Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Gangar Jikinsa Na Aura Book 2 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

a danginta yana cewa shifa yana so ya aureta. Dan har yaje ya sanarwa damaigari. Maigari yasa aka kira Hanna fada ya shaidamata abunda Alh Bilya yake nema a wajenta shin taamince zata aureshi, ta yarda tana so a dauraauren ? Hanna ta fito gar da gar ta fadi gaskiyatace'' ranka ya dade banki jin shawarar da ka bani ba amma dan Allah ina so a barni haka bana so inauri kowa. Gaba daya aka dau salati aka fara yiwaHanna ''cari to ba'a garin nan ba. Duk garin nanwacece ta taba kaiwa shekara goma sha takwas baa yi mata auren fari ba? Hanna tace'' ba zan iyaauren Alh Bilya ba a matsayinsa na mahaifina dan ni tamkar mahaifi yake a wajena. To haka akayi daHanna a fada. Alh bilya yaji haushin Hanna data kiyarda amma yasan tuggun da zai tafka mata yarama.Bayan anyi haka da hanna a fadar maigari dakwana uku. Alh bilya yazo har cikin gidan su hanna da rana tsaka . Hanna na daki a kwance tanajin yunwa tana jiran a kawo mata abinci daga gidaniya salmai tana fargabar ko suma basu yi abincin bane yau sai ta jiyo muryar alh bilya yana rafsasallama iya abu ta fito iya abu tace''yau alhaji dakanka a gidan namu. Yace'' eh wallahi zuwa nayi mu gaisa inji ko yaushe kudin hayar dana biyayake karewa? Iya abu tayi dariya ta sosakwarkwata a kai tace'' ai sauran wata uku ne inajin''ya ce''to ki raba kudin hayar gida hudu ki daukikashi uku naki ki bani kashi daya ragowarwatannin uku ki kori hanne daga dakin da take haya in bata biya ki ba ba ruwana'' iya abu ta batarai tace. To ni yanzu na kashe kudi yaya kake sonayi a ina zan samo kudinka da zan dawo makadashi ? Hanne fakara'u ko sisi bata dashi ina zayasamo wani kudin haya ta biyani? Gaskiya alh bilyakai ya dace kaci gaba da biyan kudin haya don haka kace a gaban maigari''yace''kash ni bakifahimceniba abu ba don in takura miki ba nace kibani sauran kudi ji rike sauran kudin ina nufinyanzun ki koro hanne daga dakin da take donnibada yawuna take zaune a dakin ba kuma ba'akudina ba. Iya abu tayi dariya tace''oh na gane wato yanzu dai in rike ragowar kudin watanniukun da suka rage kenan sannan in koro hannewaje idan bata biyani kudin haya ba ko. Ko bahaka kake nufi ba? Alh bilya yayi dariya yace''hakanake nufi mana.iya abu tace an gama ai a gabankazan koro shegiyar. Gaban hanna ya yanke ya fadi tayi zumbur ta tashi zaune ta dafe kirji tana tainnalillahi wa'inna ilaihirraju'un. Iya abu ta wangalelabulen dakin ta shiga budik ta sami hanna a kankatifa a zaune ta mikawa hanna hannu tace''banikudi. Hanna tace''bani da kudi. Iya abu ta wawurijakar hanna zata wurgar waje hanna ta rike tana mata magita tayi hakuri dan Allah ta rufa mata asiri,amma kamar zuga iya Abu take.Hanna ta fito da gudu daga dakin ta zo ta durkusaa gaban Alh Bilya tana rokonsa dan Allah yayihakuri ya bar mata kudin hayar wata uku kafin nanzatasan yadda zatayi ta sake biya. Amma yayikunne uwar shegu da ita yana cewa''yauwa Abu ki tattaro kakaf kayanta ki watso''ana cikin wannanhali sai ga Wada nan dauke da kwanan abinci yakawowa Hanna abincin rana ya sami Hanna kacekace tana kuka a durkushe a gaban Alh Bilya tanarokonsa iya Abu kuwa tana ta faman watsi dakayanta. Cikin kuka Hanna tace'' wada kaga halin da nake ciki jeka ka kira iya Salmai tazo ta rokarsu.Nan da nan wada ya garzaya dan ya shaidawa iyaSalmai halinda yazo ya tarar da Hanna. Bayantafiyar