Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Gangar Jikinsa Na Aura Book 2 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yaya ta gani bayan ta gamamagana tace ko waye muka zabar mata tana so. Cancanta ma ai ba sai an fada ba sun dace ai''hanna ta sukuyar dakai kasa sai hawaye shar yasake keto mata. Bello madu kam ya cancanci asoshi bashi da makusa kyau kuwa kamar shi yayikansa dan buzaye asali kamar balarabe, hankali datausayi kuwa ba'a magana don da yaji labarin hanna hawaye ya dinga yi don tausayinta bashi damakusa ko kadan amma ita abun da ya kara satakuka shine tana matukar ganin mutuncinsa donhaka bata so aka ce shine zai aure taba don dukwanda ya aureta sai yayi hakuri sabod bazai samisoyayyar taba GANGAR HIKINTA zai aura zuciyarta na wajen haisam har abada, hankalin hanna yasake tashi sosao da taji sunan wanda zata aurakawu ahmad yace'' ni wannan kukan naki ne yaketsoratani hanna kiyi magana idan akwai wani abunda yake damunki. Hanna tayi dan murmushi tagirgiza kai ta ce'' babu kimai zabin da kuka yi min yayi. Inna goshi ta dau buda kiwa ya hau cewa''allah ya sanya alheri ya baku zaman lafiya. Hanna tamike ta shiga cikin gida bata tsaya a ko!ina ba sai adakinta ta rufe kofa ta fada kan katifa sai ta budesabon shafin kuka mai tsanani taji a ranta kamarwata sabuwar soyayyar haisam aka kara zuba mata taji sonsa ya sake sartseta kamar zata yihauka. Bayan anyi haka da kwana uku hanna nazaune a tsakar gida tana tankaden gari da yammatana taya hajir aiki, hajir kuma na wajen murhutana kada miyar kuka, suna taba yar hira hajir tace''hanna ina ganin kinfi sauran mata sa'ar samun kintsatstsan miji a duk yan matan garin nan sabodaduk yawanci yan matan garin babu wacce batakaiwa bello madu hari ba farin jini gareshi sosai.Kyawunsa ne ko kuwa illminsa , ko kuma jan ajinsane yake rudarsu oho? Amma ke gashi kwatsam yadamu da sanki kinsan tun ba yauba kawunki ahmad ya fadamin cewar bello madu yana sonkiamma ya gargadeni da nayi shiru kar in sanar mikihar sai ya sanarwa da magabatansa shima. Hannata cije tayi dan murmushi tace'' hajir kenan watonayi sa'a sosai ashe dana sami bello madu ta sama.Ba tare dana wahala ba? Amma ni a wajena sai dai ma ince shine yayi sa'a sosai ma kuwa.Alhamdulillah amma akwai matsala tabbas. Hajir tajuyo gaba dayanta tana kallon hanna can tace'' bangane akwai matsala ba. Wacce irin matsala kumahanna ? Ko bakya sonsa ne? Hanna ta girgiza kaitace ta ce a'a ni naki shi bayan shine zabin iyayena ina sonsa mana. Muryar bello madu ce tace.''assalamu alaikum''.Kai tsaye ya shigo cikin gidan kamar yadda yasaba shigowa daman. Kai tsaye wajen hanna yadosa. Hajir ta amsa masa sallaman gami da yi masatsiya ta ce'' oh dan halak kaki ambato yanzuzancenka fa muke yi ango kasha kamshi dagazuwanka ka doshi wajen hanna da idan kazo wajen wa kake dosa? Bello madu ya kyalkyale dadariya yace'' kai hajir kin fiye tsokana kinsan da saiinyi sati biyu a boda ban damu da zuwa garin nanba amma yanzu kusan kullum sai nazo garin nanko banzo gidan nan ba ina jin dadin garin sabodamatar da nake so tana cikin garin. To yanzu an banu izini inzo wajenta kina nufin sai in doshiwajenki duhu bayan shigowata hasken fuskarhanna ne ya bugi idanuwana. Kinsan ko a kabarihaske ake nema ana neman tsari da duhu. Hajir tarike baki tace'' ah bello madu daina hadani daduhun kabari allah ya baka hakuri'' wannan hira tasu ta bawa hanna dariya bata san sanda tatuntsire da dariya ba duk da wani kululun bakinciki daya dira a ranta yanzun nan da bello madu yashigo haisam kawai zuciyarta take