Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

A Dalilin Da Namiji Book 2 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ki rufa mini asiri don Allah, kada kisa na ai kata abinda ban ta6a sha’awar aikatawa ba, don Allah ki canza wannan kayan na jikinki kada shaidan yayi galaba a kanmu ni dake…” Yana gama fadin haka ya fice daga dakin ba tare da ya qara kallon in da take zaune ba. Sama da minti goma tana zaune a kan daddumar data idar da sallah asubahi, ko qwaqwqwaran motsi ta kasa yi, babu abinda take tunani illah abinda ya faru dazu tsakaninta da Abdul. Tana sanye da doguwar riga baqa, daya daga cikin kayan daya kawo mata. rigar ta yi mata cas a jikinta tamkar ya san size dinta, amma bata kama ta sosai ba, kunya ce ta hanata fita falo duk da tana jin qaran T.V sama sama daga in da take zaune. Sallama ta ji yana yi a kofar dakin ba tare da ya shigo ba, ta amsa da sanyin murya. "Aysha kin idar?" Da sauri ta amsa masa da cewar ta idar, duk da bai shigo dakin ba amma ta jiyo qamshin turaren jikinsa, hakan shiya bata tabbacin ya shirya ita yake jira su yi break fast. Ko da ta fito bata nufi kan dining table din ba in da ta hangesa, kan kushin ta zauna tana wasa da ‘yan yatsun hannayenta ba tare da ta kalleshi ba, a maimakon kallon qasa sai ta maida idanunta kan T.V don sauraren labaran duniya da ake shirin farawa. "Ki zo muyi break fast, lokaci yana qara qurewa” Ta jiyo muryar Abdul yana fadin haka, sai data dan ja fasali na seconds sannan ta kalleshi ido cikin ido ta ce, “Bana karyawa da wuri, sai zuwa 12:00am, ka ci abincin ka kawai ka dauko mini Sadiya mu koma gida, nasan yanzu hankalin su Fatima yana kanmu" Hankalinta yayi gida gaba daya, ta san suma suna can hankalinsu a tashe yake da rashin dawowarsu tun jiya. “To shi…." Maganar daya farayi ya maqale a maqogoronshi sakamakon hoton da a ka hasko a T.V tare da karin bayani kamar haka. "A yau ne da asubah wasu al’umma mazauna unguwar Zango dake cikin tudun Wada kaduna suka tsinci gawar wannan yarinya yashe a cikin wani kango cikin mummunan yanayi. Mutanen da suka tsince ta basuyi qasa a gwiwa ba gurin sanar da mai unguwar wannan yankin, nan take mai unguwa ya sanar da jami’an tsaro mafi kusa da gurin, domin yanayin da gawar yarinyar take ciki ya qazanta, a yanzu haka dai jami’an tsaron sun miqa gawar yarinyar ga likitoci don gano ainihin musabbabin mutuwar tata. Idan iyaye da ‘yan uwan wannan yarinya sunji sai su tuntu6i Ofishin ‘yan sanda na Tudun Wada kusa da Zango don samun qarin bayani a kan al'amarin” Fuskar Sadiya aka hasko sosai face fece a cikin jini, da yankan wuqa a gefen kunnenta na dama. Wani wawan ihu data qwallah tareda fashewa da kuka mai tsananin qarfi yasa ya mike akan dining din a firgice tare da toshe dodon kunnensa, a saba'in ya karasa kusa da ita ya zauna yana qoqarin rarrashinta don kada ta tara masa jama’a, amma sam taki saurararsa, kuka take iya qarfinta tana had'awa da qwallah ihu kamar wata qaramar yarinya. Kusa da ita ya dawo ya zauna sosai a kan kejera tare da kama hannunta yana murzawa a hankali alamar rarrashi, jin kukan yake har cikin zuciyarshi, babu abinda yake buqata illah nutsuwarta, amma sam taqi saurararshi. Karfe goma sha daya daidai agogon falon ya buga, hakan ya tabbatar masa ta dauki tsawon minti ashirin da biyar tana gunjin