Chapter 2
Chapter 2
gashi kya dan kashe'' dadi yalullubeta ta sami na cin abinci don yunwa take ji. Tayi masa godiya ta nufi gidan iya salmai . Ta isketaa zaure ta kasa zogale tana zaune tana jiran masusaya hanna tayi sallama ta shiga, bayan sun gaisaiya salmai ta ce'' hanna lafiyar ki kalau kuwa kinburkice gaba daya kamar ba keba? Hanna tayimurmushin karfin hali ta ce''iya yunwa nake ji ko da sauran dumame'' tace''wada na ajiyewa ya tafokwallo, rabonki ne zuba kici, da sauri hanna tamike ta nufi kicin don ta zubo tuwan. Iya salmai tabita da kallo, cike da tausayinta. Sharkab tana kukahanna ta fito ya sami iya salmai tana cewa allahsarki habu ka mutu kanar yarinya marainiya a duniya kaine daman gatanta'' hanna ta zauna asanyaye tana cin tuwan su duka hawaye suke yi.Iya salmai na tausayinta itama hanna na tausayinkanta. Bayan taci ta koshi tasha ruwa taje ta ajiyekwanon a cikin gida ta wanke hannunta sannantazo ta zauna ta shaidawa iya salmai halin da take ciki ta ce kuma tana neman alfarma idan da hali iyasalmai ta ajiye mata kwanan tuwo a gidanta tanaaika mata iya salmai taji dadi kwarai da hanna batayi kauron baki ba tazo ta sanar mata da wuri taceinsha . Allahu kome taci da kashin hanna to ammaitama ba kullum suke dora tukunya sau uku a rana ba.Itama ba da ko ta agareta ba bishiyoyin zogalene burjik a shuke a gidanta. Ta tsinka ta dafa tasayar ko azo a tsinka a danye a biyata. Daga ita saiwada wani dan kanwarta data rasu ta barshi tunranar da aka haifeshi ta dauke shi. Shima yanakokari ya samo kudi, to da haka suke cin abincin, ranar da ba'a samu ba su sayi na siyarwa ko suhakura idan babu kudin sayan na sayarwa. Iyasalmai tace'' ai idan naga 'ya'yan Habu raina dadiyake yi, ba don habu yana dan uwana bamasoyayyar da nake yi masa ce Hanna har yau ina jindandanonta a raina'' hanna tayi shiru tana tunani a ranta tana kuma tausayawa kanta cewar'' in har iyaSalmai bata daina jin dandanin soyayyar da takeyiwa mahaifinta ba har yanzu shekararsu tafiashirin da biyar da rabuwa gashi kuma ma har yamutu rana zancen sonsa ashe har abada iya Salmaibaza ta daina jin dandanon son nanba. To itama tana kyautata zaton haka zata kasance da donHaisam tunda gashi dai yanzu bata ganinsa yayiaurensa ma amma sai kara jin tana kara sonsa takeashe itama haka zata dauwama kenan har karshenrayuwarta. Soyayya gaskiya ce'' Hanna ta fadaabaiyane. Iya salmai tace'' soyayya gaskiya ce Hanna. Haka dai suka yini suna hira hanna ce tadafa musu abincin dare suka ci sannan suka yisallama Hanna ta tafi gida. Sun rabu akan iya Salmaizata ringa turo wada yana kawo mata abinci duksanda suka sami damar dafawa. Haka hanna ta kasance duk sanda iya salmai tadafa abinci ta aiko mata taci ranar da itama batadafa ba haka hanna take zama da yunwa. Ta ramekurkut da ita sai ido da dogon hanci tayi duhukuma saboda tsaban wahala da tsananin tunani .Ranar da iya abu ta fita takaba sai maigari ya hado malaman garin da masu fada aji na garin da yanuwan malam Habu don raba gadonsa ga iyalansa.A zauren gidan aka zazzauna ga iya abu gayayanta kakaf mata da maza ga hanna a gefe.Itama da iya salmai. Maigari yace'' a karantawamamacin kulhuwallahu kafa uku uku, da inna a'adaina kalkausar uku uku aka shafa Allah yakaikabarinsa. Sai maigari ya fara da cewa'' malamHabu ya rasu yabar mace daya da yaya takwas.Dukiyarsa kuwa wannan gidan ne da kumakatuwar gona. Amma tun ranar