Chapter 7
Chapter 7
dakatar da ita mahaifiyar ta tayi Tatashi ta nufi k'ofar dakin sa tanazuwa tayi Sallamah taji shiru Ta tura k'ofa tashiga tana shiga ta tarar dashi Kwance Yanata famar Kuka murmushi tayi tace Nikam Mezan gani dan uwana kadaina kwallafa ranka akan abu Ba lallai bane kasamu abunda Kake so A lokaci d'aya saikasha wahala wani lokacin ma allah saiya jarrabeka da son Abu yakuma hana ka gwada ka, Kazamo mai tawakkali dan allah dan uwana kayi hak'uri dan allah ta ke itama tafashe da kuka tace Idan ka nayawan saka damuwar yarinyar nam aranka zata iya haifar ma da matsaloli mukuma bazamu juri ganin ka cikin damuba yaya Kabiru bazan iya jurar Ganinka cikin wannam halin ba tasake fashewa da kuka tayi ficewar ta tafita waje taci kukan ta tasa hanu tashare hawayen ta koma wajen mahifiyar ta cikin Fara'a ta danne Abun Acikin zuciyar ta. Tana zuwa Tazauna gefen Mahaifiyar, *"KABIRU, kallon fuskar ta tayi tace Yasmeen yaya naga kamar idanun ki sunyi ja, Murmushi tayi tace Babata Wani k'earone ya shigamin idona Kabirune ma ya huremini Idona Murmushi tayi Ta kwalla kira *"KABIRU! KABIRU!! Har sau uku fitowa yayi yana sosa kai Ya durk'usa yace Anti Ina kwana ta amsa lafiya k'alau sannam ya sunkuyar da kan sa yace mama ina kwana Tace lafiya Wai dagaske Abune ya shiga idanun *"YASEEMIN, fadamin gaskiya kodai kaine ka mata laifi murmushi yayi ya girgiza kai ya ce A mama Na huremata Wannam kina kallonta sakalcinta yayi yawa Dajin Haka gabaki D'ayan su suka tintsire dadariya Suna cikin Dariyar Ne Saiga Alhaji Wata Dan uwan mahaifiyar kabiru Suka gaisa ya nemi gu yazauna kabiru na Durk'ushe a ka'asa yace Inason Wata magana Daku gabakidayan ku Duk Hukuncin da kuka yanke shikenam. Shiru Yayi nadan wasu mintoci, Ajiyar zuciya yayi yace Kabiru Yace Na'am Baba yace Wannam Mahaifin Wacce kake son Ya tazar tani Tozarcin da zaiyi wahala na iya mantawa da shi A rayuwata. Lokacin da muka sauk'a garin adamawa Mukakai Izuwa k'ofar gidan shi Saida nayi tinanin maganar da akafadamini Akan Bashida Kirki mutuminnam Yar sa kuma kowa na shedar ta 'yace Tagari tasamu tarbiyya sosai wajen mahaifiyar ta, alokacin dana shiga cikin gidan Ita d'iyar tashi ita ce tazo ta tareni ta durkusa har k'asa ta gaishe ni ko daga kanta batayiba da nufin ta kalli cikin k'wayar idona balle fuskata ba Awannam lokacin naji ta kwanta min Araina Naji Koda nawa ne zan kashe Dan Dana *"KABIRU, ya mallake ta a matsayin matar sa Bayan ta Kaini Wani masauk'i na musamman mahaifiyar ta tazo muka gaisa Ta kawomini ruwa nasha sun tarfeni Hanu bibbiyo Daga bisani Tadawo ta d'urkusa ta bani hak'uri tace Baba kayi hak'uri Abba na yana fitowa yanzu Kayi hak'uri bisaga jinkirin daya maka. Nayi murmushi, na ce Ba komai tayi tafiyar ta jim kadam!, yafito saida ya k'are min kallo nina daga masa gaisuwa Cikin izzada gadara yace Kaine Mahaifin Wannam Yaron dayake zuwa wajen 'yata nace masa A tabbas nine Yanzuma nazo tambaya mar izini ne wajen ka Amatsayin ka na mahaifin i ta wacce ya ke so. Wani kallo yamini, yace Befada maka Abunda nafada masa bane Bazan tab'a bawa matsiya ci 'yata ba Kaci sa'a kamin zuwa bazata ne bansan dazuwan ka ba da ko bata lokacina bazan yiba wajen sauraran sha_sha shu irin ku ba, Nayi murmushi dukda abun ya batamin rai sosai, Nace masa bekamata kayi Haka ba yarannam suna son junan su Banga wani Abun aibubu Dan d'an talaka yaga yar masu hali yace yana so. Charaf yayi yace Lallai talaka idan har yazo gidana abu biyu