Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Gangar Jikinsa Na Aura Book 2 Complete Hausa Novel 1,196 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

baku jini ba kun shige dakikuna tuntsira dariya da duku dukun safiyar nan tomotar ofishinku ce tazo suna ta kwankwasa gida . Daman Hanna abinda kika sani kenan ki shiga dakida miji kina dariya aikin kenan ciki fal kashi, babugurbin kwanciyar Da sai gurbin tarin kashi'' Hannatayi kasake yayi sanyi fara.ar da take yi ta koma cikiranta ya baci damin da ana siyar da ciki da ta suyohaka kuma da a wani waje ake nemoshi da taje ta nemo duk wahala koda kuwa zata mutu ne. Ko tahuta da zagin da gorin da ake yi mata. Bello yayiajiyar zuciya yace'' inna gani nan zuwa shiryawanake'' ta wuce ta tafi tana tsaki tana cewa'' Kaje kadawo dai daga tafiyar kazo mu zauna muyimaganar saboda bazai yuba, in zuba muku ido haka kawai aure wata bakwai kenan babu ciki baalamarsa kaina da kafafuwana turawa yarinyaabinci nake sai dai taci tayi kashi kawai. Ai ba dantazo ta cika mana shadda muka aurota ba mumamuna so muga dan jariri a gidanmu. Tunda tashanye ka ta asurce ka baka ganin lefinta to ni bata asurceni ba dole ka karo aure idan ma baza kasake taba, kai dole ma ka sake ta ka auro maihaihuwa don daki daya garemu a gidan nan'' Harinna haule tayi nisa ta juyo ta dawo ta tsaya a kofardakinsu Hanna tace'' Hanna kiyi ki fito daga dakinnan yau duk ke zaki yi aikin gidan nan shara wanke wanke surfe da girki ki fara debo ruwatukunna idan kin cika randunan gidan kakaf sai kifara aikin gida da yamma kuma kije gona ki tsinkowake da gyada dan sun nuna. Yau wacce kukeaikin tare indo aikenta zanyi magarya wajenkawata. Tunda ba ciki garekiba ba goyo ba ai wannan aikin bazai gagarekiba, sai dai idan kinjikashi sai kiyi a gonar tunda cikinki sai kashi babuhaihuwa. Kinga kuwa kashin naki ya zamar mintaki a gonar kinga kin taimaka kema'' Bello maduya fisata baisan sanda yace'' Haba inna ki dainayiwa hanna gorin haihuwa ba laifinta bane rashin haihuwa Allah ne yake bayarwa inna dama haryanzu Hanna ce take debo ruwa a rafi ina almajiriindana dauko aiki nace zan dinga biyansa. Ita taji daaikin gidan su kuna almajiran suje gonar. Hannatasa hannu ta toshe masa baki tace '' yi shiru karkasa taji haushina, mahaifiyarka ce babu komai duk zanyi aikin. Inna Haule ta rike baki tace'' inyedannan ka fara fada in fada dani akan matarkalallai abun babba ne jeka ka dawo ka sameni donwallahi ina ganin zamanka ya kare da wannanyarinyar mai kama da tumatir ina ganin rabaka takesotayi da kowa a duniya har dani dana haifeka . Ba'a haiyacinka kake ba na sani bayinka bane. Tatafi tana surutanta dai barkatai. Hawaye yana zubashar daga idon Hanna. Bello yasa hannu ya gogemata zuciyarsa cike da tsananin tausayinta ammayafi jin tausayin kansa da kansa. Saboda zaifi hannashiga wani hali,idanmahaifiyarsa tasa ya saketa don shine yafi sontafiye da yadda take sinsa idan ya rabu da hanna yarabu da farin cikin rayuwarsa. Kalma daya ce yasanidan yafadawa Hanna duk irin bacin ran da takezata yi dariya idan ya ambaci sunan Haisam . Yayi dan murmushi ya kalleta yace'' Hanna dama ace ayanzu kina da ciki ki haifanmun da namiji in sakamasa suna haisam. Hanna ta dago ta dubeshiidanuwanta a cike da hawaye sunyi jawur donkuka amma saida murmushi ya subuce mata a taketaji zuciyarta ta fara dan hucewa daga tsananin tafasar da take yi saboda kunar maganganun dainna Haule ta fada mata. Hanna taji wani dan sanyi aranta wani abu ya dasu a zuciyarta da bello yace ''dama ace ana da ciki ta