daya mutu akabiya masa basussuka da ake binsa da dan kudin daya bari. Ga manyan malamai nan zasu raba gado.Ga sunayen 'yayan nan a wajensu zasu shiga cikingidan su tsatstsaga su bawa kowa nasa bangaren.Iya abu ta nisa tace ina da magana nidai nicematarsa uwar yayansa kuma bare daya ce Hannedon haka a tabbata an bata bangarenta daban kar a saka min ita cikin kason 'yayana azo ana rigima.Maigari yace'' ai abu rabon gado ba'a cewa bareAllah ne ya raba da kansa don haka duk yadda takama haka za'ayi. Malamai sun yi iya kokarinsu sunkacaccala dan mitsitsin gidan nan d gona. Allahcikin ikonsa hanna bata tashi da komai ba sai rumbun ajiyar abinci,wani dam mitsitsine kasace turmus a kasan da gidan tururuwa sai dan wanibangare karami a tsakar gida shine kashin hanna agona kuwa bata ciki. Murna ta lullube iya abu gonada gaba daya dakunan gidan nata ne da yayanta sai tace'' wannan rabo yayi daidai to yanzu ta tashidaga dakin nan'' mai gari yace haba abu har yanzutsangwamar da kike yiwa hanne baki bari ba harmahaifinta ya mutu bakya rangwama mata ba''iyaabu tace a'a babu wani rangwame yan haya zansaa sauran dakunan ina karbar kudi wannan abu ne fa na gado. Nan fa duk suka hadu suna ta bawa iyaAbu hakuri ta barHanna taci gaba da zama a dakinda take har Allah ya yanke mata wannan zamatunda komai dadewa aure zata yi. Iya Abu takekashe idanuwanta ta ce in anga ta yadda Hannayauta sake kwana cikin dakin nan nata to ta bata kudin haya ne a matsayin tana haya.A cikin mutanen dake wajen harda Alh bilya ya ceto tunda Abu tace haka shi yayi alkawari zai dingabiyawa Hanne kudin haya daga yau ya tambayiAbu ko nawa ne kudin hayar dakin da hanne keciki ta kai kaice ta zambada kudi ya zaro ya biya ba tare da ya nemi ragi ba, ya biya na shekara ya saniya abu kora da hali take yiwa Hanne ta zambadakudi dan ace yayi tsada a kama mata a wani gidacikin ikon Allah sai taga ya biya.Mai gari da sauran mutanen dake wajen suka dingashiwa Alh bilya albarka, Hanne ita da baba Uba ne kadai suka san manufar Alh Bilya shi a nufinsaauren hanna zaiyi shi yasa ya fara mata hidima,wani gululun bakin ciki ne ya dira a zuciyar Hannamusamman da ya biya mata kudin haya ta san lallaida gaske yake auren nata yake so yayi ita ko garaa kasheta da a daura mata aure da wannan mutumin kamar tace bata son kudin hayar baza tazauna a gidan ba karya biya sai tayi tunanin in bagidan uban nata ba a ina zata zauna saita hakurakawai tayi shiru idan tace zata koma gidan iyaSalmai to ai daki daya ne kacal a gidan dan karamiita da wada suke kwana a dakin ba zaiyu ita ta hadu da Wada a daki daya ba saboda yanzu Wadashekararsa goma sha takwas yama girme ta dashekara daya don haka ya haramta su cusu a dakidaya bayan nan babu gidan wanda zata iya zuwata zauna duk danginta.Da daddare bayan kowa ya shige bacci ya kwanta hanna na juyi a yar katifar ta kasa bacci tsananinbakin ciki ne ya dameta a ranta bau abinda takenanatawa a ranta sai zancen hayar na. Ita da gidanubanta yau ta zama 'yar haya sai ta rushe da kukahar ta gaji. Tace''Allah kana ji, kuma kana ganina,kana kuma sane da irin abubuwan bakin cikin da nake gani tun ranar da mahaifiyata ta sakoni aduniya Allah ka fitar dani. Kaine gatana ya sarkinsarakuna. A haka Hanna ta kasance har shekaraguda da rasuwar mahaifinta. Yau taci abinci gobe tarasa wannan bai dameta ba sosai irin zurga zurgarda Alh Bilya yake yi
Table of Contents