Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

Zainaba Yar Gata Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

: WRITERS ASSOCIATION_ _________________________________ ~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~ https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/ BY *KAMAL NO LOVE (DAN GOMBAWA)* *BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM* *26=30* *Wannam Fejin nakune, Manyan yayu.* *Bros Usman Ango* *Husain 80tk* *Hassan tanko* Da gudu_Gudu ta sake tare shi, ta ce Kabani Amsar tambaya ta shiru yayi yai murmushi chakwamar kwalar rigar sa tayi ta fashe DA kuka ta ce idan har na mutu Kaine sanadi katafi kabini waje banason sake ganin fuskar ka ta fa she dakuka. Ta wuce Dakinta ta zauna tayi shiru,kwanaki biyar suka shafe “Kabiru, Yana mata magana Amma ko daga kanta batayi Balle tasan Ma yanayi. suna zaune yace Yasmin Ki saurare ni Mana juyawa tayi tana hawaye ta ce Me kuma zaka fadamini Ka fifita ta Akaina Duk irin son da nake maka Amma ka gaza fahimta ta, Murmushi yayi Yace to zan k'i k'anwata ne. Hararar Sa tayi ta tashi Tai Tafiyar Ta, Ta barshi zaune yanata tinani yace Shin wazan Bari Zainaba dai Ina matuk'ar son ta Amma kuma itama yasmin, 'yar uwata ce Tanunamin so Da k'auna Bazan ki ta ba Rik'e kai Kabiru Yayi Yai shiru kansa na k'asa. Tagumi yayi yai shiru! Na d'an wani lokaci yaja dogon numfashi, jiyayi An dafa k'afadar sa juyowa yayi cikin sauri Suha hada Ido yace A mama lafiya Kam ko?, murmushi Tayi Tace “Kabiru Kenam Wai Nikam Mai ya ke damun ka ne kam?, murmushi yayi Ya dafa k'afadar ta ya ce Mama na kenam Babu Komai Kallon shi ta yi tace Na fahimci komai Dana kafada min Nifa mahaifiyar Ka ce, Murmushi yayi yace To mama, Ya kwashe Labarin Abunda Ya ke faruwa ya fada mata. “Shiru tayi nadan wani lokaci bata furta komai ba, Sannam tayi murmushi, Ta ce kabiru Kenam “Yasmin, 'yar uwar ka ce ta jini Sannam kuma zainaba na yaba da halayin ta sosai Ka nitsu da kyau Zaka samu mafita Kaji k'abiru dukanin su kowacce kowacce sonka ta ke bana wasa ba, Yanzu dai duk yanda za'ayi kafara shawo kan 'yar uwar ka koda zainaba kafiso kaji?. Ta tashi tayi tafiyar ta. Washe Gari d'asafe Kowa ya fito Ana karya kumallo, (Breakfast) kabiru yana dakin sa bai zoba *Antin sa* mahaifiyar *Yasmin* tace Yar autar mama jekiki Dau Abincin nam ki kaiwa yayan ki, Ranta bai soba Ta dauki (Tea da k'atoton Bread da sauran kayan hadi), Tana zuwa tayi Sallamah ya amsa yace Shigo tana shigowa ta Ajiye ta fasa madara ta masa duk abunda yadace tsayawa yayi yana kallon ta, yai murmushi Ta harare shi ta ce murmushin me kake?. Budar bakin kabiru yace Naga 'yar uwa tace murmishi tayi ta ciza baki Ta ce A'a niba jinin ka bace *Zainaba* ce Jinin ka ta juya zata tafi ya ce Yasmin Ki tsaya ki saurare ni Tsaya tayi Ta na kallon sama Tace ina sauraron ka, Tashi yayi ya zauna yace Badan halinaba A matsayina na mai laifi ki taimaka ki zauna kinji. Zama tayi nesa dashi, ta ce to na zauna yaukuma wace k'arya za'a fadamin kuma idai kasan harzaka ambaci wannam yarinyar ko kuma akanta ne to karma kafara dan kuwa Natsani jin koda sunam ta, Murmushi yayi yace A'a Akan kine K'ara gyara zama tayi yace yasmin, Bawai na k'iki bane Ki fahim ce ni wani irin kallo tamasa tace dama kumaza haka kuke Dazarar mace ta bayyana muku Abunda ke cikin zuciyar ta cewa I tafa takamu da son ku dagawannam lokacin zaku tozar tata na gwammace da barin sonka nayi acikin ziciyata koda zaizoma ajalina da fada fada maka buk'ata ta Amma