Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Gangar Jikinsa Na Aura Book 2 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

babba ya hango yaro koya bishiyar rimi bazai ganoba, ita ta haifeka tafika sanin dalilin dayasa tacemaka ka zauna da matarka a kusa da ita . Allah yabamu zaman lafiya gaba dayanmu ni da ita. Ni dakai kuma na gode'' wannan kalamai na hanna yakwantarwa da bello madu hankali don bai taba zaton hanna ba zata damu ba idan taji yare dasurukai zata zauna amma sai yaji ita take kokarin yimasa nasiha, akan ya kwantar da hankalinsa yabimaganar mahaifiyarsa. Kuma hanna ita ce take yimasa godiya. Daga karshe ya yiwa hanna sallamayace zai koma wajen aiki sai nan da kwana hudu zai dawo an turashi tsakanin boda dake tsakaninmaigatari da niger da zarar ya dawo za'a kawo lefeinsha allah. Hanna tayi masa fatan dawowa lafiya yatafi ita kuma ta shiga gida,Ta iske hajir tana kwasar tuwo . Taje kusa daita ta jawo kujera ta zauna. Hajir ta kalleta taceamarya a gidan custom bello madu kinsha kamshi,amaryar nan da wata guda. Wai ya naga duk jiknkiyayi sanyi ne har koke koke kike yi? Koda yakemuma fa duk munyi wannan don gabanin bikina kurket na rame sai kuka ina zaton auren waniabun tashin hankaline ashe babu abinda ya kai shikwanciyar hankali, ke kuwa daga ke sai masoyinkiku biyu a gida ku rakashe kowa kokarin yafarantawa dan uwansa yake yi. Ke gidanki nasiminti ne kewayayye ai bello madu ya zuba sumunti a gidansa tal a lailaye da simunti kamar abirnin. Mu da muke gidan kasa ma muke jin dadinrayuwarmu balle ke'' hanna ta ce'' kai hajir ai dagidan simintin dana kasar duk dayane yanzu yakecemun mahaifiyarsa ta tubure lallai lallai bata yardata kaini gidansa ba sai dai in zauna a gidansu. Hajir ta zabura ta wurgar da marar da take kwasar tuwota mike tsaye ta rike haba da hannu tace'' hanname kika ce kina nufin yanzu gidan su bello za'akaiki? Lallai mun shiga uku mu masu kai amaryama balle ke da zaki zauna da ita. Hanna ra jawohannun hajir ta zaunar da ita tace'' hajir zauna mana muyi magana daga zaune me yasa kika cemun shiga uku wani abune ? Hajir tayi ajiyar zuciyata koma ya ta zauna tace'' hanna bazan boye mikiba a gaskiya innar bello bata da haki saboda dukgarin nan babu wanda bai san bala'in inna hauleba har tafi iya abu matar babanki da kike bani labarinta don tun maigidanta yana nan bai rasu batake azabtar da kishiyarta indo wahalar duniyarnan yau idan kika je gidan indo da yayanta tamkarbayi ne a gidan. Debo ruwa ma a rafi ya ishekibayan zuwa gona da sassafe amma shi bello meyasa zai yi mana haka bayan yasa halin mahaifiyarsa ko da yake ba laifinsa bane don idanta saka musu kara basun isa su tsallake bamusamman bello yana yi mata ladabi sosai fiye dasauran kannanshi shine babba a gidan. Ina jin batsso yayi nisa da ita gani take komai ya samu yanzuke zai dinga dankawa gaba daya'' kafin hanna tace wani abu ahmed ne yayi sallama ya shigo sukaamsa masa gami dayi masa sannu da zuwa. Amurtuke ya amsa sannan ya juya ta kalli hajir tadaka mata tsawa yace. Ke hajir ki iya bakin kidanme kike kokarin rikita hanna akan aurenta dabello madu akanta aka fara zama da sirikai'' ya juya ya kalli hanna yace'' to saikin toshe kunnuwankishi aure dan hakuri ne kiji kiki ji ki gani kiki gani,ladabi da biyayya shi zai rabaki da masifa datakurawar surukarki. Kada ki yarda da 'yan zugamasu nuna miki kin hadu da masifar suruka mutumko shaidan ne yasan mai kyautata masa don haka idan kika bi inna haule sau da kafa dole ta