Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Gangar Jikinsa Na Aura Book 2 Complete Hausa Novel 1,219 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gidan kamar a mafarkitaga kartan maza suna ta ajiye buhunhuna a kofar dakin inna haule . Mata suna ta shigowa dafantekun alkaki, nakiya dibulan da sauransu.Wannan al.amari ya bawa inna haule mamaki,nauyi da kunya saboda sunyi mata ba zata duk tabigari tana fadin ba.ayiwa hanna gara ba kuma bazasu iya yiba kwatsam sai ga gara wacce ko 'yayan attajiran garin ba'a taba yi musu gara mai yawanbuhunhunan haka ba. Nan dai inna haule ta haufara.ar borin kunya tana cewa ashe kuna tafe ku kaki sanar min nima in gayyato yan uwana suxo sutayani karbar irin wannan abin alhairi sannunku dazuwa ku shigo daki mana ya zaku zauna a waje. Hanna dibo tabarminki dana indo a shinfida baki.Ai da kun sanarmin zaku zo da nasa anyi mukugirke girke da soye soye irin wannan abin arzikihaka'' yan uwan hanna suka ce'' babu komai ai bazama muka zo yi ba mun kawo gara gata nan,zamu koma don yarmu ta sami salama a zamanta na aure da mijinta'' suma suka yaba mata ba dadi.Washe gari inna haule da sassafe taje ta debowahanna akwatinanta ta kawo mata amma ankwashe wasu kayan da yawa babu ta kumagargadi hanna kada ta sake ta fadawa danginta komijinta tayi shiru da bakinta. Da bello madu ya dawo faran faran inna haule ta kira shi ta nunamasa gara har tana cewa'' allah sarki ashe bakaramin shiri suke yiba shi yasa basu kawo dawuri ba irin wannan yawan gara sai kace yarsarkin noma ka auro '' bello yayi dariya ya ce'' Allahya sanya alheri ya bamu zaman lafiya'' ya nufi dakin hanna, bayan tayi masa sannu da zuwa ta kawomasa abinci da ruwa yasha sai ya jawo akwatinanya bude kamar yadda ya zarga tabbas mahaifiyarsazata kwashe wasu kayan haka kuwa ya gani takwashe kaya da yawa. Ya waiga ya kalli hanna saita sunkuyar da kanta kasa bata ce masa komai ba... Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 GANGARJIKINSA NA AURA 2 Part 2 Posted by ANaM Dorayi on 03:14 PM, 30-Apr-15 Under: Gangarjikinsa ta Aura Yace '' hanna an kwashe miki lefenki ko? Kiyihakuri zan suyo miki wasu insha Allah idan muka yialbashi wani watan'' hanna ta dago cikin ladabi datattausar murya tace'' ni na yafe duniya da lahira basai ka biyani ba wahalar zata yi maka yawa. Kawubello babu abinda zance maka sai godiya da wannan gara daka yimin Allah ya saka da alheridomin ka kwatar min yancina tun daga ranar daaka kawo inna bata sake yimin gori ba. Yanzu zanyizaman farin ciki a gidan aurena: yayai murmushiyace'' farin cikin ki shine nawa Hanna, Allah ya karasanya ki a farin ciki fiye dana yanzu'' tace amin na gode. Karshen wata nayi da bello ya dau albashi saida ya sisiyawa hanna kayayyakinta damahaifiyarsa ta kwashe cikin dare ya kawowahanna a boye yace ai hakkintane dole ya biya ta.Hanna tayi godiya ta karba haka hanna da bellosuka kasance yana kyautata mata a boye komai ya gani na sakawa kona marmari sai ya suyo mata dadaddare ya shigo mata dashi ya bata a boye ba taredaya bari mahaifiyarsa ta gani ba. Bello yana karason hanna saboda ladabinta hankali da nutsuwada uwa uba tsananin hakurinta da tawakkali itakuwa hanna har yau har wayewar gobe ta kasa masanya gurbin haisam ta mayar da bello zuciyarta.Idan bacci take yi tana kwance da bello ammamafarkin haisam take. Idan tunani take yi haisamkawai take hangowa a zuciyarta. Tana kokarin tamayar da soyayyar da take yiwa haisam kan bellosaboda ita ma ta saka masa da soyayyar, sabida irin kyautata mata da yake amma abu ya faskara hakadai take dagewa tana