be yakawoshi koyamin bauta na biyashi kokuma yazo neman na masara, Dan haka kadaina tsam_manin wannam had'in zai yuwu Natsani talaka. Ta shi nayi A fusace jikina na bari nace To ai Shi Arziki nufin Abungiji ni Dan yabaka bawai muma Ya mata damu bane inamai bakashawara Kokuma ince Duk masu dukiya irin ka dasuke Cewa su bazasu bawa 'ya 'yan su talakawa, suna ruwa Karkamanta Idan Allah yagadama sai kabawa mai tarin dukiya Allah ya jarrabishi Gabaki d'aya dukiyar ta k'are Kenam zakaje kace Lallai saiya saki maka 'yar ka dan allah ka gyara halinka. Bangama rufe bakinaba yasa hanu yamare ni tasss! Lakaci d'aya iyalin sa ta taho sukatar na rik'e kunci na na dama nayi shiru, Gabakid'ayan su kowanne jikinta yayi sanyi! Najuya zantafi yar tasa ta taho ta dur k'usa A gabana ta ce Dan Allah Baba kayi Hak'uri tsayawa nayi na kalleta ta fashe dakuka ta ce ni *"KABIRU, Nake so murmushi nayi na kalli mahaifin ta na girgiza kai nace mata Bakomai Tatashi tatashi Najuya zan tafi Ta sake bina tana kuka tace Karka Hana kabiru Shima yana sona Munason junammu. Ya ga ma basu labarin kenam kowa jikin sa yayi sanyi yace ina mai neman shawari ne A wajenku wana hukunci kuka yadace Muzartar kowa yayi shiru baice komai ba. Yayi magana har sau uku bawanda yace mai komai, Ya ambaci sunayen su d'aya bayan daya kowanen su yace duk hukuncin dayaga yadace shikenam, *"YASEEMIN, Ne tayi magana ta ce Abba Nibana goyon bayan Ace Yaya k'abir ya bar *"ZAINABA*, Cikin wannam hali Aganina Baikamata A biyewa mahaifin ta ba Tinda mahaifiyar ta da ita kanta suna son shi, Amma kuma Abba kai yakamata ka yanke hukuncin dakaga ya dace Tashi tayi Tana murmushi tace Zandan kwanta kaina ciwo yakemini Wucewa d'akin tatayi ta dura k'ufa ta sa kanta na kallon k'asa akan wani k'asaitaccen gado mai laushin gaske Hawaye ne kawai suke zubuwa daga idanun ta. Ta ke mahaifin Nata ya umurci kabiru daya bi bayan yaseemin Sutaho tare Kwan_kwasa mata k'ofa yayi tayi maza_maza ta share hawayen ta ta bude k'ofar yace Abba na k'iranki Tahowa sukayi tare tanazuwa ya mik'owa kabiru key d'in motar sa yace Kakaita Babban Asibiti Abata magani Amma kabi Ahankali kaga hanun ka bai fada ba ka kiyaye yace to Abba yaciro kudi 10k yabashi yace kasha mai na 5k sauran 5k din kuma zai isheku zuwa asibiti Kama hanya sukayi Yashiga mota yabude mata k'ofa tashigo Tafiya suke Ya kalleta yace nikam yaseemin maiyake damun kine kam Kifadamin dan Allah murmushi tayi ta harareshi Tace Bakomai Kawai dai nima bansam takamai_mai abunda yake Damuna ba Tafiya suke har sukazo mashigar Asibitin Yanemi gurin Ajiyar mota ya Ajeta Tafito Daga mota kenam Taga K'afafunta Na hahhardewa Jiri ya d'ebeta ta taho zata fadi yatare ta rike hanunta yayi Ta kwanto jikin sa Sunatafiya Har sukazo wajen Ganin likita Sannam Ya zaunar da ita Ta kalleshi tace yunwa nake ji yaya kabiru take yafita akahado mata shayi mai kauri, Yazo yabata tasha bayan wasu 'yan mintoci gumi yayanko mata, Ta kishin gide Bacci yadauketa Tasamu awa d'aya Tana bacci *"KABIRU, yana gefe Yana kallon ta har layinsu yazo Aka k'irawo su yace A'a nabayan sa suje Ya yiwa likitan bayani tana baccine Likitan yace Shikenam Dazarar ta tashi Sai su K'ariso Adubata Awa biyu Tayi masu kayu sannam ta farka daga bacci tayi Hamma Kabiru ta gani a gefen ta yana gyan_gyadi ta yi murmushi. Farkawar dazaiyi yace Kintashi kenam tace A yace to Mu isa Kije kiga likita Tana tashi taji Gabakidaya Jikinta da k'arfi sosai
Table of Contents