wada ba dadewa sai ga iya salmai da maigarida tawagarsa sun shigo gidan suka iske hanna acikin wannan hali. Maigari ya ce'' subhanallai Alh Bilya da girmanka meye haka? Alh Bilya yace''ranka ya dade babu yadda za'ayi taci gaba da zamaa cikin kudina bayan bata sona shi yasa nazo na ceto in Abu taga zata bar Hanna taci gaba da zama akyauta to. Amma ba dai nine ke biyan kudin nandole Hanne ta fita don bazan barta taci gaba da zama a kudina ba tunda bata sona. Nan dai akahau bawa Alh Bilya da iya Abu baki ana musuwa'azi da nasihohi akan rayuwa ce kuma sumasuna da yaya zasu iya mutuwa su bar yayansusuma ayi musu haka. Hanna tasa gefen zaninta tagoge hawaye ta mike daga durkusan da take yi ta juya ta kalli su maigari tace'' ku kyalesu ni nahakura da zama a dakin zan koma rumbun inzauna hanna ta fara dibar jakunkunan ta tanashigarwa cikin rumbun nan mai gidan tururuwa dacinnaka ga bunhunhunan dawa da kaikayi.....ANA CIKIN WANNAN hali ne Musa danmakwabtansu ne ya shigo yace'' wasu maza gudabiyu gasu nan a waje wasu farare ne kamarlarabawa sunce suna neman Hanne 'yar gidanMalam Habu. Mai gari yace'' larabawa daga ina ?Musa yace sunce daga Niger suke maigari yace'' to muma ai tafiya zamu yi mu tafi kawai, har Hannasuka yiyo waje wasu samari farare sol sol ne gudabiyu a tsaye a kofar gidan daya daga gani kotambaya babu jinin hanna ne don kamar su dayakamar an tsaga kara maigari yace ''kune bakindaga Niger ? Suka amsa 'eh' sannan suka duka suka gaishe dasu maigari. Hanna ta tsaya a gefetana kallon wadan baki nata bata san suba ammadaya daga cikin samarin kamarsu daya futik dagagani babu tambaya daga tsatso daya suka fito.Maigari yace'' to ga Hanna . Yaya kaman baku sanjuna ba. Mai kama da Hanna yace'' ni sunana Ahmad wannan abokina ne sunansa Bello Madu. Nikanin mahaifiyar hanna ne uwa daya uba daya.Hanne bata taba ganina ba ban taba ganinta bashine nazo na nemota don muga juna'' Hanna najinhaka sai ta daka tsalle ta rungume Ahmad sai itadashi suka rushe da kuka. sai suka rushe da kuka. Maigari da sauran mutane sai suka hau girgiza kaisuna masu tausayinsu. Maigari yace'' Alhamdulillahgara da Allah ya kawo ku sai mu koma daga cikin atattauna. Bayan kowa ya sami waje ya zauna,Hanna ta tashi ta dauki kwano ta kwalfo musuruwan sha a randa ta kawo musu, bayan sun sha. Maigari ya fara bayani ya shaida musu duk halindaHanna take ciki yanzu ma ga jakunkunanta nan awatse a waje dakin da zata zauna ma yanzu yazama garari. Ahmad ya matse hawaye yace'' hakikatuntuni munji irin halin da mahaifiyarki ta shiga harta rasu mun san kuma halin da yarta Hanne zata shiga amma da yake ni ina yaro bani da ikon inzoin dauketa shi yasa na hakura akwanakin nankuma na dinga mafarki iri iri na 'yar uwatamarigayiya uwar Hanne. Kullum na kwanta baccisai inga yayata Habi tazo tana cewa Ahmad danuwana yanzu baza kaje ka nemo 'yata ba Hanne kaga halin da take ciki ba a duniya ba, ko darenjiya ma nayi mafarkinta abu daya kuma takemaimaitawa don haka yanzu daman nazo da niyyarmu tafi da ita ko da mahaifinta yana nan zanrokeshi ya bani ita idan batayi aure ba in tafi da ita.Balle kuma yanzu da ya rasu dole in tafi da ita. Iya abu ta tabe baki tace malam tunda ransa ya hanaakai hanna wannan garin'' maigari da jama'arsa suka yiwa abu caa suka rufetadafada suna cewa'' ba yanzu kika gama mata watsida kaya ba? Bayan bakar wahala da take sha tuntana karama ta zamo

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});