Chapter 17
Chapter 17
barta a motar. Bai bi ta kan 45 miscalls din da ya gani a fuskar wayar ba ya lalubo lambar Ardo ya danna kira. lokacin qarfe takwas da rabi na dare. Miqewa Aysha ta yi tana hararar Abdul din ta nufi cikin daki. yasa hannunshi ya janyota ya zaunar da ita a gefenshi. A speaker ya danna wayar yanda Aysha zata iya jin duk abinda ake fada daga can dayan bangaren. taji tattausar murya mai cike da kamala da dattijantaka ta watso sallama, Abdul ya ce, “Barka da dare Ardo!" bayan ya amsa sallamar cikin tsantsar ladabi da kwantar da kai. “Barka dai Modibbo, ina fatan dai lafiya?” “Akwai matsala babba Ardo.” Abdul ya fada muryarshi da tsananin damuwa. “Muryarka ta tabbatar da akwai matsala, me yake faruwa da har ya dimauta Modibbo?” Cikin nutsuwa Abdul ya gama korawa tsohon bayanin duk abinda ya faru tun daga zuwan su Yasmin da zuwan mahaifanta gidan da shawarar da ya yanke na mai da Aysha can garinsu ita kuma taqi amincewa. Ajiyar zuciya mai nauyi Ardo ya sauke kafin yace “Ina ita Aishatu?" “Gata nan tana jinka Ardo.” Abdul ya matso da wayar saitin bakin Aysha tana jin duk abinda Ardon yake cewa, "Assalamu Alaiki Aisha.” Ardo ya furta da muryarshi mai cike da kwarjini. ita kanta Aysha jikinta rawa yake gurin amsar sallamar tsohon, a kwai wata baiwa da Ubangiji yayi wa Ardo, wanda duk taurin zuciyar mutum dole ya shiga nutsuwarshi idan ya saurari maganar Ardo. Hakan ce ta kasan ce ga Aysha. “Aysha kiyi haquri da Modibbo, yana tsananin sonki shi yasa yake neman duk hanyar da zaibi ya tserar dake daga masu nufin cutar dake, ki bashi dama gobe ya kawo ki Yola, mu masu tsayuwa ne a kan al’amarinki bamu da nufin cutar dake, ki amince da duk buqatar da Modibbi zai zo miki da ita matuqar bai sa6ama addini ba, don Allah..” Gaba daya tsohon ya gama kashe mata jiki, sam ba zata iya musa masa umarni mai hade da roqon alfarmar da ya yi mata ba. duk da Aysha bata ta6a haduwa dashi ba, bata san lokacin da bakinta ya yi saurin fadin “Shikenan! zan biyo shi mu taho zuwa nan din, in Allah ya yarda" "Yauwa diyar albarka, Ubangiji Allah ya yi miki albarka” Yayi mata addu’a da muryarsa dake tabbatar da yayi farin ciki da saurin bin umarninshi da ta yi ba tare da musu ko gardama ba. “Amin summa Amin" suka amsa tare da Abdul, sulalewa Aysha ta yi zuwa cikin daki don ta je ta bada faralin sallolin da suke kanta ta Magariba da Isha’i. wani sanyi da dadi ne ke kwarara a zuciyar Aysha domin yau ne karo na farko da wani DA NAMIJI ya sanya mata albarka. WARWARA Zaman minti biyar suka yi a babban falon da Ardo yake ganawa da baqi na qofar gida. babu wanda yaga shigowar su cikin falon a mutanen gidan, kuma Ardon bai nemi su shiga cikin gidan ba, sai umarni da yayi wa Abdul ya bude fridge din falon ya dauko musu ruwan sha da kofuna. Qarfe goma sha biyu da rabi na rana a garin Yola ta yi wa su Abdul da Aysha, kasancewar jirgi suka hau kuma da suka isa shatar mota ya daukar musu har zuwa tafkeken Family House dinsu. Bayan musayar gaisuwa da suka yi tsakanin Ardo da Aysha sai sunkuyar da kai da ta yi cikin matsananciyar kunya, Abdul kam ko ba a fada ba an san farin ciki ne fal a cikinshi, yana zaune a dan nesa da inda Aysha take ya kalli Arxo ya kalleta. “Anya kuwa ita ce Aishar dana gani a hoto