ta sake yi masa amai irin na dazu ta ce, “Duk abinda ka kawo zanci, ba baquwar zafi bace.” Ajiyar zuciya Abdul ya sauke mai qarfi gami da zuba mata idanu kamar zai hadiyeta. A kunyace ta miqe zuwa cikin bedroom har tana hardewa da qafafunta sabo da kallon qurilla da yake binta dashi. Minti biyar da shigarta dakin ta ji alamun ficewarshi daga gidan. *** Tunda suka ga qarfe biyu na dare ya yi Aysha da Sadiya basu dawo ba hankalinsu yayi mummunar tashi, a wannan rana babu wacce tayi barci a gidan suna zaune jigum jigum a falo da casbaha a hannayensu suna ja, domin tabbas sunsan babu lafiya. Baba Jummala tana zaune a kan darduma bayan ta idar da nafilfili, ta dad'e tana adduo’I a cikin sujjadarta tana roqon Allah ya tsaresu Aysha a duk halin da suke ciki. Fatima kam tana jan carbi tana hawaye, a fili take addu’ar kada Allah yasa wani mumunan abu ne ya faru dasu, idan wani abu ne ya samu su Aysha ya zasuyi? Tun a cikin daren Safiyya da Rahma suka fara tunanin ko zasu fita don bin bayansu. Baba jummala ta ce, “A yanzu bamu da tabbacin a wane hali suke ciki, amma mu jira idan gari ya waye zuwa qarfe goma na safe idan basu dawo ba sai abi bayan su" Suhaila ta ce, “Amma fa Baba Jummala idan kika duba irin haka bata ta6a faruwa ba.” Safiyya tace, “Hakane Suhaila, amma bari mu jira zuwa safiyar kamar yanda Baba ta yi umarni" Har gari ya waye babu wani labari a kan rashin ganin Aysha da Sadiya, kuma tsananin damuwa ta hana su kunna T.V balle su san halin da ake ciki. Da ruwan tea da burodi kawai suka iya karyawa domin damuwa da tunani ya hana Baba Jummala shiga kiching, ruwan shayin ma sai Safiyya ce ta dora. Qarfe goma dai dai suka gama shiryawa don shiga cikin garin Kaduna da niyyar bin kowane gidan cin abinci dasu Aysha suka ta6a zuwa. Har qarfe hudu na yamma basu samu inda su Aysha suke ba, sai daga qarshe suka yi tunanin su je BBQ, gidan wani abinci ne da yake tashe a garin Kaduna. Suna zuwa gurin suka yi fakin da motocinsu, basu shiga ciki ba sai da suka fara duba motocin da suka yi fakin a gurin, daya bayan daya, da tsananin mamaki suke kallon motar su Aysha. Rahma ta ce, “Ai a bude take” Ta fada da sauri bayan ta kama qofar mai zama kusa da Driver taga ya bude, amma duk wani muhimmin abu an kwashe. “Da ganin yanda aka bar motar nan a bude babu lafiya” Safiyya ce ta fadi haka bayan sun gama duba ko ina a cikin motar. Suka maida motar suka rufe gami da kutsa kansu cikin gidan abincin. Duk iya binciken da ya kamata suyi sunyi, amma sam basu ga alamarsu Aysha ba. Hankalinsu ya qara tashi suka fito daga ciki suna tunanin abinda ya kamata suyi na gaba. Gurin mai sai da ice cream suka nufa suna tambayarsa ko yaga masu motar can tun jiya da daddare? Mai shagon ya amsa da “A’a amma dai har na kulle shagona jiya da daddare misalin sha biyu na bar waccen motar tana nan da kuma wani mutum da ya tambayeni ko naga wata yarinya ta sanya doguwar riga ta wuce ta nan, tunda na amsa masa ban ganta ba ya bar gurin nan amma har na tashi yana nan tsaye
Table of Contents