Chapter 1
Chapter 1
GANGARJIKINSA NA AURA 2 Part 1 Posted by ANaM Dorayi on 02:56 PM, 30-Apr-15 Under: Gangarjikinsa ta Aura Hatta iya abu data tsani hanna yau hanna ta batatausayi matuka sai ta rushe da kuka ta dinga rikehanna tana lallashinta. Da kyar matan nan suka iyabanbare hanna daga kan shimfidar mahaifintasuka shiga da ita cikin gida. Hanna tana rusa kukakamar rabta zai fita amma ta nemi hawaye ta rasa. Sai tayi shiru ta shiga dakinta ta kwanta ita damahaliccinta ne kadai tasan me takeji a ranta waniabune ya tokare mata zuciya kamar dutse abun yafikarfin kuka. Hanna ta kalli gabas da yamma kududa arewa taga babu wani mai fitar da ita dagatsananin bakin ciki nan da take ciki sai allah . Ta tuno nasihohin da haisam yayi mata aranarkarshen da ya rakasu tasha sai tasa hannu ajakarta ta lalubo carbi ta fara ja. Addu'oi iri iri hannako magana ta daina yi, yan gaisuwa a jere a jeresuna shigowa dakinta suna yi mata gaisuwa sai daikawai ta bisu da kallo har sha.awa take idan taga masu kuka da hawaye. Don ita kukan ma takenema ido rufe tayi ko taji sanyi a ranta ta kasa sallace kawai take fito da hanna tsakar gida sai kumaasuba take shiga bandaki tayi wanka.Banda wannan babu abinda hanna take yi sailazumi. Babu ci ba sha sai da aka ga kwana da kwanaki hanna taki cin abinci sannan su iya salmaisuke dama dan farau farau suka tsaya tsayin dakaakanta suka ce sai tasha kurba kawai take badondadi ba ji take kamar madaci suka dura mata donrashin jin dadin bakinta da take ji anyi sadakarbakwai kowa ya watse gida ya zama daga hannah sai iya abu . Yayanta ma suk sunyi aure kowacce takomagidan mijinta sai mutuwa ta dawowa hannasabuwa fil sai a yanzu ne ta fara samun zubar dahawaye . Kullum hanna kuka take rusa ita kadai adaki babu mai lallashinta kaico hanna. Sati daya satibayu iya abu ta gaji da ciyar da hanna, ayau da sassafe shida da rabi iya abu tazo ta fara bugawahanna kofa kamar zata karya kyauren hanna nakishingide akan abun salla tun asuba bayan tayisalla ta zauna jan carbi gyangyadi ya dauketakamar a mafarki take jin bugun kofar tayi firgigit tabude ido taga ba mafarki take yiba ta zabura da sauri taje ta bude kofar. Iya abu ta gani a tsaye takama tsantsan tayi kalar rashin mutunci. Hanna tajigabanta ya yanke ya fadi tasan rashin mutuncin yamotsa yau kuma sai yadda allah yayi da ita.tace'' hanna a to an gaba hada hadar mutuwa nayina allah nayi na annabi na ciyar dake a aljihuna har sati bayu. Ga rogo can n aika a siyomin zan dafa infara zuwa kasuwa ina siyarwa don nima dan kudincefanen hannuna ya kare ubanki bakar dawakadai ya bar mana a rumbu don haka ke kincikashinki saura ta zama kashin 'ya'yana zan ringasiyar da rogo ina samun na cefane ina tuka dawata, daga yau ki fara ziyar da kanki kafin a raba gadogama sunce sai na fita takaba kar kice daman bangaya miki ba dan kar in ajiye tuwan dumame nekizo ki gutsira mun tuwo in kuwa kika sake kikagutsirar mun sai na shakeki sai kin amayo shi.Hanna ta sunkuyar da kai kasa hawaye ya zubo shar tace'' to naji'' iya abu ta tafi ta barta anan atsaye kamar an kafata ta rasa mafita kuma. Hanna ta kasance tana kwana da yunwa sai ruwada take dirka wai ko iya abu taji tausayinta ta dingabata dan tuwo amma taga makatau, sai ta shirya tanufi gidan malam uba kanin mahaifinta ta shaidanasa cewar yanzu bata da abunda zata ci ko zaiajiye mata kwano a gidansa ta dinga zuwa tana daukar abinci ko da sau daya ne a rana ? Yanabudar bakinsa sai yace mata daman ta girma ta rikawai ita yar boko ga irinta nan abincin da zata ci yagagareta shi dai shawara daya da yaga ta dacetunda duk samarin garin suna tsoron zuwawajenta suce suna sonta ganin ita 'yar boko ce to ta yarda yayi wa alhaji bilya mai kudin garin nanmagana yazo ya aureta, zata fi karfin abinci don hartuwan shinkafa dafawa akeyi a gidansa dadaddare. Wani daci ya disu a zucitar hanna da tajibayanin kanin mahaifinta. Alhaji bilya da yakemagana wani shirgegen tsohon mutum ne matan sa uku yaya kuwa sun doshi talatin da yawaiyayensu basa gidan kuma jikokinsa ma sa'annintane, manomine ba laifi yana samu a dai garin shi maikudi ne amma ai tana zuwa gidan ada wajenkawayenta tasan yadda yanayin gidan . Watakatuwar tukunya ake dorawa a gidan kamar ta yan makaranta girki ma kadai ya ishi matan baya gadukan mata da yake yi yana da ciwon kuturtakuma harma ta fara fitowa hannunsa da bakinsazaka kalla kasan kuturu ne yatsun ne kawai basugama guntulewa ba amma sun fara diwa. Hanna tatabbatar lallai baba uba ba sonta yake yiba tunda zai hadata da alh bilya aure. Tayi shiru a durkushe agaban malam uba tana jin bayanan da yake matayace'' kin amince inje in sanar masa ko kuma kinada magana kiyi.Hanna ta nisa ta sunkuyar da kai kasa tace'' bababana kin jin maganarka bane ko naki yarda alh bilya fa kasan halinda yake ciki yana da lalurarkuturta. Baba yanzu zaka yarda in aureshi a haka?Malam uba ya fusata ya zabura hanna da fada'' kekinfi sauran matan zane ne, asirinsu a rufe ko goyashi zaki yi kina yawo dashi? Kuma shi da kansa yasameni yace yana sonki zai aureki. Nake jira daman a gama zaman makokin nan in shaida miki. Tundakinki sai ki tafi ki nemo abinda zaki dinga ciigardiya dake kinki aure babu mai ciyar dake, tashiki tafi bani waje mutuniyar banza. Hanna ta tashisumi sumi ta fice tana sharba hawaye. Tana fita tanufi makarantar boko, ta kuwa ci sa'a ta sami alhaji wani ma'aikacin da yake zuwa daga local gov'nt tarubuta takardar neman aiki[application]tun tuni zainemar mata aikin koyarwa a primary garin.Hanna cike da fara'a da murna tazo ta duekusahar kasa ta gaishe da alhaji ya amsa. Tun ma kafintace masa komai yace''hanna na kai takardarneman aikinki wajen manyana alhamdulillahkansilan garin nan ya gani ta sa hannu an kaiofishin sacretary'' murna ta rufe hanna yaci gaba da cewa'' to amma abunda sakatare yace shine bazasu iya daukarki aiki ba saboda akwai wadatattunmalamai a wannan makaranta akwai daimakarantun da aka rurrubuta za'a kara ma'aikataamma daman banda garin nan don haka sai daikiyi hakuri. Hanna taji ba dadi hankalinta ya tashi tace'' yanzu malam alhaji ko share share baza adauke ni ba ko a can local govnt din? Ya ce shareshare ai kinfi karfin yin shara hanna kije dai kicigaba da addu'a , na manta ma ban fada miki ba natambaya ance result dinku na jarabawa yafito amma an rike na f.g.g.c kazaure saboda kunyi matukar ci sosai wai har da masu nine distinctionkinga dole aki sakin sakamakon sai anyikyakykyawan bincike anga ko an baku amsa ne.Hanna tace'' binciken zai dadae ne? Ya ce''gaskiyairn wannan yana daukar kusan shekara ma ba'asaki ba. Amma daman da da result dinki a hannu da tuni na samar miki aiki ko ba'a garin nan ba.Hanna ta dade a tsugunne a gaban alhaji tayi shiruta rasa yadda zata yi can ta yunkura zata mikedakyar saboda jikinta yayi sanyi sai alhaji ya mikomata yan kudi yace''
Table of Contents