Chapter 5
Chapter 5
Tahaye Gado ta kama Kuka, Tashi Kabiru yayi yabita Abaya yanazuwa tace fucemin Daga Dakina Banason ganinka Murmushi Yayi Ya zauna nesa Da ita, Yace Yi hak'uri k'anwata Tsokanar ki muke Dajin Ankirata da k'anwata saita Share Hawayen ta tazauna Tace Shikenam. Yawuce, Kayi hak'uri Besa ga laifin danamaka Kallon ta yayi yace Tab..! Ai saina rama zaro ido Tayi tace Ramawa kuma yayi dariya yace A'a "ta durk'usa hark'asa tace Natuba Kayi hak'uri Naga kai dan uwanane Idan kuma kanaga bazaka hak'uraba to kaje kayi Duk Abunda zakayi, Wani kalla ta masa ta harare shi Shikuma yayi murmushi yace, kinga ni bak'one Agarin *KEBBE*, ko zaki rakani In Allah ya kaimu gobe mudan zagaya gari. Tntsirewa tayi Dadariya tace Tab..! Ina Ni Inada wajen zuwa gobe da yamma Amma shikenam Zamufita amma dasharadi Dole zakayi wanka na kece raini Haka kuwa akayi washe gari, *KABIRU*, Ya fito yafesa wani tirare mai bala'in kamshi..! Yafito kenam Yaji an kama k'afar sa yanajuyawa yayi murmushi budan bakinta tace Yaya Nima Zanbika wajen da zakaje, Fitowar *"YASEEMIN*, kenam ta hantare ta tace to Sarkin iyayi babu indazaki je Tafara marza idonta *KABIRU*, yararrashe ta da kyar sannam ta hak'ura Fitowa sukayi Ta dauko motar ta suka shiga gari daf da magariba Sukadawo gabakid'ayan su A gajiye bayan*KABIRU*, Ya idar da sallar magariba k'arar shigowar Tex yaji ya ciro wayar sa yana dubawa yaga *zainaba*, Ta rubuta sak'ako Kamar haka, Inaso kad'aga wayata inason zamuyi maganane da kai mai mahimmanci kaji?. Tsaki yayi yadanna number ta yanashiga sukagaisa, Tace Banzaci zakamin hak'aba ji nake Koda nabaka dama zakabani kunya Amma shikenam Yanzu kana ina ne, Nasamu labarin baka garin Adamawa, ka koma kebbe dazama, Idan zuciyata ta buga Kaine Sila, Kawai takashewar ta. Kabiru yayi murmushi, yanazaune Saiga *YASEEMIN*, tafado dakin sa ko sallamah babu, Hankalinta A kwance Ta kwanta kan katafar sa, Budan bakin sa yace Ke ina wasa dake kitashi ki Fita kibani Waje Murmushi, tayi Tace Dawa kake waya Tayi wuf ta Dauki wayar sa tadanna call yanashiga *ZAINABA*,Tadaga tace Wacece ke, Murmushi ita kuma tayi tace be fada miki bane Ai yajima da Yin Aure yanzuma haka da matar sa, Kike magana. Wuf yayi ya karbe wayar sa, yace zamuyi magana anjima bagaskiya tafada mikiba, yanakashe wayar sa yace kekuma yaya zakimin haka Kinsam wahalar danasha kafin na zamu soyyyar zainaba kuwa, *YASMEEN*, bakisam Darajar so ba Shiyasa zakimin haka amma nima zan rama. Bayan sallar Isha'i *kabiru*, yak'ira number zainaba tana d'agawa tace Dama kanada Mata Shine ka boye mini?. Dogon numfashi, yaja tare da aji ye numfashin, "Yace haba *zainaba*, yanzu kin yadda da zancen Da *YASMEEN*, Tafada miki kenam, Hmm tayi tace wacece Kuma yasmeen?, murmushi yayi yace K'anwata ce Yar baffa nace, Yanagama furta wannam maganar,*Zainaba*, tace (WHAT)? Tace to ai akwai aure tsakanin ku Dan Haka Ka kula da kanka Jinake Kamar Zata mini k'wace walla *yaya na*, Murmushi yayi ya ce, haba ma Ai ai Kekadai ce Zainaba babu wata, Kafin yarufe bak'i *"Yaseemin*, yazo wajen kunnen sa taje Malama kiyi hak'uri wata tariga tashagaban ki, Tafita da gudu tanata famar Dariya. Dak'yar yasamu ya rarrashi,*"zainaba* sannam ta yadda Amma bayan ta yadda tace Yaya ina son ganin ka Nam da sati d'aya akwai wata magana mai mahimmanci dazamuyi kaji Yayi shiru yace Satina uku kenam dazuwa garin kebbe amma insha allah Ranar Asabar Zan Yi iya duk wasu K'arerayina baffa yabar ni nazo ko kwanad'aya ma nayi Haka kuwa Akayi Ranar Jumma'a da safe Yafito