Modibbo?” Ya tambaya yana kallon Abdul cikin yanayi na tsokana. “Qwarai itace Ardo, me kaga ta yi?” “Gani na yi tafi wacce na gani a hoto kyau nesa ba kusa ba, anya bazanyi maka juyin mulki ba? don tafi dacewa dani ba kai ba” “Haba dai Ardo, me zata yi da tsoho bayan ga sabon jini? ai tsoho sai su Adda da suka ga jiya suka ga yau!” “Aisha wai ba zaki auri tsoho ba?” Ardo ya tambayi Aysha yana dariya cikin nishadi, murmushi kawai Aysha ta yi gami da sake sunkuyar da kai qasa cikin kunya mai tsanini, kwarjini da girman farin dattijon su suka hanata sakewa, ji take kamar qasa ta tsage ta shige don kunya. Sallamar da a ka doka a qofar falon ita tasa Aysha dago kanta da sauri tana kallon hanyar shigowa, da Ardo da Abdul suka mai hankali gurin amsa sallamar gamida bada umarnin shigowa. Aunty Hassana da Aunty Hussaina ne tare da mahaifinsu mijin Ammi Zahra’u, wacce ta zame wa Aysha Uwa da Uba da dangi gaba daya. Duk da tun lokacin sasuwar Ammi Aysha taga Dattijon tana da shekaru goma sha biyu ne a duniya hakan bai hana yanzu da ta ganshi ta shaida fuskar sa ba. “Oyoyo Aunty Hassana.” Aysha ta fada cikin murna tare da ta shi da sassarfa ta isa gareta ta rungumeta sannan ta koma kan Aunty Hussaina ta rungumeta tana dariya don tsananin farin cikin ganinsu. Har qasa Aysha ta durqusa ta gaida Abbansu Aunty Hassana, ya amsa mata cikin sakin fuska da walwala. “Diyar Zahra’u ta girma sosai, me kuke bata Hassana?” Dattijon ya tambayi Aunty Hassana fuskarshi qunshe da murmushi yana kallon Aysha, kunya tasa Aysha ta boye fuskarta a jikin Aunty Hussaina tana murmushi. Da fara’a a fuskokinsu tamkar sun ta6a ganin juna suka gaisa tsakaninsu, sannan Dattijon mai farin gashi duk jikinsa ya rungume Ardo suka sake yin gaisuwa irinta larabawa, har qasa su Aunty Hassana suka tsugunna suka gaida Ardo shima Abdul ya tsugunna cikin ladabi ya gaida Abbansu Aunty Hussaina, da fara’a ya amsa masa sannan suka yi gaisuwa a tsakanin su da Aunty Hassana. Mamaki ne fal a zuciyar Abdul ganin wadannan kyawawan larabawan ‘yan biyu kuma kyawawan ‘yan mata masu kama da Aysha. idan bai manta ba Aysha ta sanar dashi zai iya auran wadda batada da dangi? amma ga wadannan ‘yan biyu abinda ya raba kamanninsu da Aysha kan ne su farare ne tas yayinda ita kuma bata kaisu haske ba. A yanda Abdul ya fahimta shine a kwai sanayya ta ‘yan uwantaka tsakanin Aysha da ‘yan matan. da shaquwa mai tsanani tsakaninsu. Abbansu Hussaina ya ce, “Hussaina sai ku sallami qanwar taku koh?” ya fadi hakan yana kallonsu daya bayan daya. robar ruwan swan wanda Aysha bata lura dashi ba a hannun Aunty Hassana ta miqo mata, ruwa ne fari tas a cikin sa amma bai kai rabin robar ba. Hussaina ta ce, “Shanye ruwan cikin robar nan yanzu Aysha" Ba tare da wani tunani ba ko kokwanto a zuciyarta ta bude robar ruwan ta kai bakinta bata ajiye ba sai da ta shanye ruwan ciki gaba daya! Aunty Hassana ce ta amshi robar ruwan a hannun Aysha ta a jiye a gefe, ganin duk sun maida hankalinsu a kanta yasa mamaki da shakku suka fara qoqarin kawo farmaki a zuciyarta, bata sami damar yin tunani ba saboda wani barci mai qarfi da yayi awon gaba da ita ta sulale ta kwanta a jikin Aunty Hussaina da take zaune kusa da ita. Aunty Hussaina ce ta cire dan qaramin
Table of Contents