haska matainama inama aceda haisam za'ayi musu auren nanwata guda ya rage ayi bikinta. Bello madu yace'' hajir yi hakuri bada duhun kabari nake hada kibani na isa? Ai nasan kokarin da kike min wajenturani fadar zuciyar hanna tun dazu ina zaune atsaye ina jin hirar da kuke yi. Kuyi hakuri ba labe namuku ba ina doso kaina bello madu naji anaambato shiya sa na dakata sai dana gama jin komai'' hajir tayi dariya tace a'a baba bello ka faralabe a gidan mutane dai kawai zaka ce min'' yakarasa wajen hanna ya jawo wata kujera a gefentaya zauna a hankali yayin daya kafawa hanna idoyana kallonta. Ji yake tamkar ya hadiyeta sabodason da yake yi mata. Fargabarsa daya yana tsoro kada hanna taki amincewa da soyayyar da yake yimata haka nan bayan abokinsa ahmad ya shaidamasa an bashi hanna yayi farin ciki amma farincikin ragagge ne yana gudun kada a takurawahanna ta aureshi yazo ya rasa soyayyarta ammayau sai gashi da kunnensa yaji hanna tace''ni na kishi bayan zabin iyayena ina sonsa'' don haka yauyafi kowa farin ciki. Hanna ta dago a kunya cetagaishe shi ya amsa cike da fara'a ya mika hannu yakarbi rariyar dake hannunra ya fara tankade. Hajirkuma tana yi masa tsiya tana cewa'' wai bellowannan bamu san wanne irin abu za'ayiwa hanna bayan anyi aure tuwan ma kai zaka dinga tukamata. Bello yace ke kin fadi kadan tauna abincikawai bazan yiwa hanna ba saboda bazaiyu intauna mata ba amma a baki zan dinga bata bayanna dafa mata domin hanna tafi saraunoyar da takemulkin duniyar nan idan ma akwai yadda nake jinta a raina,Ga mamakinsa sai suka ga hawaye shar yatsiyayo daga idanuwan hanna. Babu abinda ya satakuka sai tausayin kanta dana bello madu dominkowannensu son maso wani yake yi, inama haisamne yake jinta a ransa haka kamar yadda bello maduyake jinta a ransa. Shima ina ma yadda yake sonta tana sonsa haka'' allah sarki bello ka makara''hanna ta fada a ranta' sai bello ya kurawa hannaido kawai yana kallo sai ya juya ya kalli hajir wacceitama tayi kasake a tsaye tana kallonsu. Ya miketsaye ya kade garin da yake hannunsa yace dahanna ta taso suje zaure yana son ganinta yana da magana da ita. Hanna ta mike ta dauko ruwa tawanke hannayenta ta yafa gyalenta tana biye dashisuka fita zaure. Tambayoyom da bello madu yajerawa hanna sun doshi goma dom son yaji meyeya sata kuka ko aurensa ne bata so amma duk daa'a hanna take amsa masa. Domin idan ta kuskura ta bayyana abunda yake ranta ta sake shiga ukutasan bello ba zai takura yace sai ya aure ta bahakura zaiyi idan ya fasa aurenta wazata aurakuma tunda bata da maganin ciwon da yakedamunta. Na san na rasa haisam, na rasa shi kumahar abada na rasa soyayyarsa na rasa farin cikin rayuwata, meye ya rage mun a duniya kuma?Banda jiran ranar mutuwa. Bello ya katsewa hannatunani yace'' to tunda na tambayeki kince ba komaiakwai wata magana guda da nake son muyi dakehanna don allah kiyi hakuri ki sake yin hakuri daduk yadda kika tsinci rayuwarki, abinda nake nufi shine watakila hajir ta fada miki ina da gida nawana kaina yanzi ma a ciki nake zaune nan za'a kaikibayan anyi bikinmu, to kinsan halin iyayemusamman ma mata mahaifiyata ta kekashe kasatace lallai lallai sai dai a kaiki cikin gidanmu ma'anagidan da take zaune da kishiyarta wanda ba karamar takura bane dakine kwaya daya jal ganata ga wanda za'a kaiki. Kiyi hakuri ko bayanbikin zanci gaba da bata hakuri akan ta yarda inmaida ke gidana'' hanna ta sunkuyar dakai tacekawu wannan ba wani abu bane da zaka damukanka. Kaabi maganar mahaifiyarka domin abunda

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});