Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 4

Chapter 4

Gangar Jikinsa Na Aura Book 2 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tamkar baiwa a gidannan.Ahmad ya ce'' ba saikun bata bakinku bama wajenbata amsa mu dai zamu tafi da ita . Sai yanzu daya mutumin yayi magana wato Bello Madu yace'' aianan kusa muke a garin dashi muke. Dashi dababban mutum ai border ce ta raba. Ni costom neina aiki a border lokaci lokaci zan dinga kawomuku Hanne kuna gaisawa. Ahmed ya katse shiyace ''duk zancen ka lallashi matan nan bai taso ba kaga kankat din gari wato maigari da jama'arsasun bamu izinin mu tafi da ita to wacece kuma zatace sai hanne ta zauna yunwa ta kashe ta. Iya Abutaji wani dacin bakin ciki ya rufeta ganin Hanna tasami wajen da zata je ta huta. Taso ace da ta yiwaHanna watsi da kaya duk garin ta rasa inda zata zauna. A haka dai aka rabu Ahmad da abokinsaBello Madu suka yiwa mai gari da jama'arsa sallamasuka daukarwa Hanna jakunkunanta, Hanna tayafa gyalenta tarungume iya salmai suna kukanrabuwa Hanna da kawunta suka tafi.sun isa garin Dashi da daddare gidan Ahmadsuka sauka. Ahmad yana da mata daya da 'ya'yabiyu , sunan matarsa Hajir itama irinsu ce buzuwa.Hajir ta tari hanna cikin fara'a da murna ta kaitadaki ta kawo mata ruwa ta sha sannan ta zaunasuka gaggaisa sannan taje ta shirgowa hanna tuwo. Hanna taci tuwo nan tamkar tunda allah yahalicceta bata taba cin tuwo mai dadin haka basaboda tsabar yunwa da take ji, taci tayi nat sannantace a nuna mata bandaki zata yi alwala Hajir tanuna mata. Hanna ta shiga ta dauro alwala tazo tayisalloli tana idarwa taje ta watsa ruwa tayi wanka ta kwanta. Hajir taji tana son Hanna, tana sonta dakawa daga gani ma sa'an nune, hajir ta zauna agefen shinfidar Hanna na kwance suna ta hira kalakala,Hajir bata bar dakin ba sai da taga Hanna tafara bacci sannan ta hure mata fitila ta rufo kofa tafita ta nufi dakin kwanciyarsu. Da asuba Hanna ta farka taji ana kiran assalatu ta mike ta nufi ban dakitayi alwalla tazo tayi salla ta zauna tana Lazumi.Gyangyadi ne ya dinga daukar hanna ta mike takoma kan katifa ta koma bacci tayi ta barci har shadayan rana babu wanda ya tashi Hanna sai da tayibarcinta ta gaji ta farka dan kanta. Tana tashi tayi ido hudu da soye soyen abinci kala kala Hajir tazota jera mata. Ba Hajir kawai ba 'yar uwan uwarHanna fa yawa labari yakai musu cewar hanna tazodon haka suka aiko mata da abincin karin kumalloiri iri sunka ce kafin suzo su ganta. Hanna ta fadawanka tayi brush sannan ta saka kayanta tazo ta zauna a gaban abincin burjik a jere a tsakar dakintaduk nata ne sai taji wani farin ciki ya lullubeta ba'asabanba, yau hanna ce da barcin safe ta farka tagaabinci burjik an jere mata haka Allah yake, duniyajuyi juyi. Tun kafin hanna ta gama karin kumallo tajitsofaffi da mata suna sallama a tsakar gida, yan uwan mahaifiyarta hanna ne suka fara cinci rindonzuwa ganin hanna, sai koke koke daga su harHanna taga dangin uwarta cunkus amma suka cemata wadannan ma kadan ta gani don tushenzuri'arsu Azbinawa ne [buzaye] suna Agadas state .Sai dai wani abu guda da hanna ta lura duk danginta talakawane sosai suna cikin rashi wasuNono suke sayarwa rugage suke wasu kumamanoma ne. kawu Ahmad ne kawai dan Bokowayayye mai dan hali akan sauran koyarwa yake amakarantar firamaren garin har ya sami matsayinmataimakin headmaster. Shima dai rufin asiri ne kawai ba wani arziki gare shiba. Gidansa ginin kasane dakuna uku ne, bandaki da zana aka zagayekicin kuwa a tsakar gida aka dasa murhuna. Hakadai Hanna taji ta shiga wata sabuwar rayuwa maidadi fiye da rayuwarta