Chapter 7
Chapter 7
yake tafiya yana kallonta har ya fice daga dakin yayin da ita kuma take watsa mishi harara tana huci har ya 6ace wa ganin ta. Tana zaune a inda ya barta har ya dawo daga masallaci, da sallama ya shigo cikin dakin! sanin daraja da ladan da yake tattare da amsa sallama yasa ta amsa masa a ciki ciki, don bata tunanin ya ji abinda tace. Har ya nemi gurin ya zauna daga can gefan gadon bata fasa kallon shi tana watsa masa harara ba. “Idan kika daure fuska qara kyau kike yi, idan kika harareni wani sanyi da farin ciki ne ke kwarara a cikin zuciyata, don Allah ki ciga ba da harara ta.” Ya fadi hakan murya kasa kasa yana watso mata murmushi. Tabe baki tayi tana kallon shi haushin shi yana qara cika mata zuciya. “Ina ‘yar uwata Sady?” Shiru yayi na ‘yan mintuna ba tare da ya bata amsata ba, har sai da ta sake maimaita masa cikin daga murya. “Kwantar da hankalinki Aysha, Sadiya tana cikin qoshin lafiya da yaddar Allah. idan anjima gari ya waye zan dauke ki muje gurinta.” Hayayyako masa tayi da masifa tana cewa “Menene nufinka da ka dauko ni zuwa nan ko an faxa maka a daji nake kwana? Kai wai ma miye gami na da kai?.” “Allah ya baki haquri. gani na yi baki da lafiya, a tunanina zanyi gwaninta idan har na taimaka miki" “To ba kai gwaninta ba, kuma ban gode ba. Har abada bazaka ta6a yin abinda zanji ka min gwaninta ba" Ta fada tana murguda mishi baki, gabas da yamma. “Da yake daman can ba don ke na yi ba, na yi ne don Allah kuma don masoyiya ta. Ya fadi haka idanunshi na kanta don jin amsar da zata bashi. “Masoyiya? Wace ce masoyiyar taka?” Ta watsa masa tambayar tana kallonshi da madaukakiyar mamaki a fuskarta. “Aysha Azzahara’u ce masoyiyar tawa, tsananin son da nake mata yasa bazan ganta a cikin wani mawuyacin hali na kasa taimaka mata ba, ko da kuwa da zan rasa rayuwata ne" Ta6e baki tayi a lalace, sannan ta kalleshi sama da kasa ta watsar, sannan tace “Allah ya kyauta… Aysha ta yi a sarar masoyi…” “A ganinki ko? ni dai na san a duniya babu wanda ya kai Aysha da ce da masoyi, sabo da tsanain son da yake mata ya sanyawa kansa bibiyar al’amuranta ba tare da saninta ba, a hakan kike ganin tayi a sarar masoyi?” A yanzu kam kallon wahalalle take masa, kamar bazata tanka masa ba sai kuma ta budi baki ta ce, "Ai saka ba da himma, amma ka sani bazaka ta6a cimma burinka ba.” “Kin san me Ubangiji zai zartar a gobe ne?” Ya tambayeta yana mai kallon qwayar idanunta. Bata kalleshi ba kuma bata bashi amsa illah kwantar da kanta data yi a kan filo ta runtse idanunta. Ganin hakan da ya yi yasa ya nufi falo ya kwanta a kan kejera yana tunanin maganganun da suka yi da ita, shi kadai yake yiwa kansa murmushi, wani dad'i da farin ciki yana kwarara a cikin zuciyar shi, babu abinda ya fi tsaya masa a rai illah yanda take juya dan qaramin bakinta tana masa tsiwa a kan duk maganar da ya yi mata. Qarfe takwas na safe ta ji ficewar shi da mota, ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi domin tana tunanin Sadiya ya je daukowa kamar yadda yayi mata alqawari, minti arba’in tsakani ta ji dawowar shi da sauri ta nufi hanyar da taga yabi lokacin da zai tafi sallar asubahi, a falo ta ja ta tsaya don jiran qarasowar su, hannunsa ta gani dauke da ledoji manya