haka k'a k'ini Haba maza kidinga yimana adalci mana Gudun haka yakesawa yawancin 'yammata ke buyo damuwar su su barta cikin zuciyar su Amma kasani Hargobe Nidai ina sonka yaya Kabiru Amma nasam Kafison Zainaba fiye dani Komai ya wuce Ni zan hak'ura amma kasani kana cikin zuciyata Har abada mantawa dakai Abune mai matuk'ar Wahala Ba komai murmushi tayi ta share hawa yen da suke gangarowa daga kuma tunta. Tatashi hartaje Bakin k'ofa Ta juyo tayi murmishi, Ta ce dan uwana Komai ya wuce Da dinnma bawai fushi nake da kaiba Kishi ne kawai irin namu na mata Na barka lafiya. Kallonta kabiru yakama yi ya gagara cewa komai Ta fita kenam, Batawuce taku uku zuwa hud'u ba Ta ji Kabiru Yayi k'ara juyowa tayi A figice Ta taho yayi shiru taga kofin shayin a gefe A fashe Yace Haba kekuwa Baki fadamini ruwan shayin da zafi sosai ba ne, Murmishi tayi Tace Kaji wannam fa kodai tinanin ta kake Har kamanta ka d'id'ara shi Abakin ka kodai kana tinanin unty *Zainaba* ne kam?. Tajuya tayi tafiyar ta, Kabiru yayi mamaki sosai Ganin yanda suke mu'a mala kamar da wasa dadariya Watarana suna zaune su biyu kabiru Yace wai nikam Natambaye ki mana dariya tayi ta ce ina sauraron ka a matsayin me nake Awajen ki, murmushi tayi tace d'an uwa mana kasan dai ni ba sa'ar ka bace nawuce Ajin soyayyah da kai. Tintsirewa yayi da dariya yace, A haka kuma naga wata harda kuka, Ta ke tace banaso kadaina tinamin Abunda ya faru Baya dan allah ko so kake mu kuma Abunda ya faru da kenam ko?. Lallab'ata yayi haka sukacigaba da mu'a malar su kamar da, Abun burgewa. Yasmin, Ta dauki Kabiru A matsayin Dan u wanta, haka Tanaji Tanagani Ta Hak'ura DA muradin ta Danganin Ta farantawa Mishi Rai. Zainaba Tashiga Damuwa Sosai bisa ga Abunda ta Aikatawa Kabiru, Zaune ta ke Tayi ta gumi..! A bun tausayi, K'yalla Ido tayi Ta hango Wayar ta, Ahankali cikin tsaro DA fargaba ta latsa lambar Kabiru, Tayi sa'a Alokacin DA wayar tashiga Tana hanun sa Dauka yayi yaji muryar mace, suka gaisata Ta ce Yaya kabiru Kayi hak'uri bisa Abun da ya faru ina mai Baka hak'uri. Wani murmushi na musamman yayi, Ya ce Haba zainaba ni fahimci komai DA Komai, Karki damu Kinanam Acikin zuciyata juyawar dazaiyi kenam. Yasmeen, ya hango A gefen sa tana murmushi, ta ce bazaka bani ita mugaisa bane?. Mik'amata wayar yayi Amma zuciyar shi na k'adawa tana k'arba tace Unty zainaba ya ya like?. Amsawa tayi DA lafiya k'alau, Ta ce Yayana yana sonki Sosai Kirike mini shi Amana, inada tabbacin bazaki nuna gazawa wajen bashi kulawa sosai Unty zainaba. Murmushi zainaba tayi tace Insha Allah zanyi iya ka k'okarina karkiji komai, Kidai kitaya mu da Adu'a mahaifinane Bashida Dad'i bankwana sukayi, tana gama wayar ta ganshi Akan ta. K'are mata Kallo yayi, Yace kinbani Mamaki bazaki Tab'a fahimtar Mahaifin ki ba, Narabaki DA wannam yaron Amma Kink'i fahimtata. Daka mata tsawa yayi, Yace To kisani nikuma Bazan tab'a Amincewa dashiba bazan had'a zuri'a DA matsiyata ba. Juyawa yayi yai tafiyar sa. Binsa tayi DA Kallo, yaje dai_dai Bakin k'ofa Kenam tace Baba kana son farincikin 'Yar ka Kuwait?, dakatawa yayi yai shiru Ta ce Baba kabarta Da auri Wanda take so, Amma duk Hukuncin daka yanke shikenam. Tsayawa, yayi yace To ina so ki manta da wannam yaron, shiru tayi ta ce shikenam Baba, fashewa tayi DA matsanan cin kula!. Ya koma d'aki yai zamanshi, washe Gari DA sassafe Yafito sukayi ban kwana, Yajuya zai tafi yace ina Yar gatan baba

Table of Contents

Chapters

16 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});