da agidansu. A koda yausheyana godewa Allah da yayi mata canji daga ukuba da bakin ciki hantara ya kawo ta inda aketarairayarta. Hanna da Hajir sun shaku sosai a kodayaushe suna tare suna hira wasa da dariya. Tunhanna na boyewa hajir wasu abubuwa nadangane da rayuwarta har ta yaba da hankalinta tafara gaya mata wasu abubuwa da suka faru da ita ada na dangane da tsananin son Haisam ranarrabuwarsu. Tace har yau kullum da daddare sai tayikuka idan taje kwanciya barci saboda tunaninsa.Hajir ta tausayawa hanna sosai har hawaye tayimata ,daga karshe tayiwa hanna nasihoho akantayi hakuri kaddara ce daga Allah haka Allah ya rubuto musu.BAYAN zuwan hanna da kamar wata guda kawuAhmad da sauran manyan danginsu suka kiraHanna babban zauren dake gidan. Bayan ta gaisheda kowannensu ta koma gefe ta takure. BabaSha'aibu yace'' Hanna kinsan dalilin da yasa mukakira ki nan? Hanna cikin ladabi ta amsa musu a'a yace to a matsayinmu na iyayenki da kakanninkimunyi nazari mun kuma tsayar da shawara abindanake nufi da munyi nazari shine bai kamata ba muzuba miki idanu haka nan ba babu aure don hakaya kamata kiyi aure a watannan kuma. Gabanta yayanke ya fadi ras dajin kalmar aure cikin rudani tace''....... Wazan aura ai ni bani da kowa a garinmuanan garin ma babu wanda yace yana sona.'' suduka suka kyalkyale da dariya. Ahmad yace''hanna kwantar da hankalinki dole mu aurar dakega mai sonki kece dai baki sani ba amma zuwankigarinnan maza sun doshi goma suka sameni suka ce suna sonki shawarar da muka yanke ita cemuduba a cikin waye yafi hankali. Addini. Sana'aasali wanda zai rikeki tsakani da Allah mu aura mikishi tunda ke bakuwa ce ba sanin halayensu kika yiba babu kuma isasshen lokaci da za'a barki kinasoyayya dasu har ki zabi miji mu baza mu zaba miki wanda zai cucekiba . Hanna babu wanda ya fadomata a rai sai Haisam, soyayyar da take yiwa Haisamsai kara yabanya take a cikin ranta, Hanna ta ciresha'awar auren wani a rayuwarta tunda ta rasaHaisam shine ma hawaye yake zuba dagaidanuwanta don tasan ta rasa wanda take so duk duniyar nan ta rasa farin cikin kuma. Wannanhawaye na hanna da yake zubowa dagaidanuwanta yasa jikinsu ahmed yayi sani kumamamaki ya rufe su yaya za'ayi hanna ta fara kukatun kafin taji waye aka zabar mata ta aura. Koakwai wanda ta kudira zata aura ne basu sani ba ? Inna rabi tace'' Hanna kukan me kike bafa cewamuka yi dole sai kin auri wannan da muka zabarmiki ba idan kina da wanda kike so fadi mu auramiki,daman ganin babu kowa ne shi yasa muketunanin hadaki da wani. Hanna ta share hawaye tagirgiza kai tace'' babu wanda nake so zan aura dukwanda kuka zabar min zanyi biyayya in aure shi kowaye kuma. Nasan baza ku zabar min wanda zaicutar dani ba'' gaba daya suka fara shiwa hanna albarka suna jinjina mata bisa tsananin biyayya datake yi musu allah yayi mata albarka. Kawu ahmadyayi gyaran murya ya gyara zama yace'' hanna tunfarkon zuwanki abokinna koma ince ya zama danuwana saboda tun muna yara muke tare nasanhalinsa ciki da bai fiye da uwar data haifeshi bata sanshi ba fiye da yadda nasan yadda yake yana damutunci da sanin ya kamata yace yana sonkitsakani da allah zai aureki wannan aboki nawashine bello madu abokina din nan da mukajenigeria garinku dashi muka daukoki . Yana dasana'arsa kuma yana da ilmi gaba daya boko da arabiya yanzu ma babba ne ba laifi a aikinsa aikincostom yake sune suke tsaye a bordar nigeriazuwa niger. Ni dai a ganina bello masu ne kawai yacancanci ya aure ki ko ya kika gani? Iya ma'idatace'' wanne irin

Table of Contents

Chapters

17 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});