manya guda biyu, ganin ya maida qofar ya rufe ya tabbatar mata shi kadai ne babu Sadiya. “Ina Sadiyar?” Ta tambaye shi bayan ta tare masa hanyar wucewa Bed room. Murmushi ya yi sannan yaja ya tsaya ya zuba mata kyawawan idanunshi, minti daya suna musayar kallo daga bisani yace, “Haba Baby..! ai a ganina sannu da zuwa ya kamata ki fara yi mini a matsayina na mai shirin zama mijinki…” “A ganinka ka ce koh? Don haka ni banyi niyya ba, ina ‘yar uwata na tambayeka ba dogon surutu ba” Ta fada bayan ta katse maganar daya fara yi tun kafin ya sauke numfashi. “Baby rigima ko? ‘yar uwar ki tana cikin qoshin lafiya, wanka zan yi muyi break fast sai in dauko miki ita.” Haushi da takaici ne ya cika mata ciki, wai ta ya ya ma wannan dan nacin ya samu nasarar dauko ta zuwa gidanshi? Ta tambayi kanta a cikin zuciyar ta. “Yi haquri, ga doguwar riga da hijabi na siyo miki ki yi wanka ki yi sallah sai mu yi break fast, daga haka abu na gaba a gareni shi ne dauko miki Sadiya don samun kwanciyar hankalin matata Aysha.” Bata kalleshi ba kuma bata amsa masa ba, illah juyawa da ta yi zuwa cikin bed room din da ta tsinci kanta tun data farko. Bayanta ya bi da kallo, a zuciyar shi yake addu’ar Allah ya mallaka masa Aysha a matsayin matar aure, “Amin” ya amsa a fili, sannan ya sunkuci leda daya ya bi bayanta zuwa cikin bed room din. Tana zaune a gefen gadon daya mamaye fiye da rabin dakin, ta dora qafa daya kan daya tana kadawa, ta hada girar sama data kasa. Yana shigowa ta watsa idanunta a kanshi, ta rasa abinda zata ce don haka ta cigaba da kallonshi har ya zazzage kayan cikin ledar a kusa da inda take zaune. “Ga bandaki can ki shiga ki yi wanka ki canza kayan jikinki ki bada faralin sallar da yake kanki, duk dogayen riguna ne, domin nafi qaunar ganinki a cikin doguwar riga kafin muyi aure…” Yana gama fadin haka ya nufi hanyar ficewa daga dakin, cikin sauri ta janyo bayan rigarshi, da yake dakakken namiji ne ko gezau bayyi ba, sai tsayawa da yayi cak, tasha gabanshi ta fara maganganu cike da fusata, “Wai me kake nufi ne? ka fada mini abinda kake nufi dani tun kafin nayi maka rashin mutunci, haka kawai kana neman takurawa rayuwata? Bayan kuma ni ban san ka ba, bana sonka bana qaunarka, ko ana dole ne a rayuwa?” Ta tsayar da maganarta tana maida numfashi cikin harzuqa, kallonsa tayi jin bai tanka mata ba, idanunshi suna kan qirjinta, saboda tsabar kallon da yake wa qirjinta ko qiftawa baya yi. Karo na farko da a rayuwarta da taji wani abu mai kama da kunya ya ziyarci qwaqwalwarta, laqwas ta yi cikin sanyin jiki, ta sauke qwayar idanunta zuwa qasa cike da matsananciyar kunya. Qirjinsa ne yake matuqar bugawa fat-fat, yana ta so ya dauke idanunsa daga kansu amma sam zuciyarsa taqi basa hadin kan hakan, gani yake har wani hanqoro suke suna toroko, shaidan hana ta kara kawata masa su a idanunsa. Dakyar ya fisgo a'uziyya yayi a zuciyarsa “A uzubillahi minash shaidanir rajim.” Ya fadi hakan tare da kauda qwayar idanunsa daga kan qirjinta, rashin qarfin jiki dana zuciya yasa yayi shiru tsawon wasu dakiku, sannan ya kamo hannunta guda daya suka nufi gadon, a gefe ya zaunar da ita sannan ya tsugunna a gabanta yasa gwiwoyinsa a qasa, murya qasa qasa yake fadin, “Aysha
Table of Contents