haifi da namiji ya saka masasuna Haisam taji dama ace hakan faru mana. Ammadata tuna yanxu ma haka al'ada take don haka zancen ciki ma babu shi sai ta sake rushewa dakuka. Bello ya jawota ya rungumeta akirjinsa yanashafa lallausan gashinta yace'' Hanna lallai yauranki ya baci sosai har in kira miki Haisam ammakici gaba da kuka kiyi hakuri ki yafewa innata mucigaba da yi mata addu'a Allah yasa ta gane gaskiya Allah ya cusa mata soyayyarki a ranta. Hannatayiajiyar zuciya tace amin'' amma ka tayani addu'aAllah ya bani ciki kafin karshen watan nan inaganin haka zai saka soyayyata a zuciyar inna. Belloyace amin ya Allah, zan dukufa da addu'a kema kiyiAllah ya amsa mana. Ya goge matahawayen idanuwanta ya sumbaci kumtunta yace'' Haisamsunan danmu fa. Hanna ta kyalkyale da dariya tarufe ido sai taji wani farin ciki ya lullubeta. Tatsugunna ta jawo takalminsa ta fara saka masa akafa tana sake goge masa da tsumma. Ta feshemasa jikinsa da turare tace'' Kawu bello Allah ya kiyaye hanya kuje lafiya ku dawo lafiya. Yace aminHanna Allah yasa nazo na sameki lafiya cikin farinciki'' yana tafiya yana waiwayan hanna, itama ta fitohar bakin kofar dakin ta tsaya tana daga masahannu har ya shiga dakin mahaifiyarsa sannanhanna ta koma daki. A zaune a gefen gado Bello ya iske mahaifiyarsa tana tunani tana gayda kai yadurkusa ya gaisheta ta amsa a fusace ta fara masfada tace'' to dannan abunda nake so dakai shinekarka yadda kayimin musu akan duk hukuncindana yanke akanka ina nemar maka aure a gidandagacin garinnan yar sarauta ka dace ka aura tubda ka makalewa Hanna baza ka iya sakinta bato ta zauna anan gidan tare dani ita kuma waccamidan anyi aure sai a kaita gidan ka. Bello ya dagakai ya kalleta zuciyarsa cike da bakin ciki.Gidan da yasha magiya ta yarda akai Hanna takiyau gata da bakinta tana cewa yayi aure yakaimatarsa can amma banda Hanna ba. To ashe hannadin ta tsana kawai . Ya nisa yace inna me zai hanamu tare mu duka da amarya da hanna duk inhadasu acan din'' Ta girgiza kaia tace '' nace maka karka yimin musu ko? Haka naga dama, tashi kajeka dawo din mu karasa maganar amma idan kamatsa akan sai ka mayar da hanna gidanka zaka saince ka sake ta don wallahi hanna baza ta tare awancan gidan va sai dai idan bani na haifeka ba. Kobayan raina ka kaita can Allah ya isa'' Bello ya rike kai don takaici can yace'' Naji inna na gode, danAllah ki yafemin duk abunda nayi miki, idan na batamiki rai a rayuwata gaba daya''Tayi dariya tace ''Babu abunda ka taba yimin wallahi ko musun madaka tarka kake mun bayin kanka bane ta shanyeka ne na yafe maka Allah yayi maka albarka Bello ya mike ya fita hawaye ne shar yake fita dagaidanuwansa . Yana fitowa hanna tana jika gero tayisharkaf da hawaye daga gani ta gama jin dukmaganganun da suke yi. Kallo daya yayi mata yajihawaye ya sake kece masa. Yazo ya wuce tagabanta yace'' Hanna kiyi hakuri, ki sake yin hakuri, Allah yana tare da mai hakuri'' ta bishi dakallo tana hawaye yana waiwayanta yana hawayehar ya fice . Tayi shiru tana sauraren karar motarsuhar suka yi nisa ta daina jin karar motar, ta rushe dakuka tana cewa a ranta'' A bakin ciki ashe zandauwama? Yanzu aure inna zata sa kawu Bello zaiyi ya tareda amaryarsa agidansa ni abarni anan, meyasa inna ta tsaneni ? Me nayi mata tatsaneni? Meyasa kowaya tsaneni a duniyarnan ? Ubangijinayana sane dani, Allah kasan halin da nake ciki,Allahka fitar dani, Allah kaine abin godiya. Bayanfitar Bello madu da kamar awa guda. A lokacin hanna tana surfa gero,

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});