nunawa bello tana sonsawanda a zuciyarta ba haka bane. Wasu lokuta dayawa idan suka tashi da safe. Bello yakan ce matayaya haisam? Don jiya kina kiransa a mafarki.Hakika hanna duk sanda ta kwanta mafarkin haisam take yi ashe har ambatonsa take a fili.Saboda tsananin son da bello yake yi mata ya yardaya amince kuma zai zauna da ita a haka. Bai tabanuna mata bacin ransa ba. Ita kuma hanna sai tajitausayinsa ya kama ta nauyi da kunyarsa talullubeta. Amma yaya zata yi tunda GANGAR JIKINTA YA AURA ZUCIYARTA na wajen haisam.Matsalar gara ta wuce tsakaninta da surukarta saikuma matsalar da inna haule ta dakko ta dorawahanna ita ce har yanzu hanna ko batan wata batayiba balle ta samu ciki fada da gori a wajen innahaule babu dare babu rana. Bello yayi kokari ya wayar mata dakai akan cewa ba laifin hanna baneciki Allah ke badawa amma abu yaci tura inna hauletaki ta saurarawa hanna cewa take ga sa'anninaurenta nan dukka ciki garesu wata bakwaibakwai tunda yanzu watan hanna bakwai da aure.Yau hanna tun karfe biyun dare take kai kawo a tsakar gida bacci ya gagari idanuwanta. Duk budeidon da bello zayyi sai yaga hanna tana fita ko tanashigowa cikin dakin kaman a mafarki yake ganinta. Can yaji ana kiraye kirayen sallar asuba tayi. Yasahannu ta laluba gefensa yaji hann bata nan. Yayifirgigit ya tashi ya fito tsakar gida ya hango hanna a gaban murhu tana hura wuta ya karasa inda takeyace.' Hanna yau lafiyarkikalau kuwa tun dare kike shige da fice kinki kikwanta yanxu da asubar nan wutar me kikehurawa? Hanna ta danyi murmushi tace'' kawu kamanta yau da duku duku oganka yace zai aiko damota za kuje Agadas shine nake dora maka ruwan wanka naji yau garin da sanyi sanyi''Yayi murmushiya ce'' Ai jinsa nayi kawai meye abun turo mota daduku duku sai kace zamubar kasar'' Hanna tace''Agadas ai da nisa shi yasa kuma wata kila bakwana zakuyiba ko ? Yace' Gaskiya agadas da nisaba kuma cikin garin zamu shiga ba local government zamu je ina ganin wajen 450 Km nekuma bana jin zamu kwana ziyarar aiki zai kaimucan mu kuma yan rakiya'' Hanna tace '' Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya. Ina jin kiran assalatukafin ruwan yayi zafi ga buta ka fara yin yin Sallah ?Ta mika masa buta ta durkusa har kasa. Bello ya tsaya yana kallonta kawai saboda wata tsantsarsoyayyarta ce take kara sarke masa zuciya.Musamman wannan kulawa da ladabi da Hannatake masa, ya karbi butar ya shiga bandaki, kafinya idar da sallar Hanna ta hada masa ruwa wanka .Ya tashi ya shiga wanka. Kafin ya fito ta debo wankakkaun kayansa data wanke ta goge masa tadora akan gado ta goge masa takalmin da zai sakamar yadda tasaba masa kullum. Bayan yakammala yana goge gogensa da yan shafe shafesai ya dauko kayan da Hanna ta fitar masa ya saka.Tazo tana balle masa maballin wuyan rigarsa. Yayi murmushi yace'' Hanna na gode da irin wannahidima da kulawa da kike nunamin wannan yasaina kara sonki dari bisa dari, idan akwai soyyya datafi dari bisa dari ina miki Hanna sai dai ni anyakuwa na sami kwaya dayan nan kacal da nake so asanmin a cikin darin da ake yiwa haisam ?Cikin kunya hanna tace'' Haba daya kacal ai kafiguda daya'' yace '' a.a zancen gaskiya muke, nawaaka karamin ? Tayi dariya tace'' kawu ka wucegoma ma zaka kai sha biyar'' su duka suka tuntsireda dariya. Yace '' to tunda a wata bakwai na samigoma sha biyar nan da shekara bakwai zan iya tadda haisam'' suka sake tuntsirewa da dariya.Muryar inna haule ce ta katse musu dariyar da sukeyi tana bakin kofar dakinsu tana cewa'' tun dazumagana nake muku

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});