kuka, sannan kuma sam bata da niyyar tsayawa, sai ma qara qaimi da take yi tana qoqarin funcike hannunta da ya riqe, hannunshi biyu ya sanya ya jiyo da ita tana fuskantarshi, fuskarta kaca-kaca da hawaye, Idanunta sunyi jajur, rasa abinda zai mata yayi sai kawai ya janyo ta jikinsa, ya kamo fuskarta da hannu biyu ya hade bakinsu guri daya, da farko qoqarin qwatar kanta take yi tana mutsu mutsu, amma da yake qarfin mace da namiji ba daya ba dole ta yi laqwas a jikinsa. Juya harshensa yake cikin wani irin salo a bakinta, shaidan yana kara ingiza shi, ita kuwa tuni ta nemi kukan da take yi ta rasa sai a jiyar zuciya mai qarfi da take saukewa lokaci zuwa lokaci, don kanshi ya zare harshen nasa tare da tsotsar la66anta tsawon lokaci sannan ya zare bakinshi daga nata ya kwantar da kanta a qirjinsa yana shafa bayanta a hankali. Sun dauki lokaci mai tsawo a haka, sai da don kansa ya gamsu ta samu nutsuwar da zayyi magana ta saurare shi kuma ta fahimci me yake nufi sannan ya janye ta daga jikinsa. A hankali ya warware mata zare da a bawa na abinda ya faru tsakaninsu jiya da daddare, da suman data yi na tsawon a wanni hudu bata san a inda kanta yake ba kuma ba barci take yi ba. “Yanzu ki zauna kici abinci zan je na binciko duk halin da ake ciki sa’annan musan abinda ya kamata muyi.” Ya qarasa maganarshi cikin tattausan lafazi yana kallonta, fuskarsa cike fal da tausayinta. Fuskarta a marairaice take kallonshi, rau-rau tayi da Idanunta sannan ta bude baki dakyar tace “Don Allah ka barni na koma gida gurin ‘yan uwana, idan ina tare dasu zanfi sanin duk abinda yake faruwa….” Kallonta ya yi na tsawon daqiqu biyar zuwa shida daga bisani ya ce, “Ki yi haquri Aysha, a wannan halin da a ke ciki bai kamata kiyi zancan komawarki gurin ‘yan uwanki ba, abu mafi mahimmanci shine mu san a wane yanayi Sadiya take ciki…” “Toh ni dai zan bika, ina buqatar ganin gawar ‘yar uwata, kuma ina son sanin dalilin mutuwar ta” Aysha ta katse shi muryarta na rawa, qiris take jira ta fashe da kuka. Shiru yayi yana tunani tsawon minti daya sannan yace, "To ai ba kiyi break fast ba, kuma ko jiya ina ganin abincin da service ta kawo miki ai ko ta6a wa baki ba.” Sake marairaice fuska tayi, tace “Allah kuwa na qoshi, sam banajin yunwa, mu tafi kawai don lokaci yana daxa tafiya” Gyara zama yayi ya daure fuska, da muryar da babu wasa yace “Ashe kuwa babu inda zamuje, mutuqar baki ci komai ba na fasa fitar balle har in fita dake.” “To ni me zan karya da shi? Ni fa ba ko wane irin abinci nake ci ba…” Ta fada tana tura baki. Dining table din ya nufa ya hado mata tea mai kauri a kofi ya nufo inda take zaune ya ajiye, buredi ya dauko hade da soyayyan dankalin turawa duk ya jera a gabanta. “Oya! Sauko kici abinci matuqar kina son mu fita yanzu” Fuskarta a yatsine ranta a 6ace ta zauna a kan capet kusa da kayan karin da ya aje mata, bata kalli tea din ba don lipton kawai take sha da safe, dankali da qwan ta dan tsattsatsakura ta miqe tana fadin “Allahamdu lillhi.” Wani kallo ya watsa mata sannan yaja hannunta ya zaunar da ita a qasa, shima ya zauna a kusa da ita ya tsareta da idanunshi masu kwarjini, fuskarshi a daure yace, “Ina buqatar ganin wannan kofin tea din a ajiye a qasa matuqar kina buqatar mu fita” Ganin alamun da gaske

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});