Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 11

Chapter 11

Gangar Jikinsa Na Aura Book 2 Complete Hausa Novel 1,215 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

inna haule tana tsakar gidatana cin dumamen tuwo, indo kuwa daga wanka tafito zata shirya ta tafi magarya inda inna Haule zataaiketa. Suka ji ,Mota tururus ta tsaya a kofar gidansu.Wani ma'aikacine mai sanye da kayan 'yan sanda,yayi sallama ya shigo ba tare daya gaishe suba. Yace '' Nan ne gidan su custom Bello madu ko @inna haule ta tsaya dacin tuwonta tace '' Nan neamma baya na waye yake nemansa? Yace inazuwa'' ya fice, gaban hanna ya hau faduwa . Daf-daf daman tun jiya ta kasa bacci saifaduwar gaba take. Jingine tabarya da take surfe ta tsaya. Kawai ji suka yi ana cewa' ku kamada karfiwajen kafadan zaku rike inna haule ta zabura ta mike da gudu ta lekoHanna ma ta biyota da sauri idanuwansu sukagane musu wannan gagarimin tashin hankalin,Gawar bello madu ce ake shigowa da ita. Allahyayi masa rasuwa a sanadiyar hatsarin motar dayaritsa dasu yanzu-yanzun nan suna hawa hanyarsuta tafiya Agadas wata babbar mota ce tazo gwaramusu suka kutsa ta tsakiyar motar cikin ikon Allahbello ne kawai ya rasu, sauran sun sami munanan raunika suna asibiti. Hanna ta fadi ta suma,yayin da inna haule take neman tube kayan jikntadon gigicewa sai da aka rirriketa. kafin kace kwabogida ya cika yayi makil da 'yan uwa da makwabtamaza da mata. Ani masa wanka, an suturtashi ankaishi an binne kamar yadda sharia musulunci ta tanada. bello ya tafi ya bar rikici gidansa kuma shitasa ta kare a duniya domin rikicin duniya da mairai akeyi duk wani rai saiya dandana mutuwa Allahyasa mu cika da imani, amin. hanna tayiwa belloaddu'ar har yawun bakinta ya kame, idan ta ya gajida addu'ar ta rushe da kuka tayi ta huta haka dai har akayi sadakar bakwai 'yan zaman makoki sukawatse aka bar 'yan gida. yayin da bacci yakegagarar idanuwansu, kamar yadda inna haule takekuka cikin dare haka hanna ma sai ta laluba kusada ita taji ita kadai babu bello sai ta tashi tayi kukahar ta godewa Allah. kaico hanneta rasa kowa a duniya. hanna bata shiga. watamatsala batabangaran ci ko sha ko aikin gida ba har ta fitadaga takabarta.sai bayan ta fita daga takaba an fara zancenrabon gado sannan inna haule ta daka tsalle ta diretace babu abunda za'a bawa hanna na gadondanta tunda hanna ba haihuwatayiba da bello saidai ta hada 'yan komatsanta ta bar musu gida.kawu Ahamed yaji haushi sosai ya kuma lashi takobin ko sama da kasa zata hadesai ya kwatarwa'yarsa hanna hakkinta a tumuli takaba shari'ar shida inna haule har kotin koli idn bata bari an rabagadon nan da hanna ba. yace kuma babu indahanna zataje a gidan zata zauna sbd bello yana dagado a gidan ubansa, inna haule kuma tace ita kuwa baza ta bayar da dukkiyar belloba sai dai suzuba. makudan kudi kuwa aka kawo daga wajenaikin su bello, gashi da filaye da wannan tafkekengidan nan daya sha suminti da bulo. inna haulekuwa tace duk natae banda hanna ko sisi baza tabata ba tunda ko kwai bata saka a gidan ba. tashin hankali ya tabbata a zuciyar hanna ta rasa yaddazata yi da rayuwarta da kawunta zai hakura ya bariinna haule ta rike dukiyar bello dukka ba sai anraba da ita ba. duniyar nawa take wanda yatara ma ya tafi yabarta kowa ma mutuwa zaiyi. dukwani hango jin dadin. rayuwarduniya yagoge a zuciyar hanna babu abunda take bege sai mutuwatazo ta dauketa ta tafi ta hutaitama. daga gidankawu ahamed dake aiko mata da abincin dare darana. tafi tafiya suma wata rana basa aiko mata donyau da gobe sai Allah. hanna ta fara fitar dazannuwan daurawarta da kwanukanta tana siyarwa snnn taci abinci. wata