Chapter 18
Chapter 18
hijabin dake jikin Aysha gashin kanta mai laushi da santsi ya bayyana, mahaifin nasu ne ya matsa daf da inda take kwance ya tofa mata addu’a a tsakiyar kanta sannan suka dan ninka suka rufe mata gashin kanta, suka maida hankalinsu gaba daya kan mahaifinsu. Atishawa Aysha ta saki mai qarfi har guda uku, amma duk da haka bata farka daga barcin da ya yi awon gaba da ita ba. “Alhamdulillah.” Kalmar da mahaifinsu Hassana da Hussaina ya furta kenan sannan ya cigaba da janyo addu’oin bude majlisi cikin harshen larabci don samun albarkar Allah da manzonsa, sai da ya dauki tsawon minti goma yana jero addu’oin daga qarshe ya rufe addu’ar tashi da kalmar Assalamu alaikum. Sai da ya jira suka amsa sallmar tashi sannan ya fara da cewa, “Da farko dai sunana ABDUL YASSAR, wadannan da kuma ‘ya’yana ne ‘yan biyu da Ubangiji cikin baiwarsa ya azurtani dasu Hassana da Hussaina kamar yandna kuka ji Aisha ta kira sunansu, mu mun kasance daga cikin jinsin Aljanu amma musulmai masu bin Alqur’ani da sunnar Annabi (S.A.W) Mu mazauna qasar Sa’udiyya tun kaka da kakanni, a taqaice dai a daren da za’a haifi wannan yarinya Aysha muka samu sa6ani tsakanina da mai dakina Zahra’u mahaifiyar su Hassana da Hussaina,cikin fushi ta bar qasar Sa’udiyya a wannan rana, kasancewar mu tafiyar mu ta aljanu ba daya ne da taku ta Bil’adama ba. Sai ta dira a kasar Nigeria. Tana ta yawo sai Allah ya nufeta da giftawa ta gidansu Aysha. lokacin ita mahaifiyar Aysha tana tsaka da naquda tana neman taimako a gurin Ubangiji har ta fara fitar da rai da rayuwar duniya ta ji ana gyara mata tsugunno domin jaririyar jikinta ta samu damar fitowa duniya cikin sauqi. A hannun matata Zahra’u aka haifi Aysha bayan rasuwar ita mahaifiyar ita Aishar, sai riqon Aishar ya ci gaba da kasancewa a hannun mai dakina Zahra’u, mahaifin Aysha yana daga cikin maza marasa adalci ga iyalansu shi yasa sam Zahra’u bata qaunarshi. Aysha ta taso da halaye irin namu na aljanu. kadan daga cikinsu sune tana da kaifin qwaqwalwa duk da qarancin shekarunta, Tana da dauriya da Juriya da rashin tsoro, ba kamar bil’adama ba, tana da zafin nama da yin wasu abubuwa da sam bil’adama bazai iya ba. shekarun Aysha sha biyu a duniya Allah ya dauki ran mai dakina kuma uwar goyon Aysha. kafin rasuwar ta ne ta saka wasu hadimanta a jikin Aysha, shi yasa duk mai nufin cuta ga Aisha baya samun nasarar isar hannunshi jikinta. Idan ranta ya baci takan kwanta wani haske ya zagayeta wannan daga cikin aikin hadiman Zahra’u ne, tanada qarfin da bil’adama bashi dashi. A idanun namun daji sukan ganta ta zama naman dawa shi yasa har ta yi rayuwa shekara guda a dajin babu dabbar data ta6a yunqurin cutar da ita. Wadannan duk aikin hadiman Zahra’u ne, a ranar da Zahra’u ta koma ga Ubangiji ne na tofa wata addu’a a kan Aysha ta yi barci bata farka ta ganta a ko ina ba sai gidan mahaifinta, wannan addu’a da nayi mata shine sanadin da sam bata iya barci da kanta idan har ba irin addu’ar aka sake yi mata ba, rashin samun hakan da kuma son ta yi barci yasa har wani namiji ya koya mata shan kayan maye, shi kanshi yaron bai samu nasarar hakan ba sai a dalilin abu daya, A lokacin da Zahra’u ta rasu mun dauki gawarta zuwa Sa’udiyya ni da su Hassana da sauran hadimanmu ciki har da wadanda suke jikin Aysha, wannan