Ya sanar Da baffan sa gashi gashi Zaije dauk'o wani Abunsa ne amma kwana d'aya zaiyi Ya dawo *ANTI LABARA* Mahaifiyar yasmin tana gefe tace kabiru dan Allah kasan yadda zakayi ka lallabo Adda kutaho tare Baffan ka zaiji dadi idan tana tare dashi murmushi yayi yace Shikenam Zanjarraba Sukayi bankwana Yafito Kenam ya tarar da yasmeen awaje tare da 'yar karamar kwanwar ta Zuwa yayi ya zauna yace kukuma mai yake damun ku, Harar sa yasmeen tayi Tace Oho Yanzu Akan wannam Yarinyar Zaka Kama hanya Kaje wajen ta?. Murmushi yayi Yace Yasmeen kenam ke yarinyace bakisam girman so ba Ina matuk'ar sonta sosai Bazakigane ba Tsaki tayi taja k'anwar ta suka wuce Cikin Gida Yajuya yayi tafiyar sa yaje yahau mota, Misalin K'arfe 11:17am ya sauk'a garin Adamawa ko gida bai isaba ya k'ira *zainaba* Awaya yace kifito waje Kinyi bak'o cikin Gaggawa Ta saka hijabin ta tafito Tana kallon kabiru Tafara famar rufe idanun Ta Alamar Tanajin kunyar sa, Kallon ta yayi Yai murmushi Suka gaisa Ya nemi guyazauna Itama ta zauna Yace *"Zainaba* ganinam Yanzukam magana ta k'are ai ko?. Tsayawa tayi tana kallon cikin kwayar idanun sa harna tsahon minti biyu batace komai Ba, Can ya ce Tinanin me kike haka Zainaba Tace bakomai Yace A'a tace Tinani nake Inajin Kamar Bazan zama matar Kaba, Ta ke Hawaye ya fara zubuwa daga Idanunta. Jikinsa yayi sanyi yace A'a kidaina fadin haka Kishare hawayen ki Tashare hawayen ta Tace daman Kawai nak'ira kane Dan na jarrabaka naga irin son dakake mini Nagode Insaha allah bazan ci Amanar kaba Namaka Alk'awari Amma ina so ka dad'a dagiya akan tada Yanzu Haka maganar Da ake mahaifina nason Had'ani Da wani ummana nace take fadamin Sonake Kagwada Sa'ar ka Ka tinkari Mahaifina Ko zai Amin ce Ya baka ni Ta ke zuciyar Sa ta k'ada Ta ce Yana cikin Gida Kazo zan maka rak'iya Shiru *kabiru* yayi yace A'a zan dai tsaya daga waje ki ce Ana sallamah dashi tayi murmushi Tace to shikenam Ta shiga batafi minti d'aya ba ta k'irashi Awaya Tace Yana zuwa inaso Ka kirani Karyasan kak'irani inaso naji tattaunawar Dazaku yi kaji yaya na?. Ya na tsaye Harkusan minti shabiyar, harya juya zaitafi Yaji ta bayan sa ance kai Yaro dakata, Juyowa yayi Ya danna k'ira *zainaba* ta daga tayi shiru yasaka wayar A'aljuhun sa ya sama, Yana zuwa ya d'urkusa yace Ina wuni Baba, Yace Lafiya k'alau Shiru yayi baik'ara cewa komai ba, Mahaifin *Zainaba* yace Ganinam maike tafe dakai shiru yayi Yagaga d'aga kansa ya kalleshi saboda tsabar tsoro. Budan bakin *KABIRU*, ya ce Baba daman maganar Zainaba ce kyal_kyala dariya yayi yace Daga gani Ai dama buri yayi kama da mutum, Bakasan halina ba ko To idan ma Sonta Kake Ina mai baka shawarar maza_maza ka kashe son ta daya ke cikin zuciyar ka Bazan bawa talaka 'yata ba Ninadauka ma kazo neman Na masarane!, Kabiru kansa na k'asa yace A'a baba kayi hakuri idan na maka laifine Amma Munason juna nida zainaba, K'afar sa yasa ya tankade shi Yace maganar Banza maganar Wofi. Ina nine mahaifin ta to na Ce bazan baka 'yata ba Saboda bazaka iya rik'emin ita ba kabar wanna maganar karnasa ke jin sunam ta Abakinka Bakasan koni waye bane shiyasa Amma kaje Banason sake ganin ka a k'ofar gida na. Daga wayar sa yayi ya k'irawo zainaba yaji tana waya yasake kira kwalla k'ira yayi tataho da gudu Idanun ta gaba k'idaya sunyi ja Tana zuwa ta durk'usa Yace daga yau banason Ganin ki tare Da wannam matsiyacin Ina fatan kingane Dago kai *Kabiru* yayi ya kalli zainaba yayi murmushi Yajuya yayi tafiyar sa Yana isa gida mahaifiyar sa tace Mezan gani Haka
Table of Contents