Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

Gangar Jikinsa Na Aura Book 2 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

a jikinsa damgi suke nema. Yasan ko za'a taimaka masa da gudummawa bai wuce ayimasa fantekar alkaki da nakiya ba sai 'yankwanikan cin abinci wadanda suka daddage nezasu bashi setin samira. Da cin bashi da komaiahmed ya hada kudin gado mabi lamba one damadubinsa. Dan kudin da hajir take tarawa na dinkin hular da take ta bashi ya hada da sauran yargudummawar da ya samu ya sayi ledar daki dalabule shikenan sai kwanukan rabon abinci dasamira seti hudu aka haka aka jerawa hanna adaki. Bayan an sha biki an kai amarya dakinta tsaftsaf daidai karfinsu sai dai wani babban tashin hankali ahmed ta buga sama da kasa ya rasa kudinsiyama hanna gara. Don haka yace hajir da wasumatan suje su bawa inna haule hakuri insha allahukafin ta haihu za'a kawo mata gara don har ta farahabaici an kawo amarya babu gara. Kwanan hannauku cur tana rusar kuka bayan an kaita gidan miji . A ranar na hudun ne bello madu ya shigo dakintada jakar kayansa shi ma ya kauro gidan daga cangidansa. Da misalin karfe goma na dare gari yayishiru kowa yayi bacci abinka da rayuwar kauyeamma a zaune a gefen gado ya tarar da hanna tayitagumi tana tunani ido yayi mata jawur a kumbure , yayi mata sallama ta shigo. Ta daga kai da sauri tadube shi sannan ta amsa masa sallamar da yayimata. Ya shigo ya ajiye jakarsa a gefen akwatinantayazo kusa da ita ya zauna yana mai yi matamurmushi da nuna farin cikinsa a fili, ya dubikwayar idanuwanta yaga jawur don tsananin kuka da tasha yi yace'' hanna kukan ne har ya zamarmiki da idanuwanki haka ? Don allah ki daina kuka,hanna ni mai kaunarki ne bazan cutar dake ba'' tasake rushewa da kuka yasa hannu ya jawotajikinsa sai yaga tayi sauri ta zabura ta mike tsaye,Wannan zabura ta Hanna ta bawa Bellomamaki kamar wanda ya dona mata wuta, ya miketsaye yasa hannu zai rukota. Hanna tayi sauri tajada baya tana kokarin ta fice waje. Bello ya ce'' a.ahar waje zaki fice to na kyaleki zo ki zauna bazansake taba ki ba'' sannan hanna ta dawo tazo ta zauna a kasa kan ledar dake shimfide a tsakardakin ta hada kai da gwiwa tana kuka tamkarranta zai fita. Wannan kuka na hanna ya tayarwada bello hankali ji yake tamkar tana soka masawuka a zuciyarsa idan tana zubar da hawayen nan.Ya nisa sannan yace Hanna kiyi hakuri dan allah ki daina kuka meke damunki ne ? Nifa yanxumijinkine ki daina guduna kuna ina da hakkinakanki muddin kina guduna kuma kina kuka kinatayar min da hankali.Nace kiyi shiru kinki ki daina.Ko kina so inyi fushi dake Allah yayi fushi dakeMala'ikun allah su dinga la'antarki har sai gari ya waye? Hanna ta dago da sauri ta kalleshi yace yayakike kallona? Gaskiya nake fada miki ai duk macenda take gudun mijinta Allah da mala'ikunsa zasudinga la'antarta har sai gari ya waye ko kin yaddaki halaka ? Hanna ta girgiza kai tace bana so nahalaka'' yace ''to in ba kyaso ki halaka zo nan kusa dani ki zauna muyi yira. Cikin sheshshekan kukaHanna tace"kawu na zalunci kaina, na kumazalunceka da ban fada ma gaskiyar abunda yakedamuna ba. Kawu na kasance ina cikin wani hali natsananin damuwa wanda har nake tunanin bazaniya auren kowa ba. To amma dole nasan za'a yi min aure shi yasa na hakura na amince na aureka atunanina zan iya daurewa in zauna amma yanzubayan da akayi auren ciwon da yake damuna yadawo min danye bana jin zan iya zaman aure har insami aljannar da kowacce mace take nema akarkashin tafin kafar mijinki ta hanyar biyayyar aure. Kawu kayi hakuri ka yafemin