rana da yamma daindo sunje rafi sun debo ruw suna tafe suna hira saisuka ji hassan me yekuwa yana sanarwa yanacewa "yekuwa. jama'a ga wata sanarwa, mai girmadagacin garin nan yace a sanar muku matawadanda mazansu suka rasu suka barsu da suzo fadarsa yanzun nan. ma'aikata daga nigeria sunzomusu da tallafin taimako. gwamnatin jihar kano anigeria ta aiko da taimakon kudi za'a raba musu jaridomin su rike kansu da marayin 'ya'yansu. ammakada wata ta kuskurataje idan ba mijinta bane yamutu, sai wacce mijinta ya mutu idon ta zunguri hana tace hanna muje wajen taron nan ko Allah zaisa mu dace. hanna ta rike baki tace babu ruwanmuyanzu idan mukaje ai mun shiga 3 a wajen innnacewa zatayi munje. mun tona musu asiri aci muka jemu tambaye tako zata yadda. a hanya sukadingahaduwa damata wadanda mazansu suka rasu suna ta tafiya gidan dakaci don karbarwannan tallafi mai tsoka. kowacce tagasu hannasai tace au, baza ku taho fada ku karbiwannantallafi ba daga nig fa bakin suka zo, indotace gaskiya hanna in baza ki ba ni zanje sbd idanmukakuskuramukaje gida inna haule baza ta barmu ba.amma idan mun riga munje mun karbobabu yadda zata yi damu fada ne dai da zagi yazama jiki. hanna tace to mu shigagidan. adama muajiye ruwa muje din daman gudun fadan inna nake,to kobabu abundamu kai ma kullum zagin mu takemuje kawai, suka shiga gidan adama suka ajiye ruwan da yake kansu suka nufi fada wajen taron.mata ne makil akan layi suma su hana sukajekarshen suka tsaya. wata kyakkyawar mata ce azaune akan kujera da tebur a gabanta an dorawasu fles akan teburin. kallo daya zakayi wa matarkasan tana cikin daula fatar jikintamulmul sumul. dukda matar ba fara bace amma ba baka bacekalarta mai kyau kayan jikinta kuwa ko ba'a gayamaka ba leshin zai doshi dubu hamshin sarkargwal da dankunneta da zubbunan gwal reras ahannunta guda hudu sai sheki sukeyi.matar maifaraa'a gata bata kyamar talakwa sai gaggaisawa dasu take suna yin hannu. tace. kowacce tazogabanta ta rubuta sunanta don asan yawansukuma nawa ya cancanta a basu. kowacce ta hauzara ido sbd basu iya rubuta sunanta. matar taceyanxu duk cikinku babu wacce ta iya rubutu tazo ta taimka min mu rubuta sunayenku?Hanna tayi shiru kamr tace ta iya amma gudunsurutun 'yan garin nan kar ace ta cika nuna iyawasai tayi shiru. Indo ta zungureta ta hanna bakn iyarubutu baki rubuta mana Hanna tace a'a indo baburuwana a samu wani yazo yayi dan kar ace nazogarinku na zake. Matar ta sake cewa To tunda babu wacce ta iya rubutu ina ganin ba zaiyu mu aiwatarda aikin da zamu aiwatar ba a yau sai mun nemowacce ta iya rubutu sannan saboda da mata zallamukeso mu kafa kungiyar dole mace ce zata zo tarubutu mana sunayen indo da taga kiri-kiri zasurasa bata san snda tace A'a ranki ya dade ga hanna ta iya rubutu" sauran suka hau cewa hannataimaka mana ke kuwa ashe daman kin iya rubuturubutamana karmu rasa Matar tace wacece hanna?Ta fito tazo nan Hanna taje gaban teburin matar tatsaya tace gani ranki y dade. Matr ta kalli hanna smada kasa wata burgujejyar doguwar riga wacce aka dinkintada wani wagambari mai kauri irin nddinnan itama kanwar kkrta ce ta bata, gashintatufke a tsakiyar ki tai gammo dashi da zasu deboruwa sai wani yalallen gyale baki ta yana akanta datakalminta dan madina akafarta. Matar tayimurmushi tace yaya sunanki? Hanna tace sunana Hanna Abubakar imam" matar tace HannaAbubakar kin iyarubutu? Hanna tace na iya ranki yadade, matar tace ko da yake ku anan french kukeyiba turanci ba ko irin na 'yan nig? Hanna tace ni nafiiya turancin nig, french din kadan-kadan na iyamijina yana koy min

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});