dagamiki kafa. Bawai nace hajir tayi karya ba hakahalayyar inna haule take amma sai kinyi hakurikindaure kin mata biyayya zaki ga ashe duk abundaake fada maki ba haka take bama'' hanna tasunkuyar dakai kasa tace'' to kawu naji abunda ka fadamin zanyi amfani dashi na gode madalla'' tamike ta shiga daki. Ahmed ya juya ya kalli hajirwacce ta cika tayi fushi taf kamar zata fashe'' yashafa kumatunta yace'' ke kuma daga maganameye abun yin fushin'' hajir tace'' haba ahmed mekake nufi da ka ce kada hanna ta saurari yan zuga, kana nufin nice yar zugar kenan zan hanata yinaure ko? Ya ce a'a abunda naga laifinki shinemuddin kika sanar mata halin innar bello madu aizata tsorata kuma zata ji ta tsani surukarta daganan zaman lafiya babu kuma ni bello ne yafi banitausayi har cewa yayi ko zai fasa auren hanna ne saboda yasan tabbas zata hadu da halinmahaifiyarsa shi kuma a duniya abunda yaki jiniirin batawa hanna don yana sonta kamar yaddayake son rayuwarsa. Mun kada mun raya da innahauke ta hakura ta bar bello ya tare da amaryarsa agidansa taki fur wani uban ashar ta soka min ahe haushina take ji wai na dauki yata na bashi, ashetana so ta hadashi da wata shine yaki,Sum sum nayi na ficedaga gidan. Kuma wani abun bakin ciki shine belloyayi yayi ta yadda ya rushe bangarensa yayi nasiminti ya zagaye da katanga tace bai isa ba ana kasar zai saka amaryar tasa. Sai zana ya suyo yadanzagaye dakin su kwaya daya jal kuma abincinsu ahade dana yan gidan zasu dinga yi allah dai yakyauta mana nan mun dukufa da addu'a alah yadora shi akanta ta hakura ta barshi ya zauna agidansa hajir tace''amin nima zan taya hanna da addu'a amma caf wannan suruka ta hanna. Ai kogidan bazan taba takawa ba da sunan ziyara ni tunina yarinya tsoronta na ke ko gidan bana shigaallah ya sani banasan masifa. Duk hirar nan da sukeyi kakaf a kunnen hanna wacce ke daki tana jiyosu. Tayi ajiyar zuciya ta girgiza kai don tausayin kanta da kanta tace a ranta. Haka allah yaso danihaka zan kare a kunci, wahala da bakin ciki narabu da wahalar iya abu na fada wahalat innahaule allah kana sane dani, kasan halin da nakeciki kaine majibincin lamarina la'ila ha illa antasubhanaka inni kuntu minaz zalimin. Babana yayi gaskiya da yace babu mijin da zan aura da zairikeni amana in ba haisam ba. Baba baka sanyadda mukayi da haisam ba ka mutu ka barni akaninje in cewa haisam yazo ya aureni ka bashini, yayahaisam ya auri wacce yake so yar barni, baba kabarni a duniya baka san na rabu da haisam din bama. Ta rushe da kuka mai tsanani. Ta koma takwanta a tsakar dakin tana tunanin rayuwar dasuka yi da haisam shine farin cikinta a makarantabaya so ko kuda ta cijeta tattalinta wasa da dariyakullum har ya zuwa ranar rabuwarsu. Hanna tayikuka har ta gaji sannan ta mike don zuwa bandaki tayi alwala magariba. Ashe ta dade dayi bata saniba. Kamar yadda bello madu yace za'a kawo kefeda sauran kudade na al'ada an kawowa hanna lefeakwati uku kowacce a cike danma inna haule dukta rarrage kayan amma duk da haka masha allahan zuba mata kaya. A nan kauyen sai zancen kayan ake yi 'yan uwan hanna sai murna ake ammabanda ahmed domin ya tsorata da ganin yawanlefen nan yasan dole za'a zuba ido aga me kymaza'a kai dakin hanna.A matsayinsa na dan karamin malaminmakaranta firamare mai daukar dan karaninalbashi shi zai yiwa hanna gado, gara da kumaabincin 'yan biki gashi kuma a kurarren lokaci akasaka ranar bikin. Gashi duk danginsu shine maidama dama duk

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});