dan allah karufa min asiri. Ka sauwakemin mu zauna haka batare da kowa ya sani ba, saboda sai in halaka idanmuka zauna a haka da igiyar auren ka. Bello yabude baki yana kallon Hanna can ya taso yazogabanta ya durkusa ya rike hannunta cikin yar siririyar murya mai dauke da tsananin dimaucewayace'' Hanna., fadamin ni kawunkine mai shirintaimakonki ta kowacce hanya kada kiji tsoronfadamin ko mene ne '' ta janye hannunta a hankalita share hawayenta tace '' idan bakamantaba a labarin dana baku a garinmu nace nayimakarantar sakandire da taimakon yaya Haisamson yaya haisam ne ya zame min dafi a zuciyatawanda dafin nan zai iya zamra min ajalina. Kawubello inason haisam harni ma kaina ina mamakin yadda kayi zuciyata ta kamu da sonshi haka nayiaddu'ar don allah ya goge mun , nayi azumi nayikukan kullum akan allah ya yaye min amma kamarkaramin ake . Daga karshe sai nake addu'ar allahya dauki raina da in dauwama a haka amma kaganni har yanxu a haka na rasa yadda zanyi'' ta rushe da kuka. Bello yayi shiru yana kallonta shimacan ya nisa ya ce'l hanna me yasa nazakiyi addu'arallah ya hadki da haisam ba kuyi aure kike addu'arallah ya yaye miki sonsa ko kua allah ya daukiranki? Hanna ta goge hawaye tace:: haisam yayiaure a ranar da mahaifina ya rasu'' bello madu ya gyara ya zauna a gaban hanna ya lankwashe kafadon jin labarin wannan rikirkitaccen al.amarin nahanna. Hanna bata boye maiba ta bashi labarintadana haisam tun daga ranar da babanta ya kaitamakaranta har ranar gidansu ta iske shi zai tafidaurin aurensa, daga karshe tace'' ashe yaya haisam ba sona yake ba taimako kawai yayi min nikuma zuciyata ta kamu da tsantsar kaunarsa donhaka ne a koda yaushe nake addu,ar allah yayayemun sonsa bana addu.ar haisam yazo yaaureni. Bello madu yayi murmushi karfin hali yace''haisam yana sonki yana kaunarki sosai fiye dani kaina da duk wni mai sonki a duniya. Akwai watamatsalar da tasa bai aurekiba hanna'' hanna cikeda mamaki ta kurawa bello ido tace me yasa kacehaka me ka gani daka fadi haka?'' bello yace''saboda ke yarinya ce shi yasa baza ki fahimcihakan ba, kuma nasan irin yadda kike hanna bawai haka ta taba faruwa akaina ba a.a inakwatanta nima rayuwata zata iya shiga irin wannanhalin da kika shiga idan na rasaki saboda kecewacce na taba jin ina so a duniya. Ni na yadda naamince zanci gaba da zama dake a haka amatsayinki na matata amma babu zancen saki a tsakanina dake saidai mutuwa ta rabamu sabodasanda nake miki, hanna da ace haisam yana jirankibayyi aure ba da zan daukeki ina kaiki wajenshiinaura miki shi don kiyi rayuwa cikin farin ciki, ni indawo gida in zauna ciwon son da nake miki yakasheni na yadda indai na ceto rayuwarki. Amma yanzu da yake haisam yayi aure kiyi hakuri. A cikinkashi dari bisa dari da kike yiwa haisam, ki daure kibani kashi daya a cikin dari har karshenrayuwarmu ta aure na gode. Hanna ki daure kicigaba da zama dani a haka kada ki barni ni dakeduka muyi biyu babu, kin rasa haisam ni kuma in rasaki'' yasa hannu ya jawo jikinsa zai rungumetatayi sauri ta mike tsaye ta juya masa baya. Ya tashi asanyaye yaje ya rufe kofa ya datse da makulli. Yayinda hanna taji wannan rana tamkar ranar damahaifinta ya rasu ta kuma rasa haisam yau gata adaki zata kwanta gado daya da wani a matsayin mijinta ba haisam ba, hawaye yaci gaba da tsiyayomata daga idanuwanta. Bello yaxo ya rungumetata bayanta yana mai sunbatar kunnuwanta dagefen kumatunta cikin sanyayyiyar murya hannatace'' a matsayinka na mijina akan babu yaddazanyi ka sami

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});