dalilin ne yasa ya samu nasara a kan Aysha na koya mata shan kayan maye. Dawowar hadiman Zahra’u jikin Aysha suka iske wannan baqon al’amari sunyi matuqar baqin ciki da ganin haka, duk yanda suka so hana ta shan kayan mayen al’amarin yaqi yiwuwa da yake komai sai Allah yaso da taimakon addu’a suke dakusar da qarfin kowace qwaya da tasha bata wuce awanni biyar tana barci, a yanzu dai mun fitar da hadiman mu daga jikin Aysha, kuma daga yau in Allah ya yarda ba zata sake shan wani abu don samun barci ba, zata ringa barci lafiya kamar kowane bil’adama. Duk wani taurin zuciya da taurin kai mun fitar mata dasu, jarumtar da hadiman suke bata da yanzu duk mun kaudasu. Ba komai ne yasa muka yi hakan ba sai don mun yi istahara munga kune mutanen da zasu iya tsayuwa a kan al’amarin Aysha, amma duk da haka zamu ringa bibiyar al’amuranta lokaci zuwa lokaci, kuma duk sanda take cikin mawuyacin hali zamu taimaka mata.” Bayan Aunty Hassana ta lura ya gama bayaninsa sai ta fara bai wa su Ardo tarihin rayuwar Aysha kamar yanda ta fada a baya, sannan ta qara da tabbatar da duk wani abu daya kusance ta suna sanar da ita ta hanyar saqo a wayar hannunta da lamba 777, ko bayani a kan rasuwar Sadiya saboda wayoyinta suna ajiye a gurin Abdul ne shi yasa basu tura mata ba. sannan ta ce, “Da fatan zaku kasance masu tsayuwa a kan al’amarinta kamar yanda Abbanmu ya fada a baya.” Aunty Hussaina ta sauke numfashi ta ce, "Muna tsananin son godiyarmu bazamu bari wani abu ya cutar da ita ba.” Ardo ne ya fara magana da cewa, "Alhamdulillahi rabbil Alamin, dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah S.W.T mai hikimar fitar da matacce daga cikin rayayye, tsira da Aminci su qara tabbata ga Annabi Muhammad S.A.W da Alayensa da Sahabbansa. Lallai al’amarin yarinyar nan Aysha yana tattare da abubuwa na ban al’ajabi da mamaki game da bil'ada. Amma a gurin Ubangiji wannan ba komai ba ne daga cikin qudura da iradarsa. Yana aikata abinda ya so a lokacin da ya so kuma ga wanda ya so. A lokacin da Modibbo ya zo min da batu a kan Aysha tare da nuna min hotonta na yi mamaki qwarai, ba don komai ba kuwa sai yadda na ga zallar son Aisha a idanun Modibbo wanda ban ta6a ji ko ganin yana son wata yarinya kamar ta ba. tun a lokacin na fara tunanin akwai wata qulalliyar dangantaka da Ubangiji yake son qullawa a tsakaninmu da wannan yarinya Aisha. Bayan Modibbo ya kora min duk wani bayani dangane da abinda ya sani na al’ajabi daga rayuwar Aisha, kamar misali yadda ta riqe hannun Yasmin ta karya ta, da yadda ta kwanta haske ya zagaye ta duk jama’a sun kasa isa gare ta, sai ‘yan’uwanta da suke tare da ita. Tun daga lokacin na san akwai wani boyayyen al’amari a tattare da ita. Ko da na yi istihara har na tsawon kwanaki bakwai a kanta babu abinda Ubangiji ya fahimtar da ni sai akwai wani dunqulallen sirri a kan Aisha. Kuma babu wanda ya isa ya samu nasarar cutar da ita sai abinda Allah ya hukunta a kan ta. A rana ta takwas da yin istihara ta ina zaune a nan falon sai Allah cikin ikonsa ya sa su Hassana suka ziyarce ni. Su suka sanar da ni akwai abinda zai shiga tsakanin Modibbo da Aisha, amma in yi haquri da duk abinda zan ji daga Modibbo, kuma shi ma in kwantar masa da hankali. Idan lokaci ya yi za su zo da mahaifisu don warware mana wace ce Aisha
Table of Contents